Sashe 55
Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wanzu akan fuskar ta sanda Bahijjan ta shigo cikin gidan, itama k'ok'ari tayi ta wanzar da murmushin kan fuskar ta duk da yanda take jin haushin Ayrahn a cikin zuciyar ta "Sannu da zuwa" shine abinda ta fad'a bayan ta kulle k'ofar gidan "Yawwah" Bahijja ta fad'a tana yin gaba, dan ita burin ta kawae su zauna ta fara tuhumar Ayrahn. Tsayawa tayi tana kallan parlourn daya gaji da had'uwa kafin ta ta6e baki ta nemi waje ta zauna, Ayrah bata zauna ba seda ta d'akko mata ruwa da lemo tazo ta ajje mata sannan ta koma ta zauna akan kujerar "Sannu da zuwa, ya hanya?" ta sake fad'i, dan ba k'arya taji dad'in zuwan Bahijjan, ko ba komae ta nuna mata ana tare "Hanya Alhamdulillah, kin ga ae bana zauna ban je na gaeda Mama ba koh? Muhimmiyar magana ce ta kawo ni, saboda haka muje ki raka ni na gaeda Mama kafin nan semu zauna" Bahijja ta fad'a tana mik'ewa, murmushi Ayrah tayi ta saka hannun ta ta murza zoben hannun ta sannan tace "Umma na gida ae" cikin rashin fahimta Bahijja tace "Gida kuma? Nan d'in ina ne toh?" "Gida na" ta fad'a bayan ta d'an tura bakin ta ta kuma jefawa Bahijjan harara, wani irin sanyi ne ya shiga ratsa Bahijja, se ta nemi waje ta zauna tana jin yadda farin ciki ke ratsa ilahirin jikin ta "Ashe dama kina da aure bamu sani ba?" Bahijja ta tambaya a ran ta tana tuna yadda Abeedah ta nuna musu hoton Ayrahn da doctor a wajen cin abinci, ita dama seda tayi mamaki ace Ayrahn ce taci amanar su, ashe tana da aure tuntuni, dan kuwa ta san dae baze yiwu ace seda ta dawo daga makaranta sannan akayi auren ba "Ehh" kawae ta fad'a dan bata san jan dogon zance, ajiyar zuciya Bahijja ta sauke tana jin yadda abubuwa suka zo mata da sauk'i, duk burin da taci na zuwa Kanon ya zagwanye, se a lokacin ta saka hannu ta d'auki ruwan ta sha kana ta samu sukuni ta furta "Se gani a gidan ki? Amma dae baki kyauta mana ba da baki fad'a mana kina da aure ba wallahi" "Uhmm" kawae Ayrah ta furta kamin tace "Ya hutu? Ina Mama?" "Mama na nan k'alau, hutu kuma muna nan muna shan shi" ta fad'a har lokacin farin cikin da taji na jin Ayrahn na da aure be sake ta ba. Ba ita ta fara shirin tafiya ba se dab da maghrib sannan ta mik'e ta yafa mayafin ta kana ta d'auki jakar ta tace "Toh bari na koma, na ga gida Allah ya k'aro zaman lafiya" ta fad'a tana yin gaba, bin bayan ta Ayrah tayi tana mata godiya dan babu k'arya taji dad'in ziyarar nan data kawo mata, har compound d'in gidan ta rako ta tana sake maemaeta mata ta gaeda mata da Maman su, tace zata ji. Dae_dae lokacin da suka fito d'in yayi dae_dae da lokacin da motar sa ta kunno kae cikin gidan, dukan su dakatawa suka yi, Bahijja na lek'a kan ta cikin motar ko zata hango mijin Ayrahn, dan tana da tabbaci kamar yadda Ayrahn take kyakykyawa haka mijin ta ma ze kasance, dan kada dae Ayrah ta fahimci gulma ce ta tsaeda ta ya sanya ta fad'in "Bari na tsaya mu gaesa, kin ga babu dad'i tunda ya shigo har gidan mun had'u kuma in tafi bamu gaesa ba" d'an murmushi kad'an Ayrah ta saki sanda ta k'arasa wajen motar ta sa, dae_dae lokacin da shi kuma ya fito daga cikin motar, tattausan murmushi ya sakar mata ganin ta yau a compound d'in gidan, dan kuwa ko parlour da wuya ka gan ta a ciki, kullum tana bedroom d'in ta, sam be lura da wata halitta dake d'an nesa kad'an dasu ba, babu 6ata lokaci ya bata wata kyakykyawar runguma lokaci d'aya yana sauke ajiyar zuciya saboda yanda yaji wata nutsuwa na saukar masa "Ina da bak'uwa fa" ta fad'a tana tura baki "Bak'uwa kuma?" yayi maganar a hankali, seda ta sake kumbura bakin sannan tace "Ehh fa, er makarantar mu ce" da mamaki ya sake ta a hankali sannan ya maeda duban sa inda take kalla, dae_dae lokacin da Bahijja ta runtse idanun ta dan sake tabbatarwa da kan ta abinda idanun ta ke gani, ba tare da sun lura da yanayin da take ciki ba Ayrah tace a hankali "Kae take jira zaku gaesa" "Ni kuma?" ya fad'a cikin basarwa, seta jinjina kae kawae, a nutse suka soma takawa zuwa inda Bahijjan take, mutuwar tsaye tayi sanda taga sun iso dab da ita kuma idanun ta sun sake tabbatar mata lallae wannan d'in Doctor ne, Doctor Rk ne. "Innalillahi wa inna ilaehi rajiun" ta dinga maemaetawa a cikin zuciyar ta jikin ta a matuk'ar sanyaye yana wata irin rawa kamar mazari, lumshe idanun ta tayi ta sake bud'ewa still dae akan Rk dan har yanzu tantama take yi "Kina lafiya?" ya fad'a yana tamke fuskar sa ganin irin kallan da take bin sa da shi kamar wadda taga sabon halitta, da k'yar ta i ya fuzgo kalmar "Alhamdulillah" ta fad'a a lokacin data sake tabbatar da lallae Doctor ne, shine mijin Ayrahn dama? Yin gaban da Rk yayi ne ya sanya ta kallan Bahijja tace "Bahijja ki gaeda gida na gode" "Uhm hum" shine kawae abinda ta iya furtawa dan kuwa a yanda take jin ta ba zata iya doguwar magana ba, da k'yar ta iya jan k'afafun ta ta fice daga gidan kan ta a matuk'ar kulle. .. "Ke lafiya?" Aunty Zeenah ta fad'a tana kallan Bahijja da ta shigo cikin d'akin kamar wata korarriya, yak'e tayi kana tace "Lafiya k'alau, bacci kawae nake ji saboda gajiya" "Toh maza je ki kwanta, bari na kawo miki abinci" girgiza kae kawae tayi da sauri tace "A'ah naci acan, Aunty kada a tashe ni don Allah" "Toh seda safe" Aunty Zeenah ta fad'a tana sake bin ta da kallo ganin yanda yanayin ta ya chanja lokaci d'aya, bata sake cewa komae ba ta ja k'afafun ta da suka yi mata nauyi ta wuce cikin d'akin da Muneerahn ta sauke su. Se a lokacin ta samu damar fashewa da kuka kamar ran ta ze fita, kukan takaeci, yarinyar nan ta shammace su, se dae abinda bata sani ba dama can matar sa ce ko kuma se daga baya ne suka yi aure? Idan kuwa hakane yarinyar tayi amfani da yadda suka d'auke ta kamar yarinya ta cuce su ta yaudare su, ashe itama tana son sa? Gaba d'aya kan ta a kulle yake, man kan ta gaba d'aya ya tsiyaye, wani irin bak'in ciki ne ke cigaba da ziyartar ta musamman idan ta tuna yadda Doctor d'in ya rungume ta a gaban ta, kawae seta koma ta kwanta dan samawa k'wak'walwar ta hutu dan kuwa ko tace zata yi tunanin mafita k'arya take yi. ... Washe_gari Bahijja da k'yar ta iya farkawa daga bacci saboda yadda kan ta ya mata wani gingirin, kasancewar bata sallah ya sanya tana tashi d'in wanka kawae tayi sannan ta shirya da k'yar ta fito saboda kada Auntyn ta fahimci tana cikin wani hali, a parlour ta samu Auntyn da Muneerah zaune suna hira, ta k'arasa ta nemi waje ta zauna kana ta kalli Muneerah tace "Kin tashi lafiya?" "Lafiya K'alau Bahijja, se yanzu kika tashi duk uban baccin da kika sha jiya?" "Wallahi kuwa" ta fad'a tana yamutsa fuska kafin ta maeda duban ta kan Aunty Zeenah "Aunty ina kwana?" "Lafiya K'alau" Auntyn ta fad'a tana kafe Bahijja da idanu kamar me son gano wani abun se kuma ta d'ora da "Anya kuwa lafiyar ki k'alau Bahijja?" "Lafiya ta lau Aunty, kawae dae gajiya ce" ajiyar zuciya Auntyn ta sauke kafin tace "Hakane kuma" daga haka suka cigaba da hira. Suna nan zaune ya shigo da motar sa cikin gidan, Muneerah ta kalli Aunty Zeenah tace "Gashi nan ya dawo Aunty" "Toh je ki tarbe shi hannu bibbiyu kin san fa yau zuwa gobe nake so a gabatar da komae" murmushi Muneerah ta saki kafin tace "Toh" daga haka ta fice daga d'akin, bata tsaya ko ina ba se wajen motar ta sa, ta sanya hannun ta akan hannun k'ofar tana bin sa da wani shu'umin murmushi "Sannu da zuwa Baby" da mamaki yake kallan ta dan shi kam a wajen sa wannan sabon abu ne dan kuwa hakan bata ta6a shiga tsakanin su ba, ganin yana kallan ta ne ya sanya ta yin farr da idanun ta tana jin wani irin dad'i na ratsa ta "Yawwah kina lafiya?" ya fad'a sanda ya fito daga cikin motar, shine yayi gaba yayin da ta rufa masa baya, yana dab da wuce part d'in ta tace "Amm, k'anwar Mummy tazo gidan nan, idan babu damuwa kaje ku gaesa mana" seda ya dakata kad'an sannan yace "Ohk, je ki ina zuwa zan amsa waya ne" yayi maganar yana yin gaba, da "Toh" ta amsa itama tana yin gaba ta wuce cikin d'akin ta. Da wani kallo Aunty Zeenah ta bi ta ganin ta ita d'aya "Me mijin nan naki ke nufi ne? Ni ce zan je na gaeda shi ko kuwa me yake nufi?" ta6e fuska tayi tana k'arasowa ta zauna "Kae Aunty Allah kuwa kin fiya mita, waya yake amsawa yanzu ze shigo" "Aou toh, yanzu naji batu" Aunty Zeenah ta fad'a tana gyara zama, cigaba da zama Bahijja tayi duk da yanda tunanin ta ke wani wajen, jira kawae take lokacin data d'iba ya cika ta koma d'akin ta cigaba da tunanin mafita, dae_dae lokacin da muryar sa me dad'in sauraro ta ratso cikin parlourn, suka amsa sallamar kusan a tare kafin ya k'araso ya nemi side chair ya zauna kafin ya d'an zame yace "Barka da safiya" "Barkan ka dae, ya gida? Ya amarci?" tayi tambayar kamar ba uwar amarya ba, dae_dae lokacin da Bahijja ta d'aga idanun ta dan ganin me fuskar da taji kamar muryar ta sake mata kama data abin k'aunar ta ta, se dae ga mamakin ta se idanun ta suka sake gane mata Rk, a'ah kada dae ace ta haukace fa ta fara gane_gane, abinda ta raya a ran ta ne ya sanya ta saurin runtse idanun ta sannan