← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 90

Sashe 72

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zamu yi ko kwana zan yi?" kallan ta ya cigaba da yi kafin ya d'auke kan sa yana dafe kan nasa, se a lokacin ya tuna da tafiyar su Zaria, ba dan tare da Abbun zasu je ba babu abinda ze hana shi tafiya da matar sa, se dae duk da haka ba zeyi sakacin barin ta gida d'aya da Muneerah ba dan haka yana ganin mafita d'aya ce ya bar ta a gidan su har ya dawo. A hankali yace "Zaria zan je na en kwanaki.." yayi maganar idanun sa akan fuskar ta, da sauri ta juya ta kalle shi ido cikin ido, se ya samu damar cigaba da kallan ta da kuma karantar yanayin ta, cikin lokaci k'ank'ani idanun ta suka tara k'walla, lokaci guda kuma taji bugun zuciyar ta ya k'aru, ba tare data san abin da ke cikin zuciyar ta ne ya fito fili ba tace "Kae da wa zaka je?" "Abbu" ya bata amsa da sauri musamman da ya fahimci abin da zuciyar ta ta hasaso mata. Bata san sanda wata k'atuwar ajiyar zuciya ta k'wace mata ba wadda hatta shi kan sa se da ya jiyo ta, be san sanda wani murmushi ya k'wace masa ba, ya sanya hannun sa kan kwantacciyar sumar dake kwance luff akan ha6ar sa yana kallan ta. Se ya saka hannu ya janyo ta ganin har lokacin tak'i yin murmushi ko ta saki jikin ta tunda yayi maganar tafiyar, ya ja ta cikin jikin sa ya rungume ta sosae yana sauke ajiyar zuciya, haka kawae yau d'in ta ji wani sanyi na ratsa ta sanda ta ji ta cikin jikin na sa, hakan ne ya sanya ta yin shiru tana sauke numfashi a jere a jere saboda zuciyar ta dake a kusa, bata san meyasa tunda yayi maganar Zarian ran ta ke a 6ace ba, duk da ya fad'a mata shi da wa zasu je, haka kawae take ji bata so ya tafi wani garin yayi nisa da ita. Bakin sa ya matsar saetin kunnen ta kamar me rad'a yace "Babe zan yi kewar ki, zan yi kewar komae na ki Babe.." ya k'arasa maganar yana lumshe ido gami da shak'ar k'amshin da ke tashi daga cikin jikin ta. Duk kuma se taji kunya ta kama ta hakanne ya sanya ta rik'o shi dan mik'ewa daga jikin sa, shi kuma yayi saurin sake rik'o ta yana fad'in, "Pls Babe ki bar ni naji d'umin ki sosae yau d'in nan kada ki hana ni" yayi maganar yana sake cusa kan sa cikin doguwar bak'ar sumar kan ta da mayafin ya sa6ule ya koma kan kafad'ar ta, duk da yanda zuciyar ta ke bugawa cike da tsoron dake son shigar ta hakan be hana ta yin shiru a jikin nasa ba, tana jin sanda ya d'auki hannayen ta duka biyun ya zagaye jikin sa da shi ya kuma gyara musu kwanciya akan kujerar. "I luv u" ya fad'a cikin wata shak'ak'k'iyar murya yana kuma lumshe idanun sa da suke lumshewa dan kan su. Itama lumshe na ta idanun tayi sannan ta soma bud'e bakin ta da niyyar fad'a masa kalmar da ya fad'a mata se taji wata k'walla ta taho mata, babu 6ata lokaci ta sauka akan kuncin ta, har ga Allah bata son tafiyar nan ta sa ko kad'an. Jin da yayi kamar wani abu na sauka kan rigar sa ne ya sanya shi d'ago fuskar Ayrahn ya zuba mata lumsassun idanun sa kana yace "Subhanallahi, Babe meya faru? Ni ne?" jinjina kae tayi da sauri wasu hawayen na sauka akan fuskar ta, ya d'an lumshe idanun sa kafin yace cikin er rud'ewa "Me nayi Uhmm?" "Ba kae ne zaka tafi ka bar ni ba" tayi maganar a raunane tana kae hannun ta kan fuskar ta ta share hawayen da suka k'i tsayawa da zuba akan fuskar ta. Murmushi me k'ayatarwa yayi kana ya sake jan ta ya rungume ta tietly a cikin jikin sa, a zuciyar sa yana fad'in "Rigimammiya tah" Mhiz Innocent... https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* Page 053 ___Sun kae wajen minti 1 a hakan kowanne na cigaba da jin yadda zuciyar d'an uwan sa ke bugawa, kana a hankali ya soma sassauta rik'on da yayi mata, kafin daga bisani ya d'ago ta gaba d'aya. K'ura mata lumsassun idanun sa yayi se dae a wannan lokacin itama cigaba da kallan sa tayi tana ji kamar kada ta dena. A hankali ya d'an lumshe idanun sa kafin yace komae Ayrah ta k'arasa zame jikin ta daga na shi zuwa kan kujerar gefen sa tace bayan ta kautar da idanun ta daga kallan sa. "Kada Umma taga na dad'e toh" dariya yayi sosae dan har seda fararan hak'oran sa suka bayyana kafin yace, "Fad'a zata yi?" ya tambaya yana d'age girar sa ta dama yana kuma kallan ta. Kallan na sa itama tayi kafin tayi shiru tana nazarin tambayar ta sa, se kuma itama taji dariyar ta kama ta hakan ne yasa ta dara har da rufe baki, shi kuwa ya shagala da kallan ta har zuwa sanda tace "Aou.." se kuma tayi shiru, yayi murmushi kawae yana girgiza kae. Basu jima cikin motar ba jefi jefi suna yin magana duk da kallo yafi yawa a zaman na su, dan haka daga k'arshe suka yi sallama cike da kewar junan su kafin Ayrah ta koma gida. ... Da sallama ya shiga Parlourn Muneerahn cikin takun nan na sa na nutsuwa me kuma jan hankali, ta kalle shi daga inda take zaune ta amsa kafin ta mik'e tana shirin k'arasowa wajen sa, se ya nemi waje ya zauna kana yace "Zauna muyi magana" ta6a fuska tayi kafin ta sake yamutsa ta se kuma ta koma ta zauna d'in, se da ya d'an sauke numfashi kafin yace, "Gobe idan Allah ya kaemu zamu je Zaria, so ba da kowa zan je a cikin ku ba, ita na bar ta a gida ke kuma se ki zauna a gidan nan" Kallan sa take yi kamar me son gano wani abu daga cikin fuskar sa, lokaci guda kuma wata zuciyar ta ta zuga ta, wato kenan ita waccan me iyaye, ita Ayrah tana wajen iyayen ta, wato kenan ita kuma ta zauna anan gidan kamar wata mara galihu, hakan ne ya sanya ta fad'in "Don Allah zan bi ka" "Nop, na gama magana" yayi maganar yana mik'ewa, da sauri itama ta mik'e tace kafin ya soma tafiya, "Idan kana k'aunar Allah zan bi ka" juyawa yayi ya kalle ta kamar ba Muneerahn ba, ya d'an d'aga kafad'ar sa yana ta6e bakin sa lokaci guda kafin yace "Alright na ji, amma aeki ne ze kae ni saboda haka a gida zaki zauna idan na gama se mu dawo tare" seda ta lumshe idanun ta sannan tace "Tohm" ko babu komae zata had'u da Mummyn ta, kuma ta san Mummyn zata saeta mata hanya akan wasu abubuwan tunda dae gata gata ba kamar yanzun ba da kowa ke wani garin ba. "Ki had'a abin da zaki buk'ata kafin gobe" cikin farin ciki ta furta "An gama" Shi dae be sake cewa komae ba ya fice daga d'akin, ta bi shi da kallo tana ji kamar ta janyo goben dan farin ciki. Kae tsaye part d'in sa ya wuce, tun kafin ma ya k'arasa ya d'auki wayar da ya danna kiran Abbu, bayan ya d'aga suka gaesa sannan yace "Abbu goben idan Allah ya kaemu da Muneerah zamu je, itama tana so ta je taga gida" shiru Abbu yayi na en wasu sakanni kafin yace, "Idan akayi haka anya kuwa anyi adalci?" murmushi Rk yayi dae_dae lokacin da ya ida shiga cikin d'akin sa yace "Abbu ae dan gidan su a garin yake ne shiyasa" ajiyar zuciya Abbu ya sauke yace "Toh shikenan, Allah ya kae mu" "Ameen" Rk ya fad'a yana katse wayar. ... A d'aya 6angaren kuwa wajen k'arfe 8 ne na yammacin ranar Umma ta shigo d'akin Ayrah da sallama, Ayrah ta amsa mata sallamar tana tashi daga kwancen da take, se da ta d'an murza idanun ta sannan ta bud'e. Umma ta k'araso ta zauna kusa da ita, kamar jira take yi se ta d'ora kan ta dake bud'e babu d'an kwali akan cinyar Umman, murmushi Umma tayi tana shafa gashin Ayrahn kafin tace "Dole ma na kitse miki wannan kan kafin ki bar gidan nan" kwa6e fuska tayi tace kamar zata yi kuka "A'ah don Allah Umma bana so" "Zama ki so ne" Umma ta fad'a tana d'an yin shiru kafin tayi k'asa da muryar ta tace "Babu dae wata matsala koh Auta? Ina nufin ko akwae wani abun da ya shige miki duhu ko kuma matsala tsakanin ki da abokiyar zaman ki.." d'an shiru tayi kamar me nazari hakan ya sa Umma cigaba da kallan ta tana karantar yanayin ta, kamar wadda ba zata ce komae ba se kuma can tace "A'ah Umma ba matsala fa" "Kin tabbatar?" Umma ta tambaya dan sake tabbatarwa, se ta jinjina kae kana tace "Ehh Umma" Ajiyar zuciya Umma ta sauke, wajen second 30 sannan tace "Ki tashi na had'a miki ruwa me d'umi a ban d'aki ki samu ki gasa jikin ki, zaki ji dad'in jikin ki sosae" Umma ta fad'a tana sa6ule kan Ayrah daga kan cinyar ta ta ajiye akan gadon. Ba tare da kawo komae ba Ayrah tace "Toh" ita kuma Umma ta fice daga d'akin. Mamaki ne ya kama Ayrah tabi Umman da kallo tana mamakin abin da ya sa ta fice daga d'akin hakan, se tayi shiru tana tuna maganar da Umman ta fad'a, tuna abin da ya faru d'azu da safe da kuma maganar Umma ya sanya ta sakin k'aramar k'ara tana kifa kan ta akan gado cike da matsananciyar kunya, lokaci d'aya kuma k'walla na taruwa a idanun ta. "Dama ae se da nace masa za'a gane" tayi maganar a fili tana jin yadda k'wallar ta sakko mata akan fuska, ita yanzu da wane ido zata dinga kallan en gidan na su? Ba abin tayi kwanciyar ta ba tace ba taji ba, ta san wannan maganar ma bata ta so ba tunda dae ta riga ta amsa, ita kam ya zata yi? Tafi minti 2 a haka tana sak'awa da warwarewa da taga dae
Chapter 72 · 0% Book details