← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 90

Sashe 50

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da yau d'in ze sanar da Abbu yasan komae game da zancen su shi da Abba, da irin abinda ya aekata masa, daze iya daya tsaya gaban Abbun ya fad'a masa abubuwan dake ta yawo a cikin kan sa, se dae baze iya ba, har lokacin Abbun na matsayin uban sa ne shiyasa yake neman hanya mafi sauk'i daze isar da sak'on sa wajen Abbun, koda hakan ze saka Abbun yayi nadama ya nemi yafiyar Abba akan abinda yayi masa shi da iyalin sa, ya tarwatsa musu farin ciki da rayuwar jin dad'i zuwa ta k'unci, baya so ya bar Abbun se ranar al_k'iyama sa had'e da Abba, sam baya fata hakan ya kasance. Mik'ewa yayi a hankali dae_dae lokacin da yake lumshe idanun sa lokaci d'aya ya fesar da huci daga bakin sa, be san me ze cewa Abbun ba koya shiga cikin d'akin, be san da wane baki ze yiwa Abbun magana ba, dan ze ga kamar idan yayi maganar zata zama kamar magana ce a fakaece yake fad'awa Abbun, hakan ne ya sanya shi jan k'afafun sa ya bar d'akin.. .... Da mamaki Abba ke kallan Alhaji Mato dake tsaye k'ofar gidan nasa jikin wata hamshak'iyar mota er uban su, lokaci d'aya annurin fuskar sa ya gushe, kamar ya juya ya koma se kuma ya kalle shi yace a nutse "Me ya kawo ka k'ofar gida na?" wani murmushin gefen baki Alhaji Mato ya saki kana ya sanya hannu ya gyara zaman babbar rigar jikin sa, hannu ya mik'awa Abba bayan ya matsa kusa dashi sosae yace "Ae ka bari mu gaesa koh?" ya fad'a da murmushin da Abba ya kasa gane manufar yin sa "Kaaga zaka fad'i abinda ya kawo ka ko kuma nayi tafiya ta?" "A'ah ae bata kae ga nan ba Alhaji Kabeeru.." ya k'are maganar yana sakin wata dariya kafin ya d'ora da "Wannan zuwan ae ba nawa bane naka ne" ya k'arasa maganar yana nuna Abban, da mamaki Abba ya cigaba da kallan sa dan yau d'in gaba d'aya Alhaji Maton ya chanja kamar bashi ba yana wasu abubuwa a juye wad'anda ya kasa gane su, jin Abban bece komae ba ya sanya shi fad'in "Zuwa nayi a bani kud'in da nayi asara akan d'iyar ka, dubban kud'ad'en dana kashe akan karatun ta, dubban kud'ad'en dana kashe dan naga ta zama wata amma saboda bak'in ciki irin naka wanda har d'iyar ka ma bakya k'yale ba ka saka k'afa kayi fatali dani d'in dae dazan rufa muku asiri.. Saboda haka yanzu base gobe ba ka shiga gida ka fito min da kud'i na gaba d'aya kada ko naira 5 tayi ciwo, dan kuwa babu inda zan je se kud'i na sun fito.." Alhaji Mato ya fad'a yana cigaba da kallan yanayin Abban daya chanja lokaci guda.. Mhiz Innocent.... https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* Page 041 ___Sosae Abba ke kallan Alhaji Mato tunda ya fara maganar har ya kae k'arshe, kawae ji yake kamar yana wani yaren da baya fahimta, meye had'in sa da Ayrah? Meye had'in kud'in sa da rayuwar Ayrah? Gyara tsayuwa Alhaji Mato yayi saboda yanda yaga Abban na masa wani kallo da yafi kama da kallan tuhuma, yayi wani murmurshi a ran sa yana sak'a yanda ze wulak'anta Abban a k'ofar gidan sa inda ake ganin mutuncin sa "Kada ka nuna kamar baka wani sani ba mana, kae ne ka biya wa d'iyar ka kud'in S.S 2 and S.S 3 exam? Kae ne ka saka er ka a University ko kuwa duk baka san yanda akayi take zuwa ba?" ya k'are maganar yana sakin wani shu'umin murmushi, d'an runtse idanun sa Abba yayi dan zuwa lokacin kan sa ya gama kullewa, da k'yar yayi k'arfin halin fad'in "Mato.. Ka tattara ka bar min k'ofar gida, ka dena wannan shaci fad'in idan kuma ka zo ne ka dinga wasu zance marasa kan gado zan bar maka k'ofar gidan kayi sunbatun ka kae d'aya.." dariya Alhaji Mato ya shek'e da ita wadda ba dan Abban na buk'atar k'arin bayani akan maganar Alhaji Maton ba babu abinda ze hana shi jan k'afafun sa ya bar masa wajen "Haba haba Malam Khaleel, ae wannan za6in ni ke gare shi ba kae ba, za6in gare ni yake.. Ko dae in tafi ko in zauna.." ya d'an numfasa kad'an sannan yace "Duk wasu kud'ad'e da aka kashewa er ka akan makarantar ta tun kafin ta gama secondary school ni ne na kashe su ba kowa ba, ba makarantar su ba ko wani, ni ne dae ni d'in nan, kuma nayi hakan ne dama saboda in gina ta ta ginu ni kuma na aure ta, amma tunda naga kae baka da niyyar aura min ita yasa naga gwara ayi ta ta k'are dan haka ka shiga cikin gidan nan duk inda kud'i suke ka tattaro ka kawo min, idan kuma babu ka fito in saka ka a mota kaje ka nemo.." tunda ya fara maganar Abba ke kallan sa cike da mamaki gami da tsoron da yaji ya masa dirar mikiya, lokaci d'aya kuma wani irin takaeci na mamaye shi, yana jin wani zafi a cikin zuciyar sa, me Maton ke k'ok'arin fad'a? Kada dae makarantar su Ayrahn sun yi amfani da kasancewar su malamae sun yaudari Abban, kada dae ace duk nauyin abubuwan Ayrah da ake d'auka Alhaji Mato ne ke d'auka? Idan kuwa hakane lallae Maton ya shammace su, malaman makarantar tasu kuma sun yaudare shi sun zubar da duk wani girman su da yake gani, meyasa suka yi hakan? "Kayi shiru?" Alhaji Mato ya katsewa Abba dogon tunanin daya fad'a, se a lokacin ya sauke ajiyar zuciya cikin zuciyar sa yana lalubo kalaman daya kamata yayi amfani dasu. Dae_dae lokacin da motar sa tayi parking gefen motar Alhaji Mato, tun daga nesa idanun sa ke masa gizo, kamar ya san fuskar, kamar yaso ya gane fuskar, be tabbatar da hakan ba seda ya tsayar da motar sa sanda idanun sa suka sake sauka akan Alhaji Maton, seda ya runtse idanun sa ya bud'e dan sake tabbatar da abinda yake gani d'in, se dae har ya sake bud'e idanun nasa Alhaji Maton ya gani "Menene ya kawo shi nan?" tambayar data fara zuwar masa cikin kwanya kenan, be ta6a tunanin Alhaji Maton ze samu k'arfin halin zuwa wajen Abba ba bayan sace ta da yayi da kuma k'ok'arin auren ta, baya tunanin ta 6are da shi har hakan ya janyo masa matsala? Be k'ara ko minti 1 ba cikin motar ya sanya hannun sa ya bud'e k'ofar ya fita, sannan ya soma takawa zuwa wajen a nutse hannun sa rik'e da key d'in motar sa har kuma lokacin idanun sa na kan Alhaji Mato kamar wanda ze gano dalilin zuwan sa ta cikin idanun sa "Tunanin me kake yi ne? Ko sena aekata abinda nake danne zuciya akan kada na aekata?" Alhaji Mato ya fad'a ba tare da ya ga Rk da ke dab da k'arasowa inda suke tsaye ba "Assalamu Alaekum.." Rk ya fad'a yana bin Alhaji Mato da wani irin kallo wanda ni kae na na kasa fassara a wani waje zan ajiye shi, kusan a tare dukan su suka d'aga ido suka kalli Rk, dae_dae lokacin daya d'aga idanun sa ya maeda su kan Abba sannan cikin lokaci k'ank'ani ya zube akan k'afafun sa "Barka da wannan lokaci Abba" ya fad'a cikin girmamawa, cike da k'arfin hali Abban ya furta "Barka dae.." daga haka be sake cewa komae ba, hakan ne ya sanya shima ya tashi tsaye ya maeda duban sa kan Alhaji Mato dae_dae lokacin da Abba ke fad'in "Je ka ciki ka jira ni gani nan zuwa" ya fad'a yana kallan Rk. Tunda Alhaji Mato yaga Rk jikin sa yayi wani mugun sanyin da baze misaltu ba, hatta jikin sa seda ya d'an soma rawa kad'an kafin yayi ta maza ya maaze ya cigaba da tsayuwa kamar babu abinda ke faruwa "Toh Abba.." shine abinda Rk ya fad'a kafin ya d'ora da fad'in bayan ya maeda kallan sa kan Alhaji Mato "Me kake yi a k'ofar gidan nan?" shiru yayi kamar baze tanka ba, se kuma ya sake d'akko jarumta yace bayan ya gyara tsayuwa gami da sauke ajiyar zuciya "Ba hurumin ka bane wannan d'in, saboda haka ka bar mu mu k'arasa maganar mu" yayi k'arfin halin fad'a, shiru Rk yayi yana nazarin Alhaji Mato, kafin ya maeda duban sa kan Abba yace a hankali "Abba don Allah idan maganar ta shafi Ayrah zan so na sani ba dan na isa ba" yadda yayi maganar ya sanya Abba yin shiru na en wasu sakanni yayin da Alhaji Mato mamaki ya gama kama shi, da alama Abban na shiri da Rk d'in kenan duk da yadda yaso bayan auren Ayrahn idan sun dawo gida yayi bak'in jini a wajen Abban, Abban ya dinga tunanin shine ya ja masa 'ya suka gudu aka d'aura musu aure, se dae daga yanda yake gani yanzu hakan ya tabbatar masa akasin hakan ne ya faru. Kamar yadda Alhaji Mato ya fad'a haka Abba ya kora masa bayani sannan ya k'are da fad'in "Amma kada ka damu, zan je na samu malaman inji dalilin su na yin k'arya akan wannan al'amarin, sam ban ji dad'in abinda ya faru ba" Abba ya k'are maganar a hankali cike da takaeci da rashin jin dad'i wanda hakan be hana bayyana har a cikin muryar sa ba. D'aga idanun sa da suka chanja kala saboda 6acin rae yayi ya kalli Alhaji Mato dake tsaye kamar an dasa shi, wanda tun ganin Rk da yayi jikin sa ya gama yin la'asar, d'auke kae Alhaji Mato yayi yana d'an cic cin magani "Abba don Allah ka bar ni zamu yi magana da shi" Rk ya fad'a kan sa a k'asa "A'ah ka bar ni dashi Suraj, kada ka saka kan ka cikin lamarin nan" girgiza kae yayi a ran sa yana fatan Abban ya kar6i tayin nasa "Ba dan ni ba Abba pls" "Ohk.." Abba ya fad'a bayan ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ja gefe ya tsaya, seda ya lumshe idanun sa sannan ya fara magana a hankali still dae yana kallan Alhaji Maton da duk yadda yawan shekarun sa suke be ji ko shakkar fad'a masa
Chapter 50 · 0% Book details