Sashe 89
Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya kalleta yanda ya ga tana kallansu kamar wadda ta ga bak'in halitta. Yace cikin er basarwa "Madam.. Kallan fa?" Dariya tayi tana saukar da kanta k'asa, se kuma ta d'ago tace "Laefi ne dan na kalli ababen k'aunata?" Girgiza kae yayi kafin yace bayan ya matso dab da ita "A'ah idan kina so ma ki maeda mu ciki ki huta!" se suka had'a baki wajen yin dariya gaba d'ayan su. .. Se da ya gama komae cikin d'akinsa sannan ya dawo cikin d'akin, zuwa lokacin Little yayi bacci, ya d'auke shi ya sanya shi cikin gadonsa kafin yayi kissing goshinsa sannan ya dawo kan gadon da Ayrah ke zaune tana kallansu. Se suka sakarwa junansu murmushi. Tambayar da koda yaushe take ci mata tuwo a k'warya tayi masa wato "Babe wae ina Muneerah don Allah?" ta tambaya dan kullum idan ta tambaye shi se dae yace be sani ba. Ajiyar zuciya ya sauke kana ya d'auki k'aton blanket dake ajje a gefe, ya sanya hannu ya ja ta jikinsa kana ya ja su kan gadon, ya lullu6a musu blanket d'in sannan ya kwantar da kanta akan k'irjinsa, shiru tayi ta kwanta luff tana jiran jin amsar da zata fito daga bakinsa. Kamar kuwa ya sani se cewa yayi "Ta dad'e da yin aure!" ya fad'a kana yayi murmushi yace "Kin san wani abu?" Girgiza kae tayi tana d'aga kanta ta kalle shi, ya d'an lumshe idanunsa kafin yace "Ina fad'ar haka ne dan kada kiyi sake, na san koda kin yi sake wajen kula dani idan kika tuna zan iya dawo da Muneerah hankalinki se ya tashi. Kin sani dae ina son kulawa.. Dats all." ya fad'a yana kafeta da idanunsa da zuwa lokacin suka lumshe, musamman saboda k'amshin da ke ta tashi daga jikin Ayrahn, dan kuwa ba ga jikinta ba, ba ga gashinta ba, ko ina na jikinta k'amshin yake. Tura bakinta tayi kana tace "Kae Babe!" Hannu ya saka ya kamo fuskarta ya zamana fuskarta ta tana cikin hannunsa ne, ya sake matsar da fuskarsa dab da tata sannan yace "Ko dae Abokiyar zama kike buk'ata ne?" yayi maganar cike tsokana yana taune lips d'insa na k'asa. Had'e face tayi tana k'ok'arin k'wace fuskarta ya sake rik'eta sosae kana yace "Amm.. am just joking Babe.." Duk da itama ta san da wasan yake yi amma ita maganar ma sam bata so, ganin yadda ta 6ata fuska ne ya sanya shi fad'in "Manta da wannan maganar.. Kin san na yi missing naki so much.." Ya fad'a yana kallan red lips d'inta da yau d'in suka k'ara ja kamar an tura su.Ta jinjina kae, tana k'ok'arin fad'in wani abun ta tsinci bakinta cikin nasa. Cike da kewa, soyayya, gami da Zazzafar k'auna ya cigaba da aeka mata da sak'onni. Ita kanta a yadda tayi kewarsa se ta saki jiki suka cigaba da nunawa junansu soyayyar dake d'auke da zallahr kewa. Washegari throughout be fita a gidan ba, yana tare da matarsa yana jin d'uminta dana d'ansa, ko aeki hanata yi yayi, se fita suka yi tare suka ci abinci kana suka yi take away in case suka dawo gida. Ranar gaba d'aya se ta zama ta musamman, yadda ya nuna gaba d'aya lokacinsa nasu ne, duk se take ji kamar tafi kowacce mace dacen miji, hakan ne yasa koda yaushe take godewa Allah da irin mijin da ya bata na nunawa sa'a. .. Haka rayuwar su ta cigaba da kasancewa cikin farin ciki da k'aunar juna. Babu dad'ewa kuma aka saka ranar Yah Sadeeq da Fatimar sa, yayin da ta 6angare guda a koda yaushe kullum Allah k'ara bud'a musu yake yi, harkar siye da siyarwar shaddodi da yadika kullum gaba take yi, dan yanzu haka ma ya bud'e k'aton shago me zaman kansa. Zuwa lokacin kuma Abba ya samu aeki, se dae da yake aekin ba wani shahararre bane yasa yake had'awa da kasuwar, shi ke taemakawa Yah Sadeeq lokuta da dama. Se ya zamana kwata_kwata a harkar da ta shafi sirri su 2 suke abin su. Se dae zasu d'auki mutane aeki su biya su ne kawae. Yanzu zancen da ake ma har gida Yah Sadeeq d'in ya siya musu, duk da Abba be so su tashi ba amma haka aka taushe shi ya hak'ura suka tashi d'in suka koma gidan me yalwar girma da kuma kyau daidai misali. Ta 6angaren Abbu ma ya maeda hankali wajen kasuwancinsa duk da yanzu ba kamar da bane, se dae mutumin nan da ya ta6a salwantar masa da 50mil, ba'a dad'e ba ya sake chanja d'abi'arsa, a cikin sati se yace anyi asarar miliyoyi, da dae Abbu ya fahimci da gasken cutarsa yake yi, se ya sallame shi gaba d'aya, ba ma shi kad'ae ba, se ya cire kowa akan harkar kud'ad'ensa ya zamana daga shi se d'an uwansa Daddyn Muneerah suke harkokinsu. Babu dad'ewa kuma Ayrah ta samu admission a B.U.K, za ta fara zuwa da zarar sun fara lectures. .. Fitowar ta kenan daga wanka d'aure da towel me yalwar girma, zuwa lokacin ta sake zama wata babbar mace, ta k'ara fari, kyau da murjewa. Kae tsaye wardrobe ta wuce dan d'aukar kaya, se idanun ta suka sauka akan kayan dake kan gado, da alama shi ne ya fito da su. Murmushi tayi tana dawowa wajen gadon, ta saka hannu ta d'aga kayan, kamar yadda ta tsammata kuwa riga da wando ne kamar yadda su d'in suka kasance favourite na sa, tun kafin ta ajiye Little ya saka kuka kamar wanda aka mintsina, bata san sanda ta ajje kayan ba jikin ta har rawa yake ta k'arasa kan gadon dake ajje cikin wani farin tattausan towel. Hannu ta saka ta d'auke shi dae_dae lokacin da yake cigaba da tsanyara kukansa yana lalubar hannu. "Wayyo yi shiru Little." Tayi maganar tana k'arasawa ta zauna gefen gado, dan ta san idan har be ji cikin sa ya d'auka ba ko shiryawar baze bar ta tayi ba. Tun kafin ta ida zama ya shigo d'akin sanye cikin k'ananan kayan da suka matuk'ar yi masa kyau, shi kan sa a yanzun har wata k'iba yayi, ya sake kyau da murjewa. Da sauri ya k'araso yana fad'in "Waye ya ta6a min Boy" yayi maganar yana saka hannu ya kar6i Little. Sakar masa shi tayi ita kuma ta mik'e tana fad'in "Yawwah rik'e shi na saka kaya." Kamar wanda ya saba da raenon haka ya shiga rarrashin sa sak'ale a kafad'ar sa, kamar yaron yasan me ake so yayi se kuwa yayi shiru ya koma tsotar farin hannun sa me kyau. Tana saka kayan ta kalli Little d'in tace "Lallae ma yaron nan, Babe kaga fa shiru yayi se kace wani abun na masa." Murmushi Rk yayi kana yace "Ah toh yaro d'an babansa ake fad'a miki." Yayi maganar yana neman waje ya zauna a gefen gadon, duk da haka kuma yaron be cigaba da kuka ba. Se da ta ida saka kayan sannan ta soma k'ok'arin komawa gaban mirror dan d'aure kanta dake a baje a kafad'arta. K'afa ya saka mata dae_dae sanda take k'ok'arin wuce shi, se kuwa tayo kansa, yayi saurin rik'o ta ta d'ayan 6angaren, shi kuma Little na hannun sa na hagu. D'an lumshe idanun sa yayi dan ba k'aramin kyau kayan suka mata ba, dan kuwa sun bi lafiyar jikin ta sosae sun matuk'ar amsar jikin ta kamar dama dan ita akayi su. Se da ya soma d'age girar sa sannan yace "Wannan k'ibar da kike yi anya kuwa?" Narkakkun idanun ta ta d'aga ta zube su cikin na sa kana tace bayan ta d'an 6ata rae dan ita bata so taji yace tana k'ibar nan, dan wani abun kawae tsokanar sa ce babu wata k'iba ta azo a gani da tayi. "Me?" D'an shiru yayi kana yace "Uhmm ko dae Little na dab da samun k'ani ne!" Zaro idanun ta tayi se kuma ta soma k'ok'arin tashi daga jikin sa tana fad'in "Ni dae Allah ka bari bana so.." Dariya yayi yana sake rik'o ta sosae yadda ba zata iya tashi d'in ba, ganin da gasken take ya sanya shi fad'in "Shikenan na janye magana ta!" ya fad'a dan shi ma dama tsokanar ta kawae yake yi dan kuwa a lokacin ma Little watanni ke gare shi. "Uhmm da gaske?" ta fad'a tana kallan sa. Jinjina kae yayi yana murmushi lokaci d'aya yana sakko da little daga kafad'ar sa, wanda ya koma bacci a lokacin. Dukkan su se suka zubawa fuskar sa idanu yana baccin sa hankali kwance. Murmushi ya su6uce akan fuskar kowannen su, musamman Ayrah da take jin k'aunar d'an kamar kullum k'ara mata akeyi, musamman da tun yanzu kamar sa da mahaefin sa ta gama bayyana kanta. "Kamannin ka sun gama bayyana kansu a fuskar Little Babe." ta fad'a tana sake kallan Little d'in, hannun ta akan farar fuskar sa. "Really..?" ya fad'a yana murmushi, be jira tace komae ba ya d'ora da "Next idan kika tashi me kama da ke nake so." Tura d'an k'aramin red lips d'in ta tayi kana tace tana kallan sa "Kae dae kullum koh? Allah kuwa akwae wahala fa." lumshe idanun sa yayi kana yace "Kar ki damu Babe, daga yanzu ni zan dinga taya ki Uhmm? Kin san in dae 'ya'ya daga gare ki ne ban k'i ki ajje min 20 ba." Yayi maganar yana jan ta ya had'a da Little ya rungume cikin jikin sa idanun sa a lumshe yace "K'aunar ki a cikin jiki na take Babe, Ina k'aunar ki irin sosae d'in nan." ya fad'a da gasken yana jin k'aunar ta har cikin jinin jikin sa. Rungume shi itama tayi sosae idanun ta a lumshe, Little na tsakiyar su tace "Ina k'aunarka sosae Babe.!" ta fad'a a hankali kuma a tausashe. Tana gama fad'ar hakan ya sake ruk'unk'ume su su duka kamar ze maeda su ciki, k'aunar Ayrah da Little na ratsa kowacce ga6a ta jikin sa.. *GAME OVER!!!* *ALHAMDULILLAH!* *ALHAMDULILLAH!!* *ALHAMDULILLAH!!!* *Anan na sauke wannan littafin nawa me suna ZAZZAFAR KAUNA. Abin da na fad'a dae_dae Allah ya had'a mu a ladan, abin da na fad'a ba dae_dae ba Astagfirullah, Allah ka yafe min. Duk wadda na 6atawa rae tun fara ZAZZAFAR KAUNA ina neman afuwar ta, ni kam na yafewa kowa