← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 90

Sashe 19

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dae na gama" jinjina kae Ruks tayi sannan tace "Gaskiyane, sannu da k'ok'ari, ni kam dae ina kusa da ke" "Toh" Ayrah ta furta dan ita sam bata da k'yashi a rayuwar ta, bata k'i duk abinda ta karanta kema ta baki ki rubuta ba, se dae abin nata har da rashin wayo da ga6un ta, dan kuwa zata iya bud'e miki paper ta kiyi copying ba abinda ya dame ta, Bahijja dake saka takalmi tace "Wallahi dama ni topic d'in daya gama mana last week kawae na karanta, couz ina da tabbacin a cikin sa zeyi tambaya" dariya Jidda tayi sanda take k'ok'arin ficewa daga d'akin tace "Ashe duk gwara ni ma, cha66.." tayi maganar tana ficewa daga d'akin, suma duk se suka rankaya suka fice daga cikin d'akin zuwa class. Sanda suka je 8 ba tayi ba dan haka sun riga shi zuwa, seda suka je da wajen mintuna 5 sannan yazo, tunda suka shiga ajin ta d'auko littafin ta ta cigaba da dubawa, Ruks da Bahijja sune a gefe da gefen ta yayin da Jidda ke kusa da Ruks, tun ranar data fahimci su zaman baya kamar a jikin su yake seta k'yale su kawae ita take zaman ta a gaba, se dae wani lokacin ne se suma su zauna a gaban, musamman kuma idan za'ayi test se duk su dawo gaban ko dan ta taemaka musu saboda yadda suka fahimci yanda kwanyar ta ke ja. Cikin takun nutsuwa yayi parking motar sa a bakin ajin, a hankali ya saka hannu ya zare bluetooth d'in dake kunnen sa ya ajje shi kan d'aya kujerar sannan ya cigaba da danna wayar sa, seda 8:00 ta buga sannan ya bud'e k'ofar ya fito bayan ya d'auki wasu books dake a back seat, sanye cikin k'ananan kaya kamar koda yaushe, kayan dake matuk'ar yi masa kyau, su sake fito da zalla kuma aenahin kyan sa, cikin nutsuwa ya cigaba da takawa zuwa ajin, kafin ya shiga wad'anda zuwan su kenan suka yi wani irin sauri suka shige ajin dan kada ya riga su shiga, yana shiga kuwa gaba d'aya en ajin suka nutsu "Wow! Kamar ko yaushe dae" taji Ruks dake gefen ta ta fad'a, shiru tayi dan tasan da wanda take, ita kuwa haka kawae take gujewa kallan inda yake, saboda yadda kallan nasa ke yawan haefar mata da fad'uwar gaban data rasa dalilin sa, ita har yanzu dukan su mamaki suke bata idan ta kalli yadda dukkan su suke crushing akan abu d'aya, kuma a gaban juna zasu zauna suna kod'a shi kowacce ta kawo nata point d'in, seta ta6e baki kawae a ranta tana ayyana "Meya shafeni ni?" kafin a fara test d'in abinda be yiwa su Bahijja dad'i ba shine yadda ya tarwatsa kan en ajin ta hanyar bawa monitorn su umarni, cikin lokaci k'ank'ani kowannen su aka tarwatsa shi zuwa wani wajen, sannan ya bada minti 20 kawae kowa yayi submitting test d'in sa duk da uban tambayar da yayi musu, duk da tambayar guda 2 ce amma idan baka nutsu ka fahimce ta ba yanzun nan zaka yi kwa6a, saboda haka daga wajen mutane da dama basu wani tsaya sunyi nazari ba kawae suka shiga amsa ta, se kuma wani 6angaren da suka tsaya suka yi nazari sosae akae, cikin su ne hadda Ayrah a ciki wadda seda ta shafe wajen minti 5 tana nazarin questions d'in kafin tayi bismilllah ta fara rubutu cikin k'warewa "Time taken" ya furta a nutse bayan cika mintuna 20 d'in daya bayar, mik'ewa Monitorn nasu yayi yabi kowa ya kar6a paper sa, wasu duk suka baada yayin da wasu k'alilan basu bayar ba saboda basu gama ba, Monitorn bebi ta kansu ba ya had'a paper hannun sa yabi bayan Rk daya fice daga cikin ajin har zuwa motar sa, ya bud'e ya shige motar sannan Monitorn ya ajje masa papers d'in a front seat, dae_dae sanda yake tada motar su 3 suka fito, Ayrah se wata er ajin tasu Fateema, sannan wani su kad'ae ne basu bayar ba, Monitor ya kalle su sannan ya kalli Rk yace a hankali "Sir.. Pls wad'anda basu bayar ba!" da mamaki Rk ya kalle shi kamar ba zece komae ba se kuma yace "Saboda raeni?" da sauri ya girgiza kae lokaci d'aya yana furta "No sir, ina sauri ne ban kar6i ta sun ba saboda kada dukan mu mu rasa, Sorry sir" "Leave them, next tym zasu yi saurin baka.." yayi maganar sanda yake maeda kan sa kan driving d'in daze soma "Pls Sir, ayi musu hak'uri ba dan halin su ba" yayi d'an shiru sannan yace bayan ya fesar da iska daga bakin sa "Su wakilta mutum d'aya a kae min office" ya fad'a yana yin gaba "Thank u so much Sir" Monitorn ya fad'a yana mik'ewa tsaye zuwa bakin class d'in, daga inda take ta runtse idanun ta tana ganin kamar tun yanzu tayi failing course d'in tunda gashi ta rasa C.A, tana shirin komawa cikin ajin hannun ta akan fuskar ta tana ji kamar ta fashe da kuka ta jiyo muryar Monitorn nasu na fad'in "Ayrah.." seta dakata lokaci d'aya tana juyowa, ya kalli yanda fararen idanun ta suka sauya kala sannan yace bayan yayi murmurshi "Doctor yace a cikin wad'anda ba kuyi submitting Paper ku ba ku wakilta mutum d'aya ya kae masa" lumshe idanun ta tayi tana jin wani irin dad'i na ratsa ta, seta kalli Fatima dake gefen ta itama rik'e da tata Paper a hannun ta tace tana kallan namijin da shima be bada ba, bata san sunan sa ba dan ita harkar matan ajin nasu ma bata kowa take shiga ba ballantana ta mazan ajin nasu "Gashi zaka kae masa?" ta k'are maganar tana kallan sa, Monitor ya kalle ta yace "kin san yadda za'ayi? Ki kar6i Paper su ki had'a ki kae masa" da mamaki ta kalle shi jin furucin sa kafin tace komae ya sake jinjina kae, da sauri ta girgiza kae sannan tace da sauri tun kafin ma ya sake cewa komae "A'ah ba zan iya ba.." tayi maganar da dukkan gaskiyar ta, dan a yadda take ji koda za'a ce sun rasa exam ne ba C.A ba ba zata iya zuwa wajen mutumin ba, cikin maraeraecewa Fateema tace "Don Allah Ayrah kije ki kae kin ji?" "Toh ke waya hana ki zuwa?" ta fad'i abinda take sak'awa cikin ran ta, kafin duk suce komae ta sake fad'in "Babu inda zan je ni" tayi maganar kamar zata saka kuka, hannu Monitor ya saka ya kar6i takaddun hannun su duka har ta Ayrah sannan yace "Zo muje mu kae masa" tunda taga ya kar6a se kawae ta bishi a baya kamar wata doluwa, a haka har suka k'arasa Office d'in Rk, seya kalle ta bayan sun dakata daga tafiyar yace "Kinga abinda yasa nace ki kae masa da kan ki, su Fateema sun fiya kaud'i, kuma kin san halin doctor.. kada suzo su janyo muku shiyasa nace ke kije, yanzu dae kije ki kae kada lokaci ya k'ure yace baze kar6a ba" hannu ta sanya ta kar6a fuskar ta a cunkushe, sannan ta runtse idanu tana karanto addu'ar da duk tazo bakin ta kana ta fara takawa zuwa bakin Office d'in, da sallama d'auke akan la66an ta ta shiga cikin Office d'in, ba tare data kalli kowa ba ta zube akan k'afafun ta, wani irin sassanyan k'amshi ke tashi cikin Office d'in, wanda ya had'e da k'amshin turaren sa da kuma shi kan sa na Office d'in ga kuma sanyin A.C hakan ba k'aramin k'arawa yanayin Office d'in dad'in shak'a yayi ba. Da mamaki Muneerah dake zaune kan kujera ta kalle ta, seta saka hannu ta zame k'aramin glass d'in dake fuskar ta ta cigaba da kallan ta "Malama menene zaki shigowa mutane waje without even taking excuse?" taji maganar daga gefen ta, idan kujerar da Muneerahn ke kae ta d'ago ta kalle ta toh Ayrah ma ta kalle ta, seta d'aga kae a hankali ta kalli inda yake zaune kan kujera yayi shiru hannayen sa rik'e da ha6ar sa kamar me tunani "Sir.." karo na farko kenan data ta6a yi masa magana, ita bata so ma hakan ta faru ba, so tayi har ta gama makarantar wata magana ba zata ta6a had'a ta da shi ba, idanun sa masu kaefi ya d'aga ya kalli Muneerah dake sake fad'in cikin kufula "Kamar dake nake koh?" lumshe idanun ta Ayrah tayi ba tare data juya ta kalli Muneerah ba tace "Sir test d'in mu na kawo.." tayi maganar tana mik'ewa daga zaunen da take ta ajje masa kan bench d'in dake gaban sa, jin bece komae bane ya sanya ta mik'ewa tana jin k'irjin ta na bugawa lokaci d'aya kuma tana fatan Allah yasa kada yace wani abun, ya kar6a kenan "Don't ever try dis mistake again.." ta jiyo daddad'ar muryar sa yana fad'in hakan kuma a hankali kamar wanda akawa dole, ba tare data kalle shi ba ballantana bugun zuciyar ta ya k'aru tace "In Sha Allah" tana shirin fita ta jiyo muryar Muneerah na fad'in "Kin ci sa'a yau an miki uzuri, saboda haka se ki kiyaye" ta fad'a ita a lallae dole se an gane wata ce ita a wajen Rk d'in, kallan ta kawae Ayrah tayi tana jin wani irin takaeci da haushi na musamman na zuwa suka tirnik'e ta, dan haka yanzu ma ba tace komae ba se sake d'auke kan ta da tayi, daga haka ta sanya k'afa ta fice daga Office d'in, galala Muneerah ta bita da kallo sanda ta gama ficewa daga Office d'in sannan ta dawo da duban ta kan Rk tace "Baby wannan d'alibar ka ce?" kallan Muneerah yayi kallo irin na cikin ido wanda ya sanya ta kauda kan ta gefe se dae har lokacin bata ji yace komae ba dan haka ta sake furta "Baka tunanin shirun da ka mata bayan abinda tamin kamar ze janyo min raeni ne" "Meye had'in ki da ita?" yayi maganar cikin basarwa, se tayi shiru kawae tana mamakin wannan mutumin, yaja Papers d'in data kawo ya had'a su da ragowar sannan ya mik'e yana zura wayar sa cikin aljihu yace "Zan fita" "Da wuri haka Baby? Ina zaka je?" yamutsa fuska yayi ba tare da
Chapter 19 · 0% Book details