Sashe 7
Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
babba, tayi ta bin kujera tana kwanciya kamar zata yi kuka, idan kuwa da rana ne ko a makaranta in dae basa cikin aji toh zaka same su ne kullum tare da juna, wata iriyar shak'uwa suka yi mara misaltuwa ko iyayen Raj d'in ma abin har mamaki yake basu, sunan Raj kuwa seda Ayrah ta lak'abawa kowa, daga zarar kace masa Suraj za tace ba Suraj ba Raj, kuma in zaka kwana kana fad'ar Suraj itama zata kwana tana gyara maka, dan haka yanzu en gidan su ma kwata kwata Raj d'in suke ce masa, Iyayen sa ne dae suke k'ok'arin ce masa Raj d'in ko dan Ayrahn musamman idan a gaban tane, shi kansa yanzun yafi jin dad'in Raj d'in kuma babban dalili daya kasance Ayrah ce ta saka masa sunan. A cikin shekarar da taemakon Allah komae ya cigaba da bud'ewa Abba, seya kasance ma yanzun ya zuba atamfofi ne kala kala kuma masu yawa, sosae Abbu ke taemaka masa ta hanyoyi da dama, dan yanzun ya gama sakar masa komae, ko menene in dae shi da kansa ze iya yi toh fa ze iya d'ora Abbu akae saboda yadda yayi na'am dashi, haka suka cigaba da tafiyar da shagon su 2, sosae abubuwa da dama na Abban suka chanja ciki kuwa hadda cimar gidan sa da suturun da shi kansa da iyalan sa kan saka da kuma sauran abubuwa makaman tan wannan, shi kansa Abbu ba'a barshi a baya ba dan kuwa yanzun rayuwa suke cikin kwanciyar hankali babu yunwa babu komae, dan a lokacin ma seda ya nemi Abba ya sakar masa harkar makarantar Raj amma Abba yace a'ah tunda ya fara shi ze k'arasa In Sha Allah, beyi musu ba se k'ara godiya da yayi, godiyar da kusan kullum se yayi ta baya gajiya da ita. _*MAFARI*_ ... Da sallama Abba ya shigo gidan kamar koda yaushe hannun sa d'auke da ledar daya saba shigo da ita kusan kullum wanda hakan ma ya riga ya zame masa jiki, in dae ze dawo gidan toh In Sha Allah ze siyo wani abun ya tahowa da iyalin nasa shi, da gudu ta sauko daga kan kujerar ta k'arasa ta rungume Abban tana fad'in "Abba Sannu da zuwa" "Yawwah an baby.." "Abba meka siyo min?" ta fad'a tana murmurshi, shima murmurshin yayi sannan yace "Kar6i maza ki kaewa Umman ku, ina take?" seda ta sanya hannu ta kar6a sannan tace "Tana kitchen" daga haka tayi hanyar kitchen d'in tana kiran sunan Umma, Raj dake zaune kan kujera ya sakko a hankali ya furta "Abba sannu da zuwa" "Yawwah sannun kadae" Abban ya fad'a yana wucewa d'akin sa... Seda ya samu yaci abinci a cikin parlourn sannan Umma ta gabatar masa da ruwa ya sha kana yace "Dama akwae maganar dana ke so muyi" gyara zama Umma tayi kana ta kalli Ayrah dake shirin fita daga d'akin saboda Raj daya shigo yanzun kuma ya fita "Ina kuma zaki je?" Umman ta fad'a, turo d'an k'aramin bakin ta tayi sannan tace "Umma Raj zan bi" "Ina ze je?" "Wajen Yah Sadeeq.." ta fad'a tana kallan Umman, Abba ne yanzu kuma yace "Toh shikenan, amma banda shiga ball ta maza ce" jinjina kae tayi tana murmurshi ta fice daga d'akin, Umma ta juyo da kanta wajen Abba tace "Abban su ina jin ka" seda Abban ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "Wato Alhaji Mato ne yazo min da wata shawara..toh yanzu dae so nake nayi shawarar dake inji me kikace, wato ba wani abu bane ya bani shawara ne wadda In Sha Allah akwae cigaba a cikin ta, cemin yayi meze hana tunda Allah yasa min albarka a wannan harkar na koma cikin kano ko da zama ko da sana'a, kin san kano cibiyar kasuwanci ce.." d'an shiru Umma tayi tana nazarin maganar Abban se kuma can tace "Hakan ma yayi Abban su, me son cigaban ka ae me k'aunar ka ne, ni ina ganin kawae ka amince da shawarar tasa.." "Toh shikenan amma batun zama fa? Acan d'in zamu zauna ko kuma dae in fara maganar ni kad'ae na tafi can sena dinga zuwa?" Abba ya fad'a yana Kallan Umma, murmurshi Umma tayi kana tace "Abban su ni bana tunanin wannan mafita ce, ni a gani na gwara ka tsayar da hankalin ka kan abu guda d'aya, ba kae kana can mu muna nan ba hankalin ka ze rabu gida biyu, ni a gani na kawae muma mu tafi tare da kae.." "Shikenan toh Allah ya taemake mu" Abba ya fad'a yana murmurshi. Be hak'ura haka ba seda ya nemi Abbu yayi shawara dashi, cikin ikon Allah kuma shima ya bashi goyon baya d'ari bisa d'ari, dan haka Abba ya sake jin nutsuwa a lamarin, saboda haka babu 6ata lokaci ya fara shirye shiryen tafiya kanon, ita kanta Umma ma ba'a barta a baya ba, shiri take yi na tafiyar ta su, dan haka babu 6ata lokaci Abban ya kusa gama komae, da yake Alhaji Mato yafi zama a kano ya saka shi ya nemar masa gida a cikin garin na Kano d'an madaedaeci haka me kyau, beyi k'asa a gwuiwa ba wajen tambayar Abbu yadda za'ayi, ze bishi can garin kanon ne ko kuwa anan ze zauna se Abban ya dinga yi masa aeke, girgiza kae yayi a lokacin da Abban ke masa maganar yace "Ayyah Abban Sadeeq, ya za'ayi in zauna anan kae kana can wani gari? In Sha Allah zan bika can d'in idan yaso sena dinga dawowa nan d'in wajen iyali na" Take Abba yayi na'am da maganar Abbun, dan haka yace "Toh shikenan, Allah ya taemake mu" "Ameen Ameen" Abbu ya fad'a.. Rana ku suka cigaba da tafiya babu tsayawa, har zuwa sanda Abba ya k'arasa abinda be gama ba, yanzu haka ya siyar da kayayyakin da yake siyarwa anan d'in ya had'e kud'ad'en nasa waje guda, be sanya su a banki ba saboda matsalar da account d'in sa ya samu, hakan ne yasa ya had'a su cikin wata jaka daban wadda yake ajje muhimman takardun sa masu matuk'ar amfani, duk wani abu da yasan yana da amfani a wajen sa ya had'e su duka cikin wannan jakar sannan ya had'a ragowar kayan sa cikin wata, haka zalika Umma ma tayi sallama da mak'ota en uwa da abokan arzik'i, ranar da zasu koma zuwa garin kano tazo... Tun safe Umma ta gama shiryawa tsaff cikin atamfa riga da zani da hijab dogo, ta shirya Ayrah cikin doguwar rigar en kanti da baby hijab suka fito parlour, tun d'azu Ayrahn ke ta 6ata rae da alama k'iris take jira ta fashe da kuka dan haka Umman na kallan ta tak'i kula ta ballantana ma ta sakar mata kukan shagwa6ar ta ta, tana zaune kan kujerar ta kwantar da kanta akan wata leda dake d'auke da kaya, Yah Sadeeq ne ya shigo cikin d'akin idanun sa akan ta ya fara sauka, shima yana ganin ta yasan yau da rigima ta tashi "Auta meya faru?" ya fad'a yana kallan ta, manyan idanun ta ta d'aga ta kalle shi amma ba tace komae ba, Umma dake kallan su tace k'asa k'asa "Ka rabu da ita don Allah, kar kasa ta mana kuka kuma" yaji abinda Umman ta fad'a dan haka kawae seya koma kusa da Ayrahn ya zauna, seta maeda kanta ta kwantar akan cinyar sa tana cigaba da kallan k'ofa.. Basufi mintuna 2 da zama ba sega sallama daga k'ofar d'akin, Umma da Yah Sadeeq suka amsa sallamar, yana sanye cikin riga da wando na wani yadi me kyau kasancewar sa me tsafta ya sanya kayan nasa a goge suke tsaff tsaff yayi matuk'ar kyau, da gudu ta mik'e ta k'arasa bakin k'ofar da suke k'ok'arin shigowa ta rungume shi tana sakin dariya kamar ba itace yanzu zaune kamar zata yi kuka ba, shima dariyar yayi yana fad'in "Oyoyo Ayrah" ta sake yin dariya kana tace "Ina ta jiran ka, shine ba kazo ba" dukka en d'akin binsu suke da kallo, ya rik'o mata hannu zuwa cikin d'akin yace "Gani fa nazo" "Zo kaji" ta fad'a tana janyo shi k'asa, seya d'an yo k'asan, ta sake jan shi ya tsuguna a k'asan sannan ta kae bakin ta kunnen sa tace k'asa k'asa "Jiya wata tace suna da mangoro a gidan su, zaka ciro min?" bud'e idanu yayi yana sake kallan en d'akin sannan ya mik'e ya sake kama hannun ta zuwa cikin d'akin, ita kuma ta tura d'an k'aramin bakin ta gaba, seda suka k'arasa ya zauna sannan ya gaeda Umma da suke gaesawa da Ummee sannan ya kalli Ayrah dake zaune dab dashi ta rik'o hannun sa kamar wanda ze gudu yace "Toh zan raka ki yi murmurshi" se a lokacin ta saki fuskar ta tana jin dad'i har cikin ranta. Basu dad'e da zama ba Yah Sadeeq daya fita d'azun yazo yace Umma su fito, har lokacin hannun ta na cikin na Raj sanda suka fito d'in, Ummee ta kalli Abba tace "Toh Alhaji mun gode Allah ya saka da alkhaeri, ya tsare ya bada sa'a" "Ameen Ameen" Abba ya fad'a yana shirin d'aukar jakar da Yah Sadeeq ya fito da ita a hannun sa, Abbu yayi murmurshi yana kallan Abba yace "Haba haba Alhaji ina wajen sannan zaka d'auki kaya?" shima Abban murmurshi yayi sannan yace "A'ah toh ka bar Sadeeq ya d'auka.." "Babu komae muje kawae" ya fad'a yana rik'e wata akwati kuma a hannun sa, Abba be sake cewa komae ba se kallan Ayrah da yayi wadda ta kwantar da kanta a hannun Raj yace "Toh taho koh?" mak'ale kafad'a tayi tana sake cuno baki gami da sake rik'e hannun Raj, Abba ya sauke ajiyar zuciya sannan yace cikin rarrashi bayan ya matsa dab da ita ya kamo d'ayan hannun ta "Ki taho mu tafi kinji, zamu dawo ae" "A'ah" ta sake fad'a tana kuma mak'ale kafad'a, Umma dake gefe ta d'an lumshe idanun ta kad'an ta bud'e kana ta matsa kusa da Ayrahn tace "Taho kinji, ae zaki dinga zuwa Uhmm?" girgiza kae ta shiga yi sosae k'wallar data dad'e a idanun ta ta shiga sakkowa babu k'ak'k'autawa, shi kam Raj gaba d'aya ma ya kasa kallan ta dan zuciyar sa ta riga ta dad'e da gama karyewa, Yah Sadeeq ne