Sashe 87
Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya za a yi yanzu?" Zura takalmi Abba yayi a k'afarsa kafin yace "Je ki shiryata bari naje na dawo yanzun." Be jira tace komae ba yayi gaba yayin da ita kuma ta koma cikin d'akin. .. Tun da suka hau motar take gwada kiran layin Rk, se dae ta kira fiye da sau 5 bata shiga ba, hakan ne yasa ta hak'ura ta maeda hankalinta kan Ayrah da yanzun take fidda numfashi a hankali idanunta a lumshe saboda wahalar da take ji, ita kad'ae ta san abin da take ji a cikin jikinta. Kae tsaye d'akin haehuwa aka wuce da ita, se dae inda akayi rashin sa'a Rk yana can yana yi wa wani aeki ne. Wata midwife ce ta kar6e ta. Su Umma na waje suna addu'a cike da fatan Allah ya sauke ta lafiya, musamman a yadda aka shiga da ita d'akin duk ya d'an so ya basu tsoro. Se dae duk da haka basu sare ba wajen duk'ufa suna addu'a. .. Da labarin da ya fara karo kenan bayan fitowarsa daga gama wancan aekin, ya duba wayarsa dake a kashe, ya san an neme shi ne ba'a same shi ba shiyasa kawae suka taho. Ya jefar da wayar kan kujera ya wuce d'akin haehuwar. Kukan Baby ne ya fara karad'e masa kunne a daidai lokacin da ya shiga d'akin, se kawae ya lumshe idanunsa a ransa yana sak'a tabbas Ayrah ta sauka. Bud'e idanunsa yayi kana a hankali ya cigaba da takawa zuwa cikin d'akin idanunsa akan hannun midwife Sa'adah da ta kar6i haehuwar Ayrahn, wadda Babyn da fitowarsa kenan yake hannunta. K'arasawa yayi cike da sassarfa, hannunsa har rawa yake ya mik'awa midwife d'in, se kuwa ta mik'a masa Babyn tana kallansa da murmushi kan fuskarta kana tace "Congratulations sir!" Daga haka ta koma kan Ayrah da take kwance kamar wadda tayi sumar wucin gadi, dan kuwa tun fitowar Babyn ta koma sharab kan gadon kamar wadda ta mutu, babu laefi ta sha wahala ba can ba, se dae daga k'arshe dae Allah ya tak'aeta ta haehu lafiya. .. Kallan kyakykyawan Baby Boy d'in dake cikin hannunsa yake yi wata irin k'aunarsa na ratsa shi, ya sake lumshe idanunsa a karo na barkatae kafin ya furta akan la66ansa "Alhamdulillahillazi bi ni'imatihi ta timmus salihat!" ya fad'a yana sauke bakinsa akan goshin yaron ya sumbace shi. A hankali ya cigaba da takawa zuwa wajen gadon, idanunsa akan Ayrah dake bacci, idan ka ganta a haka zaka yi tunanin lafiyarta k'alau, saboda yanda numfashinta ke sauka a hankali, se dae Allah ne kad'ae ya san yadda take ji, ita kad'ae ta san me take ji a jikinta. Farar fuskarta ce kad'ae zata d'an iya tona asirinta, saboda yadda tayi fayau kamar ta mara lafiya. Hannu ya kae ya kamo tattausan hannunta dake ajje gefe, ya sake k'ura mata idanu a ransa yana sake tausaya mata, kae daga ganin yaron kad'ae ya isa ya baka tabbacin ta wahala. Maeda hannunsa yayi kan shafaffen cikinta da yanzun ya koma kamar d'a be ta6a zama a ciki ba, kamar ba a jiya cikin nata yake wadda zata juye 'ya'ya uku. Ya sake kallan Babyn dake bacci calmly, murmushi ne ya su6uce masa akan fuska kafin a hankali ya saukar da kansa k'asa zuwa kan fuskarta yayi kissing cute red lips d'inta da suka sake tsukewa saboda baccin da tayi, yace a hankali kamar tana jinsa "I luv u matata. Allah ya baki lafiya." ya fad'a yana jin k'aunarta na sake dad'uwa a cikin zuciyarsa. .. Se bayan maghrib sannan suka fara shirye_shiryen tafiya gida dan kuwa a ranar aka sallameta saboda babu wata matsala, ta haehu lafiya k'alau babu wata damuwa. Shi yayi driving na su har zuwa gidan, yayi parking motarsa a k'ofar gidan kana ya fito, ba tare da damuwa da komae ba ya soma fito da kayan dake cikin motar yana wucewa da su cikin gidan. Umma ta bi shi da kallo a ranta tana sake godewa Allah na samun siriki kamar shi. Duk da yadda yake jin jikinsa babu dad'i na yadda Ayrahn zata yi kwanaki cikin gidan ba tare da shi ba hakan be hana shi kallan Umma ba yace "Bari na wuce Umma" Kallansa Umma tayi kafin tace "Toh ka shiga ka sake ganinsu?" Dama abin da yake jira ya ji kenan, se da ya d'an shafi sumar k'eyarsa kafin yace "Toh bari na je." .. A hankali ya shiga cikin d'akin, idanunsa akan gadon da Ayrahn ke kwance tana baccin da be dad'e da d'aukar ta ba. K'arasawa yayi, kae tsaye ya d'auki Babyn da shi ma yake bacci cikin kwanciyar hankali. Murmushi ya su6uce masa a karo na barkatae a yau d'in tun bayan haehuwar Ayrah. Se da ya sumbace shi a goshinsa sannan ya maeda shi kan gadon ya kwantar da shi a nutse. Yana d'ora hannunsa akan na ta hannun ta bud'e lumsassun idanunta ta sauke su a kansa. Wani tattausan murmushi ya sakar mata kafin yace cikin tausayawa "Sannu!" Lumshe idanunta tayi tana d'an yin murmushi lokaci d'aya tana rik'e hannunsa sosae cikin hannunta. "Sannu Babe!" ya sake fad'a. Bud'e idanunta tayi ta kafe shi dasu, kafin ta maeda kan Babyn dake gefenta. Ta sake lumshe idanunta a ranta tana godewa Allah tana kuma sake tsarkake shi, wae yau itace ta haehu, itace ke kwance d'anta a gefenta, lallae Allah me girma da d'aukaka. D'an rank'wafowa yayi ya sumbaci goshinta kafin ya mik'e yace "Kin yi k'ok'ari sosae Babe, Allah ya miki albarka, ya k'ara miki lafiyar da zaki ta haefa min yara masu kama dani." Da sauri ta kalle shi kafin ta maeda dubanta kan Babyn, idan dae ba idanunta ke gizo ba tun yanzun kamanninsa da Rk d'in ta soma bayyana. Cikin k'arfin tace "Lallae ma yaron nan, duk wahalar da na sha amma kamarka ya d'akko?" ta fad'a tana tura baki. Murmushi yayi yana d'age girarsa kafin yace "Ah toh ae kin san ni d'in jarumi ne, idan baki yi wasa ba gaba d'aya yaranmu ni zasu biyo." Ya fad'a yana kafeta da idanunsa. Murmushi kawae tayi tana sake maeda dubanta kan Babyn, ji take kamar kada ta dena kallansa saboda k'aunarsa ta musamman dake ratsata. "A'ah kada fa yaron nan ya k'wace min fadata." ya katseta da fad'in hakan. Se ta d'aga kae ta kalle shi, sannan tace bayan tayi murmushi "Ae kae na musamman ne Babe." Lumshe idanu yayi ya d'an gyara zamansa kana yace "Ki yi bacci, zaki sake jin dad'in jikinki" Jinjina kae tayi tana murmushi. .. Washegari tun safe Ummee da Abbu suka dira a gidan cike da farin ciki da zumud'in son ganin jikan nasu. A d'akin Umma aka sauke su, sannan Umma ta ajje musu ruwa da lemo. D'akin Ayrah ta koma ta d'auki yaron da aka shirya shi cikin wasu kaya masu kyau daga cikin kayayyakin da Rk ya aeko dasu a jiyan. Baccinsa yake yi hankalinsa kwance bayan d'azun da ya gama rikitasu da kukansa. Ummee ce ta fara kar6arsa fuskar ta d'auke da mad'aukakin murmushi. Abin da ta fara fad'i shi ne "Masha Allah, tubarkallah.. Wallahi sak yaron nan yana k'arami. Ikon Allah." dukan su murmushi suka yi har da Abbu da be gan shi ba, dama suma kuma su Umman duk sunga kamar tun a jiyan. Se da ya dad'e a hannunta da alama bata da niyyar bawa Abbu sannan yace "Toh ko dae ba za ki bani shi ba" ya fad'a yana murmushi. Itama murmushin tayi kana tace tana mik'a masa "Ga shi, ka kalle shi ka mik'o min shi, tafiyar mu daban ce dan kuwa se anjima zan taho, bayan na gama ganin d'iyata da jikana" "Lallae" shi ne abin da Abbu ya fad'a yana gyara zaman towel d'in da Babyn ke ciki. Sosae Abbu ya yiwa Ayrah sannu, sannan ya ajje mata kud'i ya yiwa Abba sallama kana ya tafi. Ita kuma Ummee ta cigaba da zama kamar yadda ta fad'a d'in. Cike da tausayawa take kallan Ayrahn hakan ne yasa lokaci zuwa lokaci se tace "Sannu kin ji Ayrah!" dan ita dae har yanzu bata dena tausaya mata ba saboda shekarunta da kuma yanayin jikinta. Sosae Umma da Ummeen suka sha hira cike da sabon da ya sake shiga tsakaninsu. Ita dae Ayrah duk ta kasa sakewa musamman da Ummeen ke cikin d'akin. Allah Allah take kada yaron nan yayi kuka ace ta shayar da shi. Se dae addu'ar ta ta bata kar6u ba dan kuwa yana tashi daga baccin da Ummee ta goya shi ya soma kuka yana lalubar hannunsa yana kaewa baki. Sakko da shi Ummee tayi tana kallansa tace "Toh ka gaji kenan!" Murmushi Umma tayi yadda Ummeen ke nuna kulawarta ga Ayrah da shi kansa jaririn na sake burgeta da yi mata dad'i. Kar6arsa Umma tayi daidai lokacin da Ummeen ta sake fad'in "Ae ya ma yi k'ok'ari bawan Allah" se ta k'arasa kan gadon ta mik'awa Ayrah shi, rau rau tayi da idanunta tana kallan Umman da kuma Ummee. Ganin hankalin Ummeen baya wajen ya sanya ta fad'in "Umma!" Kallan inda Ayrahn take kalla Umma tayi kana ta juyo ta kalleta, tayi murmushi tana girgiza kae, kafin tace komae ma Ummee ta fita daga d'akin, bata san me ya fitar da ita ba, dan bata nuna ta gansu ba. Se a lokacin sannan Ayrah ta kar6i Babyn da sauri, Umma ta taemaka mata saboda jikinta har lokacin babu k'wari. Ummee bata bar gidan ba se da maghrib. A k'ofar gidan ta had'u da Yah Sadeeq da ze shiga cikin gidan. Ya dakata ya gaeshe ta, ta amsa cikin sakin fuska kafin ta wuce inda motarsu ke tsaye. Shi kuma cikin gidan ya wuce kae tsaye zuwa d'akin da Ayrah ke ciki. Da sallama ya shiga d'akin, suka amsa masa dukan su kafin ya k'arasa shiga cikin d'akin. Babyn na hannun Umma da ta gama saka masa rigar sanyi saboda yanayin gari da ake sanyi, se mutsu_mutsu kuwa yake yi manyan fararen idanunsa masu d'auke da wasu kyawawan dogayen lashes tarr a bud'e. Hannu Yah Sadeeq ya mik'a yana fad'in "Umma ba ni shi" Mik'a masa tayi bayan ta sake lullu6e shi da wani tattausan towel, ya kar6e shi kafin ya koma ya zauna akan kujerar yana