← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 90

Sashe 84

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* Page 059 ___Sun d'auki mintuna da yawa babu wanda yace komae tun bayan fitar su Abbu. Se can Abba ya kalli Umma yace "Bacci tayi ne?" yayi maganar yana kallan Umma dake gyarawa Ayrah kwanciya akan gadon. A hankali ta amsa da "Ehh" dan har lokacin jikin ta a sanyaye yake. Se da ta gama gyarawar sannan ta koma ta zauna kan kujera ta kalli Abba da dukkan alamu suka nuna magana yake so yayi. Se da shi ma ya nemi waje ya zauna kafin ya soma magana "Me kike ganin ya kamata ayi akan wannan lamarin?" D'an shiru Umma tayi na tsawon sakanni a ran ta tana tunani, yanzu kam ba zata iya cewa ga abin da ya kamata ayi ba, tana ganin gwara shi da kan sa ya fad'i abin da ya kamata ayi d'in. Kamar ya san me take tunani kuwa se cewa yayi "Ni ina ganin mu jira mu ga hukuncin da shi mijin na ta ze d'auka, idan kuma kina ganin akwae wata shawarar da kike ganin zata dace toh ki fad'e ta. Se dae kuma idan har ita Ayrah tana ganin zata iya toh ta bar yarinyar da Allah In Sha Allah ze yi mata sakayya, duk da abin da tayi yayi muni da yawa amma kwana kad'an ne zata manta tunda dae Allah ya kiyaye ya tsare. Amma abu na k'arshe ko da sun cigaba da zama gida d'aya se dae ayi musu iyaka, idan kuma ta sake yunk'urin aekata abin da tayi yanzun toh In Sha Allah hukuma ce zata raba mu da ita." Shirun dae Umma ta sake yi tana kallan Abba, ita kan ta wani lokacin idan Abba yayi abu har mamaki yake bata, kyakykyawar zuciyar sa kullum haka take. Se da ta d'an runtse idanun ta sannan tace "Shikenan Abban su, idan hakan yayi maka muma yayi mana, Allah ya saka mata, ita kuma ya shirya ta." Murmushi Abba yayi kafin yace "A'ah idan hakan be yi miki ba ki fad'a min." Itama Murmushin tayi karo na farko kenan tun bayan da taji cewar Muneerah ce ta jefa mata d'iyar ta cikin ruwa. "A'ah fa Abban su, duk abin da ka yanke ae mu masu biyayya ne akae. Ko kad'an kuma babu wani abu a rae na, Allah yasa hakane mafi alkhaeri." "Ameen_Ameen" Abba ya fad'a. *** *** *** .. A hankali ya tura k'ofar d'akin ya shiga, dukkan su suka d'aga kae suka kalle shi, fuskar sa sam babu alamar murmushi akae, ya k'araso yana kallan su, duk se suka sha jinin jikin su musamman ma Muneerah da tayi saurin d'auke kan ta saboda yadda taga Daddyn yau babu wasa. Bayan shud'ewar wasu sakanni Daddy yace "Kin ji dad'i, kin yi abin da ya kamata da taemakon zugar wasu shashashan da ke zuga ki." Had'e fuska Mummy tayi dan ta san har da ita yake nufi a cikin maganar da yayi, ta wani d'auke kae irin ko a jikin ta d'in nan. Shi kam be ma bi ta kan ta ba ya zura hannun sa cikin aljihu ya fiddo takardar da zuwan ta kenan hannun sa yace "Kin yi abin da kike so, kin biye wa shashashar k'wak'walwar ki, kin so aekata abin da inda kin yi shi ba zaki ta6a samun rahama ba, a banza kina shirin kae kan ki wuta saboda shirme irin na ki. Toh kada kiyi tunanin kin ci bulus dan kuwa shi ma mijin na ki yayi abin da ya dace, ga takaddar ki nan se ki jira hukuncin da iyayen yarinyar kuma suma zasu d'auka." Daga haka ya ajje takaddar ya fice daga d'akin yana jin wani irin d'aci har a cikin bakin sa. Tun lokacin da taji Daddy ya ambaci takadda ta wani irin juyo a razane, har ya k'are maganar bata sake fahimtar komae ba, gaba d'aya idanun ta ta zube su akan takaddar da ya ajiye kamar zasu fad'o. Se ta tashi ta soma takawa zuwa inda takaddar take kamar wata sabon kamu, ta sanya hannun ta dake rawa ta d'auki takaddar da saboda yadda hannun ta ke rawa ta kasa tsayawa a hannun ta. Cikin k'arfin hali ta shiga zagaye takaddar da idanun ta, Mummy dake bayan ta itama cikin tashin hankalin ta soma karantawa. K'ara Muneerah ta saki tana yin jifa da takaddar ta zube a wajen ta soma ihu kamar wadda aka yiwa rasuwa, juyi ta soma yi a dandagaryar k'asan d'akin hannun ta a kan ta tana cigaba da ihun da duk wanda ke cikin gidan se ya ji shi. "Wayyo na shiga 3 Mummy, ya sake ni ba tare da na cika buri na a kan sa ba, na shiga 3 Mummy, yarinyar nan bata bar shi haka ba wallahi, asiri ta masa Mummy, Mummy ya sake ni fa saboda tsinanniyar yarinyar nan." ta dakata anan tana sake sakin wata k'arar, Mummy tayi saurin k'arasawa ta rik'o ta amma ina fizgewa take yi tana cigaba da kukan tana kuma tsinewa Ayrah. Se da k'yar sannan Mummyn ta iya rik'o ta cikin jikin ta tace "Dallah can kiyi shiru shashashar yarinya kawae." Duk da abin da Mummyn ta fad'a be hana ta sake fad'in "Wallahi Mummy se naga bayan ta, idan ba haka ba hankali na baze ta6a kwanciya ba, Mummy saki na fa yayi a kan ta kuma kike cewa nayi shiru, toh inyi shiru kice min me? Ki k'yale ni Mummy in yi kukan takaeci da bak'in ciki, in yi kuka ko zan samowa kae na mafita akan waccan tsinanniyar, Mummy ki k'yale ni." Iska Mummy ta furzar jin yadda Muneerahn ke cigaba da sumbatu kamar sabuwar mahaukaciya. Hakan ne yasa ta daka mata tsawar da ta sanya ta yin shiru tana sheshshek'a. "Ki min shiru ko kina son kashe kan ki ne, saki 1 fa yayi miki, kiyi shiru mana ki bari a samo mafitar da kafin komawar ki ita ta bar miki gidan. Ke baki san anyi hakan ba ne dan a k'unta ta miki ba? Amma saboda ke shashasha ce kike neman tonawa kan ki asiri, ba kya tsoron Daddyn ki yaji wad'annan alwashin da kike ta d'auka? Idan yaji ae shikenan komae ya tarwatse. Memakon kiyi shiru a nutse kuma a hankali mu yak'e su, yarinyar ta fita daga gidan Raj kafin ke ki koma, waye ze kawo kece kika aekata hakan? Idan kin kwantar da hankalin ki zaman watanni ne, a cikin su kuma zata fice daga gidan, daga baya ke kuma salin alin se ki koma gidan ki hankali kwance abin ki." Maganganun Mummyn sun shiga Muneerah sosae sun kuma sanya ta yin murmushin da bata shirya ba, se ta soma share hawayen ta kafin tace "Mummy ina k'aunar ki, wallahi kina da basira." Murmushi Mummy tayi kana tace "Ae ke shashasha ce Muneerah wani lokacin, da kin d'auko k'wak'walwa ta da ba haka ba." Juyawa Daddy yayi daga niyyar shiga d'akin da yayi tun lokacin da ya jiyo ihun Muneerah na fitar hankali, se kuma kunnuwan sa suka had'u da wad'annan maganganun. Sosae jikin sa yayi sanyi da lamarin Muneerahn da kuma mahaefiyar ta, kwata kwata kamar basa tunanin zasu mutu? Su dae burin su kawae suyi abin da zasu ji dad'i a duniya? Dama shi ya san in dae har Muneerahn ta d'auki halin mahaefiyar ta ba zata iya zaman aure ba amma ze nuna musu shi ba mutumin banza bane, se ya koyawa Muneerah hankali tunda yaga har yanzun bata da shi. .. Ayrah bata k'ara kwanaki da yawa ba aka sallame ta daga asibiti suka koma gida. Daga wannan lokacin se ya duk'ufa wajen had'a mata lefen da beyi mata ba a baya, a gefe guda kuma ya laluba sanda za'a yi jamb, dan so yake yi ta sake wata saboda ta chanja makaranta dan kuwa tun tuni ya soke zuwa A.B.U duk saboda Alhaji Mato, bayan nan ma baze iya barin ta tana makaranta a wani garin ba shi kuma yana aeki a wani garin ba. _BAYAN WASU KWANAKI_ .. A zaune take akan carpet sanye cikin k'ananan kaya riga da wando wad'anda suka matuk'ar yi mata kyau, kan ta babu d'an kwali se bak'ar kwantacciyar sumar kan ta dake d'aure a tsakiyar kan ta, plate d'in fruit ne a gaban ta wanda Rk da kan sa ya yayyanka mata take sha. Se da ta k'arasa shanye mango d'in da ta bari a k'arshe sannan ta mik'e tsaye tana yamutse fuska. D'an tsorata tayi sanda taji ya rik'o ta ta baya, saboda bata san da zuwan sa ba, se kuma da taji k'amshin turaren sa sannan ta sauke ajiyar zuciya tana lumshe idanun ta. Shi ma shak'ar k'amshin da koda yaushe baya rabo da jikin ta yayi kana yace bayan ya juyo da ita ta dawo tana kallan sa, "Ya akayi?" yayi tambayar yana kallan fuskar ta da zuwa yanzun kamar ba ta Ayrahn ba, dan har wani kumatu ta ajje, haka ta jiki ma babu laefi ta d'an bud'e kad'an se dae da yake ba wata me yawa bace kuma dama ta da diri tuntuni yasa ba tayi muni ba. Sake kwa6e fuskar tayi lokaci d'aya kuma tana amfani da hannun ta akan cikin ta, kafin tace komae yabi hannun na ta da kallo sannan yayi murmushin gefen baki "Ko har yanzu abincin ne be fad'a ba?" yayi maganar yana d'age girar sa d'aya sama, kamar jira take se ta soma magana "Ehh fa, ni kam Allah ina ga zan dena ci, kawae na koma shan fruit d'i na" Waro manyan idanun sa masu kyau yayi kana yace "Ki dena cin abinci kuma? Ae ba zaki rayu ba, yanzun da kike kusan cinye flask d'aya?" Ya fad'a cike da tsokana. Se kuwa ta shiga dira k'afar ta lokaci d'aya tana had'e fuska kamar zata yi kuka. Shi ma dama da biyu ya fad'a se yayi murmushi kana ya d'ora hannun na sa akan nata hannun yace "Anan abincin yake zama kenan?" Jinjina kae tayi kafin tace "Ehh ko da yaushe fa, se dae yayi ta min yawo amma baze fad'a ba!" Dariya ce ta sake k'wace masa jin wannan sakarcin na Ayrah, kasancewar bata san da zaman cikin ba. Se da ya sake kafe
Chapter 84 · 0% Book details