← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 90

Sashe 21

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gama maganar aka shiga kiran sallah a masallaci, dan haka dukan su suka yi shiru har zuwa sanda aka idar da kiran Sallahr sannan suka mik'e kusan a tare, Rk ya kalle ta sannan ya mik'a mata wayar sa daya fito da ita daga cikin aljihu yace "Samun contact naki" babu musu ta kar6i tsaleliyar tsadaddiyar wayar tasa ta sanya number ta a ciki sannan ta mik'a masa a ranta tana jin farin ciki mara misaltuwa, daga yanayin yadda ta fahimta abubuwa da dama sun chanjawa Raj d'in nata, kamar bashi ne Raj d'in da ba, kamar an chanja shi ne da wani sabo, ko da yake ba abin mamaki bane komae ikon Allah ne, da farko sune a sama yanzu kuma Raj d'in se dae ma shi ya taemaki wasu ba dae a taemaka masa ba, babu abinda Allah baya iya yi, yadda tayi shiru kamar me tunani ya bashi damar cigaba da k'arewa kyakykyawar fuskar ta kallo yana cigaba da karanto abubuwa da dama "Muje koh?" yayi maganar a hankali kamar me rad'a, seta d'aga kae ta kalle shi kana ta lumshe idanun ta a lokaci guda tana bud'e su, itace ta fara yin gaba sannan yabi bayan ta har suka fito, me Cafe d'in nan ya mik'e yana kallan sa yace "Doctor zaka wuce ne?" "Yeah" ya fad'a a gajarce "Tohm shikenan, Allah ya tsare" ya fad'a yana d'an satar kallan Ayrah yana so yaga wace me sa'ar ce wannan da Doctor d'in da kan sa yake kula ta "Ameen" ya fad'a yana wucewa zuwa wajen motar sa Ayrah na binsa har zuwa sanda ya bud'e murfin gaba sannan ya juyo ya kalle ta, se yaga a yanzu da suka fito haske sosae ma kamar tafi kyau, d'an guntun murmushi ya wanzu a gefen bakin sa sannan yace "I will call u Uhmm?" ya k'arashe maganar yana rufe idanun sa kad'an sannan ya bud'e, jinjina kae tayi ba tare da tace komae ba, haka kawae take jin babu dad'i har cikin ran ta, ji take ina ma su kasance a haka har abada, gefe guda kuma tana ganin kamar idan ya tafi d'in za'a sake maemaeta wancan karon, wato baze sake dawowa ba se bayan wasu shekaru, ko kuma yana matsawa daga wajen zata farka ne daga bacci taga duk abinda ya faru d'in mafarki ne ba gaske ba, haka dae ta kawar da duk wad'annan kawae ta jinjina masa kae sanda yake shigewa cikin motar, ta cigaba da tsayuwa har zuwa sanda yaja motar ya bar wajen yana cigaba da kallan ta, itama shi d'in take kalla. A hankali ta sauke wata ajiyar zuciya sanda ya 6acewa ganin ta, seta shiga jan k'afar ta data mata wani nauyi ta shiga takawa tana cigaba da tunanin Raj d'in, tana tuna Raj d'in da daga farko take masa kallan mutum mara kirki, mugu kuma mara tausayi, mutumin da mazan ajin su kaff ba taga wanda baya tsoron sa ba ballantana kuma akae ga mata, matan dake rububin sa kamar me, se gashi a rana d'aya a kuma lokaci d'aya hakan ya juye zuwa wani sabon al'amari, daga yadda zuciyar ta ke cigaba da harbawa tana tunanin Rk d'in ta fahimci akwae wani gagarumin abu, se dae ta gaza gane menene shi?. Cikin farin cikin daya gaza 6oyuwa akan fuskar ta ta shiga d'akin nasu, dukkan su suka bita da kallo, sabon abu ne da ba kasafae suka saba ganin sa akan fuskar ta ba, abu ne ma da zasu iya cewa in dae ba da Yah Sadeeq, Umman ta ko Abban ta take waya ba basa ganin irin wannan annurin akan fuskar ta, se dae na yau ma ya shallake wad'ancan d'in, dan kuwa tana shigowa ta jefar da Handout d'in hannun ta sannan ta kwanta akan gado tana sakin wani k'awataccen murmushi gami da lumshe idanu, da mamaki Jidda da Ruks suka kalli junan su, se kuma cikin k'arfin hali Ruks ta furta "Ayrah lafiya kuwa?" da sauri ta bud'e idanun ta dan gaba d'aya ma ta manta ba ita kad'ae ce cikin d'akin ba "Eh. Ehh" ta fad'a tana mik'ewa zuwa toilet, suka sake bin ta da kallo sanda ta shige toilet d'in "Ikon Allah" suka had'a baki wajen fad'ar hakan, babu dad'ewa ta fito, Jidda ta dube ta tace "Ga mangoron ki nan cikin leda" "Bash shi kawae, zuwa da safe zan sha" tayi maganar tana janyo hijab dan gabatar da Sallah "Toh lallae akwae damuwa" Jidda ta fad'a tana bin ta da kallo sanda take k'ok'arin tada Sallahr.. Wajen k'arfe 9pm ne na daren ranar tana kwance kan gadon ta, tun d'azu take expecting kiran sa amma kuma tana fatan kafin ya kira ace su Jidda sunyi bacci, se dae ba taga alama ba dan kuwa hirar su suke kamar yadda suka saba kullum se sunyi ta kamar farilla, se juyi take kawae akan gadon tana tuna kyakykyawar fuskar sa, ada sanda yake a Doctor Rk bata ta6a tsayawa ta k'are masa kallo ba ballantana har ta gano wannan kyan na musamman da matan ajin nasu kan kod'a shi akan sa ba, se yau ta kalle shi ta tabbatar da hakan, ta kuma ga zalla kuma aenahin kyau daga Raj d'in. .. Sanda ya koma gida kae tsaye d'akin sa ya wuce yau ko sashen Mummy be je ba, dan so yake kawae ya gama abinda yake ya kira ta yaji abubuwa da dama daga wajen ta, toilet ya fad'a ya watsa ruwa a jikin sa sannan ya fito ya shirya cikin wata brown d'in had'ad'd'iyar jallabiyya, ya zauna yayi karatun qur'an kamar yadda ya saba sannan yayi addu'o'i ya mik'e daga kan abin sallah, yana shirin ninkewa yaji ana knocking k'afar d'akin, d'an tsaki yaja sam be san wani ya kula da shigowar sa cikin gidan ba, kamar ba zeje ya bud'e ba se kuma ya ajje daddumar kan gado sannan ya fito parlourn ya k'arasa ya bud'e k'ofar, kawae seta sanya kae cikin d'akin ta shigo hannun ta d'auke da warmers d'in abinci guda 2 ta ajje a tsakiyar parlourn, sanye take cikin doguwar rigar shadda wadda tasha aeki ta fito tayi kyau da ita, fuskar nan kamar koda yaushe ta k'ara fari, tsaki ne ya su6uce masa akan bakin sa yana lumshe ido, ya akae tasan ya shigo gidan? "Baby yau baka shigo kaci abinci ba, yasa nace bari na kawo maka d'aki, ina fatan ban yi laefi ba?" tayi maganar tana matsowa kusa dashi, bece komae ba ya k'arasa ya zauna kan kujera sannan yace har lokacin be kalle ta ba "Sannun ki" seta saki murmushi tana dawowa itama ta zauna kan kujera tana shak'ar k'amshin turaren jikin sa daya cakud'e dana sassanyan k'amshin sabulun sa, ko second 5 ba tayi kan kujerar ba ta zame zuwa k'asa tana fad'in "Bari nayi serving naka" shi bema jita ba dan gaba d'aya hankalin sa ya tafi kan Ayrah ne, tunda ya baro makarantar ya kasa dena tuno kyakykyawar fuskar ta, gaba d'aya ta chanja, duk da dama tun tana yarinya kyakykyawa ce amma yanzu ta k'ara wani shahararren kyau kamar ita tayi kan ta, se dae har yanzu halin ta na nan, ga6untar nan da shagwa6ar nan har yanzu babu abinda ya ragu, tilas abinda ya tuna d'in ya sanya shi sakin sassanyan murmushi yana gyara zaman sa kan kujerar da yake, Muneerah data d'aga kae ta kalle shi taga murmushin da yayi, abinda yake da tsada a wajen sa, se gashi yau kusan zata iya cewa babu dalili yayi shi, seta samu kan ta da gyara zaman ta tana murmushi dan ita ta d'auka da ita yake "Yaya Daddy ya maka magana kuwa?" ta katse masa tunanin tana fatan Daddyn ya masa magana kuma ya kar6i zancen hannu bibbiyu, da mamaki ya d'an kalle ta sannan ya d'auke kae "Magana? Anya kuwa!" ya fad'a cikin er basarwa, seta yamutsa fuska sannan tace "Ohk toh ka sauko kaci abincin mana" ta fad'a tana cigaba da satar kallan sa ganin da tayi yanzu babu wannan murmushin akan fuskar ta sa, iska ya furzar daga bakin sa dan shi kam kwata kwata baya jin wata yunwa, toh wata ma yunwa zeji bayan gaba d'aya hankalin sa da tunanin sa na wajen Ayrah ne "Ban jin yunwa fa" ya fad'a yana zuba mata idanun sa, cikin er rawar murya ta furta "Haba mana Baby, pls kaci kada ka kwana da yunwa!" ta fad'a cike da kulawa kamar itace zata kwana da yunwar bashi ba, baya son dogon zance kuma ya k'agu ta fita dan yana jin idan har ta k'ara wasu mintuna bata fita ba toh ze tashi ne ya bar mata d'akin ita d'aya, dan haka ya furta "Ohk.. zaki iya tafiya, se da safe.." kallan sa ta cigaba dayi dan ita kam sam bata gajiya da kallan sa, jin shiru ya sanya shi sake fad'in "Ko na bar miki d'akin ne?" yayi maganar in a serious tune, da sauri ta mik'e sannan tace "Ohk bye luv, kayi bacci lafiya.." ta fad'a tana cigaba da kallan sa, ba tare daya kalle ta ba ya furta "Ohk" ya k'arasa maganar yana janyo wayar sa dake gefen sa, babu yadda ta iya haka ta fice daga d'akin zuciyar ta a cunkushe, ita ta k'agu kawae ayi auren nan kowa ma ya huta. Number ta ta ya lalubo ya danna kira, a 6angaren ta tana kwance kan gadon ta hannun ta rik'e da wayar ta ta tana jiran kiran sa tun d'azun, ganin kira da wata sabuwar number ya sanya ta tashi zaune da sauri tana kallan jerin gwanon numbobin dake shimfid'e reras akan wayar ta ta, kamar yadda yake special haka number sa ma take special, haka kawae taji a jikin ta shi d'in ne dan haka ta sake kallan gadon su Jidda taga duk bacci suke sannan ta d'aga tana karawa a kunnen ta, kafin yace komae tace bayan ta tura bakin ta daga inda take "Se yanzu ma zaka kira?" murmushi yayi daga inda yake yana kishingid'a a inda yake kwance sannan yace "Am sorry.." "Naqi ni dae, Allah kuwa tun d'azu fa nake jira ka kira" wani murmushin ya sake yi mara sauti yana karanto zallahr k'uruciyar dake tattare cikin maganar ta,
Chapter 21 · 0% Book details