← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 90

Sashe 61

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ba suce komae ba suka fice kowanne jikin sa a matuk'ar sanyaye, se da suka fita sannan Ummee ta maeda duban ta kan Abbu da har lokacin gumi be dena tsatsafowa daga jikin sa ba... Kuyi Manage da wannan pls. Alhamdulillah mun yi biki lpia, mun gama lpia, se dae fatan Allah y basu zaman lpia me d'orewa, masu min fatan alkhaeri da addu'o'i ina godia irin sosae d'in nan, Allah y bar zumunci Mhiz Innocent.... https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* Page 047 ___"Bangane manufar ka na cewa su fita ba? Kana nufin ka amince da abinda yaje ya aekata, bayan ka san wacece Ayrah, wanene mahaefin ta?" Ummee ta fad'a tana kallan Abbu sosae cike da son jin abinda ze fito daga bakin sa, zazzafar iska Abbu ya fesar daga bakin sa sannan ya d'aga kae ya kalli Ummee kana ya girgiza kae lokaci d'aya yana sauke numfashi "Fatima! Shin ko dae baki ji abinda yaron nan yace ba? Ko kuma kece kika manta wacece Ayrah? Kina tunanin duk tsawon lokacin nan da aka d'auka ita da kan ta Ayrahn ba zata iya fad'a masa abinda ya raba mu da iyayen ta ba? Ko kuma su kan su iyayen? Kenan da wane ido zamu kalli yaron nan muce ya sake ta? Kenan akan wane dalili? Se dae idan kuma so kike yi ragowar mutuncin mu ya k'arasa zubewa" Abbu ya fad'a yana runtse idanun sa saboda har lokacin bugun zuciyar sa be koma dae_dae ba, haka kawae kuma yake jin wani nauyi cikin k'irjin sa, ga kuma zafin da har yanzun be dena ji ba se ma k'aruwa da yake yi, sosae Ummee ta cigaba da kallan sa har na tsawon wasu sakanni masu yawa kafin tace "Yanzu kenan me kake nufi? Tun yanzu har ka sare? Meze faru idan muka bari ya gane da gasken mune muka yaudari mahaefin Ayrah? Ni ina ganin abinda ya dace kawae kada mu nuna gaskiya ne ko da ya san maganar tunda ae kowa ma zargi yake yi har shi kan sa Abban Sadeeq d'in" d'aga kae Abbu yayi ya kalli Ummee dake ta zubo wannan bayanin, shi kam gaba d'aya yau d'in maganar ta ta sam bata samu wajen zama ba, sam bata kar6u ba, haka kawae yake jin wani irin sanyi, duk jikin sa ya mutu dan haka yace bayan ya girgiza kae "Fatima kenan, baki yadda da abinda na fad'a miki ba kenan, yanzu maganar da nake miki ma takaddun Abban Sadeeq d'in dake ajje cikin d'aki na su nake nema tun d'azun ban gan su ba, ba kya tunanin yaron nan ne ya d'auka bayan ya san gaskiyar abinda ya faru?" Abbu ya fad'a kamar a d'an sanyaye, cike da son tunzura Abbu Ummee tace "Bashi bane, ko da ya san maganar bana tunanin ze aekata hakan ko dan kare mutuncin ka, ballantana ma na san baze ta6a yadda da maganar wani akan ka ba a matsayin ka na mahaefin sa, dan haka ina ganin ka kwantar da hankalin ka dukiya ce dae taka ce kawae dae ka same ta ne ta sanadin kud'in Abban Sadeeq" ba dan maganar Ummeen ta samu gurbi a wajen Abbu ba ya girgiza kae yana murmurshin da yafi kama da na yak'e, kamar ba zece komae ba se kuma can yace "Ki sanar da shi ya d'auke su su je zuwa gobe zan tuntu6e shi" da sauri Ummee ta kalli Abbun cike da mamakin jin furucin sa tace "Bangane ba Kabeer!" ta fad'i sunan sa kae tsaye abinda ze iya cewa tunda suka yi aure da wuya idan ta ta6a kiran sa haka gatsal, hakan da ta fad'a ne ya sanya shi d'aga kae ya kalle ta kana yace har lokacin be d'auke kan sa ba "Zan yi bincike ne" ya fad'a har lokacin jikin sa a mugun sanyaye, shiru Ummee tayi ta kasa cewa komae kawae seta gyara zama ta d'auke kan ta daga inda Abbun yake tama rasa tunanin abinda ya kamata ta yi, ganin haka ne ya sanya Abbu janyo wayar sa ya danna kiran Rk. Yana tsaye a jikin motar sa hannun sa gaba d'aya sak'ale a k'irjin sa, yayin da Ayrah ke zaune gefen sa kan ta d'ore akan cinyar ta tayi shiru kamar me bacci, gaba d'aya hankalin sa yana akan Ummee da Abbu ne yana tunanin matakin da zasu d'auka hakan ne yasa hankalin na sa yak'i kwanciya, kamar daga sama yaji ringing d'in wayar sa, ya janyo ta daga cikin aljihun sa dan kashe ta saboda yadda yake ji a yanzu baze iya d'aga waya ba, se dae me? Se yaga sunan Abbu na yawo a saman wayar, hakan ne ya sanya shi saurin d'agawa yana karawa a kunnen sa, tun kafin yace komae Abbun yace da muryar sa da ta d'an chanja saboda damuwa "Ka d'auke su ku je gida, zan neme ka zuwa gobe, ka tura min address na k'auyen.." shine kawae abinda Abbun ya fad'a ya katse wayar sa, wata sassanyar ajiyar zuciya ya sauke yana lumshe idanun sa akan la66an sa ya furta "Alhamdulillah.." yana murmurshi, ya kae wajen minti 1 idanun sa a kulle sannan ya bud'e su, a hankali ya soma takawa zuwa inda Ayrah ke tsugune, bece komae ba kawae shima ya tsuguna ya k'are mata kallo a hakan kana ya sanya duka hannun sa ya d'ago kafad'ar ta se kuwa ta d'ago da sauri tana kallan sa, k'awataccen murmushi ya sakar mata wanda ya k'arawa fuskar sa kyau, se kawae ta zuba masa nata narkakkun idanun dan ita sam ba taga amfanin wannan murmushin ba idan tayi duba da halin da suke ciki, hakan da tayi ba k'aramin sake narkar da shi tayi ba wanda ya tilasta masa lumshe idanun sa yana sake sakar mata murmushin, ganin dae har lokacin babu wani reaction daga 6angaren ta ya sanya shi jan ta jikin sa ya rungume ta sosae yana lumshe idanun sa "Kada ki damu babu wata matsala In Sha Allah, Abbu da kan sa yaje muje gida.." ya fad'a a dae_dae saetin kunnen ta, ita dae ba tace komae ba saboda yadda jikin ta ke a sanyaye har a lokacin kawae tayi shiru tana saurarar bugun zuciyar su daya had'u waje d'aya, sakin ta yayi bayan wajen second 40 sannan ya saka hannu ya mik'ar da ita ya ja ta har wajen motar sa ya bud'e mata gidan baya, kana ya sake kafe ta da idanun sa yace a nutse "Ki shiga kin ji? Na san wacece ke shiyasa na za6a miki nan d'in" ya fad'a dan ya san idan yace ta zauna a gaba za'a samu tashin hankali ne da Muneerah, ita kuwa ya san idan tana bayan ba zata biyewa Muneerah ba dan ta zauna a gaba, babu musu ta shiga bayan ta zauna sannan ta jingina kan ta a jikin window d'in motar ta lumshe idanun ta, kulle k'ofar yayi kana ya soma takawa zuwa cikin parlourn Ummee inda yake da tabbacin ze samu Muneerah a ciki, a parlour ya samu Bahijja na zaune kamar munafuka, be ko kalli inda take ba be kuma tambaye ta inda Muneerahn take ba ya k'arasa d'akin da k'ofar sa ke a bud'e, a nutse ya saka hannu ya sake matsar da labulen daya rufe wani 6angare na d'akin kana ya aza idanun sa cikin d'akin, tana zaune kan gado ta d'ora kan ta akan cinyar Aunty Zeenah, da alama magana suke yi ta sirri saboda yadda suke maganar a hankali cike da takatsantsan "Ki fito zamu wuce, ina parking space, ki same ni acan.." shine abinda ya fad'a, wanda yake da tabbacin ta ji shi, hakan ne ya sanya yana gama fad'in hakan ya juya a nutse ya bar parlourn, Bahijja ta bi shi da kallo har ya fice daga parlourn sannan ta dawo da duban ta cikin d'akin tana share k'wallar da ta taho mata. Kallan Muneerah Aunty Zeenah tayi tace "Maza tashi ki wuce ki bi mijin ki" mik'ewa zaune Muneerah tayi tana kallan Aunty Zeenah kana tace "Babu inda zan je matuk'ar be saki wannan shegiyar ba" ta fad'a a zafafe, murmushi Aunty Zeenah tayi tana girgiza kae "Lallae Muneerah baki da hankali, yanzu ke se wani ya zauna ya fad'a miki waye mijin ki? Halin sa ne baki sani ba ko mene? Kina tunanin wannan hargagin naki ze sa ya sake tane? Ko kin manta yadda akayi auren naku ne na tuna miki?" ta d'an numfasa sannan ta d'ora da "Toh bari ki ji na fad'a miki idan zaki tashi ki tashi ki bi shi kada ya gaji ya tafi ya barki anan yayi tafiyar sa da matar sa, ki tashi yanzu na baki turaren nan yau ba se gobe ba kiyi amfani da shi ki gani idan komae be chanja ba zuwa gobe" Aunty Zeenah ta k'arasa tana sakin wani shu'umin murmushi, kallan ta Muneerah take yi kamin can tace "Allah koh Aunty na?" ta6e baki Aunty Zeenah tayi kana tace "A'ah ki zauna yarinya ki ga zama wallahi, idan kuma zaki yi abinda nace miki toh yanzu ki tashi ki bi shi ga shi nan" Aunty Zeenah ta fad'a tana saka hannu cikin jakar ta ta fito da wata k'aramar kwalba ta mik'awa Muneerah "Ga ta nan, kamar yadda na fad'a miki haka zaki yi, kada ki 6ata komae.." daga nan Aunty Zeenahn ta cigaba da fad'a mata yadda za ta yi har seda ta tabbatar ta fahimta sannan ta k'yale ta da niyyar za su yi waya zuwa gobe ta ji abinda ke faruwa, se a lokacin Muneerahn ta mik'e ta fice daga d'akin zuwa parking lot, kallan agogon hannun sa yayi sanda ta fito d'in, ran sa a matuk'ar 6ace, tayi matuk'ar sa'a saura minti 1 mintunan da ya d'ibar mata su cika da se dae ta fito taga baya nan, ta k'araso ta bud'e gidan gaba ta shiga ta zauna ta ja k'ofar ta rufe ba tare da tace komae ba, shima ko kallan ta beyi ba ya ja motar suka bar cikin gidan. Se da ya tsaya a wani waje ya siyawa Ayrah kayan da ya san zata buk'ata sannan ya wuce gidan sa wanda Muneerah ke ciki. Yana gama parking Muneerah ta fita
Chapter 61 · 0% Book details