Sashe 36
Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta ya wani saki, wata k'atuwar ajiyar zuciya ya saki sanda ta ruk'unk'ume shin, idanun sa a lumshe ya sake rik'e ta gam yana sauke taggwan ajiyar zuciya, sun kae wajen minti 1 a hakan har lokacin tana kuka a hankali, se a lokacin ta fara tuna a'ina take kuma a jikin wa take, da sauri ta saka hannun ta ta ture shi sannan ta tashi da sauri k'irjin ta na bugawa, se a lokacin ya bud'e idanun sa da suka sake lumshewa ba tare daya kalle ta ba ya mik'e ya k'arasa ya jefar da allurar cikin dustbin sannan ya juyo ya d'an kalle ta k'asa k'asa "Tashi mu tafi" tun d'azun bata kalle shi ba se yanzu da taji yayi maganar nan da saurin da bata san tana dashi ba ta diro daga kan gadon duk da har yanzun tana d'an jin jiri amma tama manta da hakan, murmushin da tun kafin tasan wanene Abbun Raj rabon ta dayi ya su6uce akan fuskar ta lokaci d'aya kuma tana sake goge fuskar ta, wannan d'an murmushin da tayi seda yasa ya d'an ji sanyi har cikin ran sa, ganin tana k'ok'arin riga shi fita ma ya sanya shi fad'in "Je ki wanke fuskar ki" yayi maganar yana tattara abinda ze fita dasu daga cikin asibitin dan so yake ya chanja mata asibiti idan bata samu sauk'i ba, kamar zata yi musu se kuma kawae ta juya ta fad'a inda taga yayi mata kama da toilet, babu jimawa ta fito tana sake sharce ruwan dake kan fuskar ta, ba tace komae ba haka zalika shima bece komae ba yayi gaba ita kuma tabi bayan sa, seda ya kulle Office d'in sannan ya cigaba da tafiya a nutse, ita kuma tana bin bayan sa, duk haka kurum take jin ta a wani irin takure, d'an jiri jirin da take ji ya sanya tafiyar ta ta ta sake zama very slow, se kuma idan taga ya mata nisa sannan ta saka iya k'arfin ta ta kusa cimmasa, yadda ake d'an satar kallan su ne ya sanya shi sake tattaro girar sama data k'asa ya had'e su waje d'aya, dan haka yawanci mutane se suka shiga hayyacin su, seda ya tsaya a pharmacy ya kar6ar mata magunguna har lokacin tana bayan sa kamar wata munafuka se bin wajen take yi da kallo har zuwa sanda suka fita harabar asibitin, yana shirin bud'e mata k'ofar wajen me zaman banza kamar wanda aka tsikara kuma seya fasa, ya sake kicin kicin da rae dan abinda yake k'ok'arin aekatawa yanzun yasan wata rigimar ce ze kuma 6allowa, seya zagaya ya shiga driver seat ya zauna, ganin da tayi bece da ita komae ba ya sanya itama ta sake had'e ta ta fuskar kana ta bud'e ta shiga, babu 6ata lokaci yaja motar ya fice daga asibitin, sanda suka hau titin seta samu kan ta da juyawa tana k'arewa titin kallo, in dae har ba tayi mistake ba nan titin Kano ne, bata san sanda ta saki wani murmushi me sauti ba tana ji kamar ta tashi ta taka rawa, duk da yadda yaji tayi murmushin hakan be sanya shi kallan ta ba sema sake tsuke face da yayi, haka ya cigaba da tafiya tana cigaba da bin titin da kallo, ita dae ba taga yayi hanyar unguwar su ba, tun tana k'ok'arin yin shiru taga iya gudun ruwan sa har taji zuciyar ta na son karaya ta kalle shi yadda yake driving a nutse sannan ta d'auke kae tana 6ata fuska itama "Bafa nan ne unguwar mu ba mu" tayi maganar murya a cunkushe, yadda tayi maganar ne ya sanya shi yin murmushin dabe shirya ba, gudun kada ta gan shi ya sanya shi saurin sake had'e fuska, kamar ba zece komae ba se kuma can bayan ya gama jan ajin sa yace "A haka zaki koma musu gidan kamar korarriya? So kike hankalin su ya sake tashi fiye da da? Zamu je kiyi wanka ne ki chanja kaya sannan na maeda ki gidan" yayi maganar cikin tsare gida shima tasa muryar a cunkushe "Toh ina ruwan ka?" ta fad'a bayan ta jefa masa harara, daga inda take tana ji kamar ta tashi ta rufe shi da duka, yace taemakon ta zeyi, ya taemake tan to kuma ina ruwan sa da yadda zata koma gida? Meye nasa a ciki? D'aga kafad'a yayi yana ta6e baki sannan yace "Babu ruwa na, amma ni dae bazan kae ki gida a haka ba" kallan jikin ta ta shiga yi, dan ita dae bata ga abinda tayi ba da yake nema ya fad'a mata magana ba dan haka ta sake kufula tace "Toh ka ajje ni in tafi da kae na mana, bana buk'atar taemakon ka a karo na biyu" ta fad'a tana jin yanda zuciyar ta ke mata zafi, be kula ta ba haka kuma be kalle ta ba hakan ya sake fusata ta, se kuma ta shiga sauke ajiyar zuciya tana runtse idanu, yasan yanzu zata soma kukan nan nata da bata gajiya dashi dan haka yana karya kwanar wani layi yace a nutse "Shikenan muje na rubuta takaddar ki tafi" jin abinda ya fad'a d'in ne ya sanya ta kalli inda suka shigo sannan taja doguwar ajiyar zuciya tana hana kukan daya taho mata fitowa, a k'ofar wani gida ya tsaya da motar tasa sannan ya dakata ya d'auki wayar sa ya danno number Yaseer ya kira, bata dad'e tana ringing ba Yaseer ya d'aga "Kana gida ne?" Rk ya fad'a "Ehh.. Na dawo" Yaseer ya fad'a daga inda yake zaune kusa da matar sa Hameeda "Toh gani k'ofar gidan ka" dariya Yaseer yayi gami da fad'in "Haba mana Mr man, ae ba seka zolaye ni ba, nasan ba ta6a zuwa zaka yi ba" d'an murmushi kad'an Rk yayi sannan yace "Toh ka fito ka tabbatar mana, hope dae Madam na nan?" da mamaki Yaseer ya kalli Hameeda sannan yace "Yeah, amma dae fari dae bari na fito dan tabbatarwa" ya fad'a yana mik'ewa sannan ya kalli Hameeda yace "Yanzu Rk ze shigo, yace min yana waje" "Ikon Allah! Amma kuma babu sanarwa irin wannan babban bak'o haka?" "Ke dae bari naje na fara tabbatar da zuwan nasa" Yaseer ya fad'a yana ficewa daga d'akin. Kallan sa ta cigaba dayi da manyan idanun ta da suka yi rau rau sanda yake wayar, har zuwa sanda taga yana shirin ajje wayar, yana sane da kallan da take masa dan haka ya sake rik'e wayar sannan yace "Ka taho min da takadda da biro" se a lokacin ta d'auke kan ta daga kallan sa tana sauke ajiyar zuciya, "gaba d'aya yau lokaci baya sauri" ta ayyana a ran ta. Suna nan zaune babu wanda ke cewa da d'an uwan sa uffan, se ga Yaseer ya bud'e gate d'in gidan ya fito, da murmushi ya k'araso bakin motar Rk d'in yana fad'in "Ohh Rk ashe da gaske kake? Ban ta6a tunani ba wallahi" ya fad'a dae_dae sanda idanun sa suka sauka akan Ayrah dake zaune tana jira a mik'o mata takaddar ta ta wuce gidan su (lol), murmushi Rk yayi kana ya bud'e murfin motar ya fita ya kama hannun Yaseer suka gaesa "Wacece wannan?" Yaseer ya fad'a yana kallan cikin motar sannan ya dawo da duban sa kan Rk, iska Rk ya fesar daga bakin sa sannan yace "Muje ciki zan maka bayani" sosae kan Yaseer ya kulle, shi dae yasan Rk d'in bashi da wata budurwa balle yace budurwar sa ce, kae abinda ma ya sani a yadda yasan Rk d'in baze ta6a d'aukar budurwar sa yaje da ita wani gidan ba, amma jin abinda ya fad'a ya sanya shi fad'in "Ohk, let's get in" Yaseer ya fad'a yana yin gaba, komawa Rk yayi ya lek'a ta window d'in side d'in sa sannan yace yana kallan ta yadda idanun ta suka sake cika taff da hawaye, baya so yayi wani abun da zesa ta sake yin kukan dan haka ya karyar da murya yace a tsanake "Kiyi hak'uri Madam, ya manta be fito da takaddar ba, kizo muje ciki in rubuta acan" "Ka aeko a kawo min" ta fad'a tana d'auke kae "Shikenan tunda baki shirya kar6a ba" ya fad'a yana mik'ewa ya fara takawa, babu shiri ta bud'e murfin motar ta fito tana sauke numfashi a jere a jere, murmushi ya saki lokaci d'aya yana kae hannun sa kan kwantacciyar sumar kan sa ya shafa, tana ganin ya shige cikin gidan itama ta saka k'afar ta "Barka dae Madam" Yaseer ya fad'a yana kallan ta, kamar baza tace komae ba se kuma ta d'an saci kallan sa tace ciki ciki "Ina wuni?" shi bema ji ta ba dan haka ya sake jerawa da Rk suka cigaba da tafiya se dae babu wanda ke cewa komae, ita kuma tana bayan su tana bin Rk d'in cike da sassarfa, a haka har suka k'arasa cikin parlourn "Bismilllah The great Rk" Yaseer ya fad'a yana murmushi dan sosae yaji dad'in ganin Rk d'in, shima murmushin ya maeda masa sannan ya k'arasa cikin parlourn ya zauna kan had'ad'd'iyar kujerar dake cikin parlourn, tsayawa tayi kawae tana cigaba da kallan sa, so take kawae taga ya d'auki takadda amma bata gani ba dan haka ta cigaba da tsayuwar ta "Madam ki shigo mana!" Yaseer ya fad'a yana kallan Ayrah "Rabu da ita, bata buk'atar komawa gida ne" Rk ya fad'a yana d'an kallan ta ta gefen ido, a hankali ta cigaba ta takowa zuwa cikin d'akin har lokacin idanun ta na cike da k'wallar nan, seta nemi gefen wata kujera ta zauna tana cigaba da k'ik'k'ifta idanu, murmushi Yaseer yayi dan ya fahimci kuka take 6oyewa, toh wacece ita? Ya k'agu yaji menene had'in ta da Rk d'in, dae_dae lokacin Hameeda ta fito daga d'aki sanye cikin doguwar rigar atamfa da mayafi madaedaeci, ta k'araso cikin d'akin fuskar ta d'auke da murmushi tace "Barkan ku da zuwa" ta fad'a tana neman kusa da Ayrah da bata ma kalle ta ba ta zauna "Yawwah barka dae Madam, mun same ku lafiya?" Rk ya fad'a shima da d'an murmushin dake k'ara masa kyau akan fuskar sa "Lafiya k'alau Alhamdulillah, da alama dae wannan ce sirikar tamu?" ta fad'a tana kallan Ayrahn, da kallan farko