Sashe 66
Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ka" a hankali ya sauke wani numfashi gami da lumshe idanun sa, tausayi ko kuma me ya kamata ya ji akan mahaefin nasa da koda daga cikin maganar sa zaka fahimci yadda jikin sa yake a sanyaye? "Suna waje na!" yayi maganar a nutse, gwauruwar ajiyar zuciya Abbu ya saki gami da runtse idanun sa ya d'an yi jimm sannan ya bud'e "Jira ni a waje, yanzu zan fito" Abbu ya fad'a, tashi Rk yayi a hankali ya fice daga cikin d'akin shima kan sa jikin na sa a matuk'ar sanyaye. Se da ya fita sannan Ummee ta maeda duban ta kan Abbu cike da son jin k'arin bayani, fahimtar hakan ya sanya Abbu fad'in "Ki shirya zamu je wajen Abban Sadeeq gobe.." da sauri ta sake kallan sa cike da mamakin sa, kenan cikin lokaci k'ank'ani har ya chanja haka? "Abban Sadeeq kuma?" ta tambaya tana kallan sa, jinjina kae Abbu yayi kamin ya soma fad'in "K'warae Abban Sadeeq, shin kin kuwa san jiya ko da da sau d'aya ban iya rintsawa ba? Na k'agu gari ya waye dan inji tabbacin abinda nake zargi daga wajen Raj, yau d'in kuma dana tabbatar gaba d'aya hankali na ya tafi wajen Abban Sadeeq, bana tunanin zan sake amfani da kud'in da muke tunk'aho da nawa ne ba tare da naje neman yafiyar sa ba, Fatima ko kin manta ta yadda muka samu dukiyar nan ne? Ko kin manta silar taruwar dukiyar mu? Ko kin manta rabuwar mu da Abban Sadeeq? Idan ke kin man ta ni ban manta ba. Ko kuma kin manta da yadda muka hana yaron nan auren Ayrah a bisa wasu hujjoji namu na banza, amma daga k'arshe kin ga yadda akayi auren koh? Ba tare da izinin mu ba acan wani waje, inda Allah ma ya taemake mu da ya bar mu a raye har wannan lokacin, da yaso seya d'auke mu mu dukan mu sannan azo har cikin gidan nan a d'aura auren, amma da yake Allah na son mu se gashi ya bar mu a raye har zuwa kuma lokacin da nake fatan zamu je mu saka gwuiwoyin mu a k'asa wajen neman yafiyar Abban Sadeeq akan cutar da muka masa" Abbu ya k'are zuciyar sa na masa wani irin zafi, shiru Ummee tayi na tsawon lokaci sannan ta lumshe idanun ta cikin rashin sanin abin yi, tabbas maganganun Abbun sun ratsa ta aenun, sun kuma tunatar da ita abinda ta manta, sun kuma yi mata tuni akan abinda suka aekatawa Abban Sadeeq, se dae har zuwa lokacin ta kasa mantawa da abinda ya dad'e yana ci mata tuwo a k'warya hakan yasa tace cike da k'arfin hali bayan tayi kokawa da zuciyar ta. "Amma dae ka tuna abinda na fad'awa yaron nan lokacin da yazo da maganar auren Ayrah, yanzu kuma kana k'ok'arin tona mana asiri, kana nufin gwara mutuncin mu ya zube a idon d'an mu da kuma idanun iyalan Abban Sadeeq, mu ji kunya a idon duniya da ka bar maganar nan a rufe?" Ummee ta k'arasa maganar tana kallan Abbu, murmushin yak'e Abbu ya saki wanda ake cewa yafi kuka ciwo kafin yace "Toh da ki ji kunyar duniya da kuma ki ji ta lahira wanne kika za6a?" Abbu ya fad'a jikin sa a matuk'ar sanyaye.. Mhiz Innocent... https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* Page 050 ___Shiru ne ya wanzu cikin d'akin na tsawon mintuna. Ummee tayi shiru yayin da Abbu ke kallan ta yana jiran jin abinda ze fito daga bakin ta, zuwa can ta d'ago ta kalle shi sannan tace a hankali "Shikenan.." daga haka ta mik'e ta fice daga d'akin tana runtse idanun ta, zuciyar ta fall cike da tunani kala_kala, ita babban abun da yafi damun ta shine yanda zasu kalli Rk su fad'a masa maganar da suka fad'a masa tun farko k'arya suka yi, wannan d'in yafi komae ci mata tuwo a k'warya. Sanda ta fito daga cikin d'akin har lokacin yana tsaye a gefe guda hannayen sa duka biyun sak'ale a k'irjin sa, gaba d'aya hankalin sa na kan Ayrah ne se dae kuma Abbu yake jira yaji abinda ze fad'a masa. Dae_dae lokacin Ummee ta fito daga cikin d'akin, tana shirin wuce shi yace "Ummee zan wuce idan mun gama magana da Abbu.." dakatawa tayi daga inda take ta kalle shi kana tace "Ka gaeda gida.." daga haka ta wuce. Bin ta yayi da kallo haka kawae ya sake jin jikin sa yayi sanyi, tausayin Ummee da Abbun na ratsa shi, ko ba'a fad'a masa ba yaga alamar nadama da kuma kunyar abinda suka aekata daga yanayin su, musamman ma Abbu. Babu dad'ewa bayan wucewar Ummee zuwa d'akin ta se ga Abbu ya fito daga cikin parlourn sa, ya k'araso inda Rk d'in ke tsaye, gyara tsayuwar sa yayi yana kuma sauke hannayen sa dake sak'ale zuwa k'asa. "Kana ji na?" Abbu ya fad'a da muryar sa da har lokacin bata koma dae_dae ba. "Ehh Abbu.." ya fad'a cike da girmamawa. Se da Abbun ya d'an numfasa kafin yace "Ina matar ta ka?" da sauri ya d'aga ido ya kalli Abbu dan be tsammaci wannan tambayar ce zata fito daga bakin sa ba, se dae kuma abinda be gane ba, Muneerah yake nufi ko kuma Ayrah? Kamar Abbun ya fahimci be gane tambayar ta sa ba se cewa yayi "Ayrah!" sauke numfashi yayi yana d'an lumshe idanun sa kana ya bud'e su lokaci guda sannan yace a hankali kamar wanda baya so aji me yake fad'a. "Tana gida" yayi maganar yana d'an shafa kan sa da ko yaushe ke d'auke da kwantacciyar bak'ar suma, tuna a yadda ya batta daze fito. "Ka d'auko ta goben idan Allah ya kaemu zamu je gidan na su" shiru yayi na en wasu sakanni, Abbun da gasken yake kenan gidan su Ayrahn zasu je neman gafarar iyayen ta? Lallae komae yazo masa da sauk'i, ba tare da wata wahala ba gashi komae yana shirin gyaruwa da izinin Ubangiji. Se da murmushi ya d'an su6uce masa kafin yace "In Sha Allah Abbu.." "Allah ya yadda, se ka sanar da ita Muneerahn kada kawae taji mun fita unguwa babu ita, ko kuma muje tare da ita?" da sauri ya girgiza kae kafin ya bud'e baki yace "A'ah Abbu ba se taje ba, wannan d'in kamar personal issue ne so ina ganin base ta ji ba" jinjina kae Abbu yayi cike da gamsuwa da maganar Rk d'in kaf in yace "Hakane, zaka iya tafiya.. Allah yayi albarka" "Ameen Abbu" Rk ya fad'a kan sa a k'asa kafin ya wuce zuwa wajen motar sa. .. Se da ya fara tsayawa a Restaurant ya siya abinci sannan ya wuce gidan. Kae tsaye part d'in Muneerah ya wuce da sallama d'auke a bakin sa cikin muryar sa me dad'in saurara. Tana zaune akan carpet d'in d'akin kamar me tunani, tun d'azu ta rasa abinda zata yi tunda taje part d'in sa ta gama buge_bugen da zata yi ta kasa bud'e k'ofar shine ta dawo nan d'in ta zauna jikin ta a sanyaye cike kuma da takaeci. Maemaeta sallamar yayi amma duk da ta ji shi bata amsa ba se kallan sa kawae da tayi, wani abu ya tsirga mata a jikin ta amma ta basar dan so take ta nuna masa taji haushi. Be sake bi ta kan ta ba kawae ya nemi waje ya zauna gami da ajje leda d'aya daga cikin wad'anda ya shigo da su a gefen ta, fuskar sa babu yabo babu fallasa, se dae can k'asan ran sa tafasa yake, dan tabbas Muneerahn na dab da kae shi bango, tana dab da k'ure shi, wanda idan hakan ta faru be kuma san meze biyo baya ba, amma dae tabbas ya san abinda ze biyo bayan ba me dad'i bane. Bayan wajen minti 5 babu wanda yace komae a cikin su, shi dama ba damuwa yayi da tace uffan ba se dae kawae ya k'agu lokacin da ya bata ya cika ya mik'e ya bar mata d'akin yayi, ganin da yayi lokacin na dab da cika ne ya sanya shi fad'i a dak'ile "Ga abinci nan.." ya fad'a ba tare da ya kalle ta ba, dama k'iris take jira, dan kuwa ta d'auka a yadda ya ganta d'in nan ze sakko ne ya lallashe ta se dae ba taga alamun hakan ba dan haka tace a fusace "Wane abinci zan ci a gidan nan, bayan ana nuna min rashin adalci, an tauye min hak'k'i na" cike da gajiya da kuma ginsar da wad'annan maganganu nata suka masa ya d'ora hannun sa akan goshin sa ya d'an murza kad'an idanun sa a lumshe kafin ya bud'e yace "Muneerah, na gargad'e ki akan bakin ki ya kiyayi abinda ze dinga furtawa, ni ne na tauye miki hak'k'in ki ko kuwa?" ya fad'a yana kallan ta, se ta d'auke kae kawae saboda yadda maganar ta sa ta d'an dake ta se duk ta rasa kuzarin maeda masa da martani. Ko minti d'aya be k'ara ba ya mik'e ya fice daga d'akin ba tare da ya sake bi ta kan ta ba, bin sa tayi da kallo har ya fice daga d'akin kafin ta dawo da duban ta kan wayar ta dake ringing, haushi, takaeci suka had'u suka mata dirar mikiya, ga haushin Ayrah da take ji, ga haushin shi kan sa Rk d'in, ga kuma haushin kiran dake shigowa wayar ta ta daga Aunty Zeenah, janyo wayar tayi kamar Aunty Zeenahn na gaban ta ta katse wayar tana jan wani dogon tsaki kafin a fili ta furta "Aekin banza kawae" Wani kiran ne ya sake shigowa, ta saka hannu da niyyar katsewa se kuma ta ga Mummyn ta ce ke kira, da sauri ta d'aga har hannun ta na rawa ta kara a kunne, kafin tace komae ko Mummyn tace wani abu ta fashe da kuka, mik'ewa Mummy tayi daga inda take zaune tana fad'in "Ke lafiya kuwa? Meye kike kuka haka? Waye ya mutu?" cigaba da kukan tayi Mummyn na cigaba da tambayar ta, amma ba tace komae ba seda ta gaji dan kan ta sannan tayi shiru kana ta soma fad'i tana sheshshek'a "Mummy Yaya ne fa yayi aure" "Aure kuma?" Mummy ta fad'a cikin rashin fahimta, kamar Mummyn na