Sashe 15
Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
se yau "A'ah a k'oshe nake" ta fad'a tana kallan Ruks d'in "Toh dae kin ji, mu duk bama jin yunwa muma, a bar shi kawae pls" "Shikenan ae" Jidda ta fad'a "Kuuu, kun san k'arfe nawa kuwa?" Bahijja ta fad'a tana d'an waro eyes d'in ta "Wani abun ya faru?" Ruks da Jidda suka tambaya lokaci d'aya "Ni kam seda safen ku wallahi, kwanciya zanyi ko dan na tashi da wuri, gobe fa Doctor RK ne a farko, ko kun manta abinda yayi last Monday?" ta k'arasa maganar tana hayewa kan gadon ta "Nima kam seda safen ku" Ruks ta fad'a tana mik'ewa, harara Jidda ta jefa mata sannan tace "Toh ni me zan zauna jira hajiya? Ayrah seda safe" tayi maganar itama tana hayewa gadon ta.. Bin su tayi da kallo su duka lokacin da d'akin yayi shiru, se taji tsoro ya fara shigar ta, dan haka taja jikin ta ta maeda shi kan gadon ta kwanta, ta lullu6e kafatanin jikin ta da hijab d'in ta wani sanyi na ratsa ta, a hankali ta lumshe idanun ta wasu hawaye masu d'umi na sakkowa akan fuskar ta, wayar data tuna da ita ta janyo ta nemo number Yah Sadeeq ta danna kira, bugu 1_2 ya d'aga dan lokacin be kae ga yin bacci ba h Sadeeq.." tayi maganar tana fashewa da wani marayan kuka a hankali, daga can 6angaren Yah Sadeeq ya girgiza kae yana murmushi dan yasan wannan kukan nata bana komae bane sena shagwa6ar data zame mata jiki "Auta rigima" ya fad'a yana murmushi, dae_dae sannan wayar Jidda tayi k'ara, taja tsaki daga inda take kwance tana amsa wayar ba tare da tasan me kiran ba, daga can 6angaren akace "Jidda don Allah kimin snapping aekin nan zanyi copying kafin gobe.." "Don Allah kiyi hak'uri Abeedah, ki koma kije kiyi bacci ko dan gobe ki samu shiga class d'in" banji me akace daga can 6angaren ba amma naji Jidda tayi dariya tace "Doctor RK fa.." daga inda Ayrah ke kwance ta d'an lumshe idanun ta tana jin yadda ta gaji da jin sunan da suke ta ambata tun d'azu, sunan da kusan duk hirar da suke tun d'azu a kansa ne suke yin ta, seta gyara kwanciyar ta ta kawae duk da tasan yau dae ba zata iya baccin ba... _*Yanzu wasan ze soma*_ Mhiz Innocent..... https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* *TITAN'S OF TALENT* Page 013_014 ___Washe_gari tun asuba ta tashi tayi wanka ta gabatar da sallah sannan ta cigaba da zama kan carpet d'in da tayi Sallahr akae tana addu'a, bata dad'e da zama ba su Jidda ma suka farka kusan a tare, Jidda ce ta fara shigewa toilet yayin da Ruks da Bahijja suka tsaya a bakin toilet d'in kowacce na jira Jidda ta fito itama ta shiga. Tana nan zaune haka suka dinga sauri suna shiryawa kafin wajen k'arfe 7:30 dukkan su suka gama shiryawa kusan duk cikin dogayen riguna da k'ananan mayafae, Bahijja dake saka boot a k'afar ta tace "Kin gama shiryawa ne, ko har yanzu addu'ar ce ba'a gama ba?" tayi maganar tana kallan Ayrah, seta girgiza kae kafin tace "A'ah ku jira ni yanzu zan shirya" "Ayrah mun yi gaba, kiyi sauri ki shirya ki taho kafin 8 tayi" Ruks ta fad'a sanda take d'aukar jakar ta, jinjina kae kawae tayi ba tare da ta sake cewa komae ba, ta bisu da kallo sanda suke ficewa daga d'akin. A hankali ta mik'e ta sake fad'awa toilet ta wanko fuskar ta sannan ta fito ta shirya cikin riga da skirt na atamfa kana ta saka hijab, ta d'auki sabuwar jakar da Yah Sadeeq ya siya mata wadda ta zuba littafan ta a ciki ta fito daga d'akin. A hankali take takawa a cikin filin makarantar cikin nutsuwar ta, duk da babu abinda ta shafa akan fuskar ta amma tayi kyau sosae, bayan ta d'auke da jakar goyo yayin da ta rungume wasu text books guda 2 wanda suma duk Yah Sadeeq ne ya siya mata saboda ta samu sauk'in karatu. Tun kafin ta k'arasa inda ze sada ta da ajin nasu taji shiru kamar babu mutane cikin ajin, har seda ta fara tantamar anya kuwa ba tayi 6atan kae ba?, dab da zata isa wajen ajin sassanya kuma daddad'ar muryar sa ce ta fara dakar mata kunnen ta, ba'a iya jiyo abinda yake fad'a d'in amma tana iya jiyo sautin yadda nutsatstsiyar muryar tasa ke fita, haka kurum taji k'irjin ta ya buga da wani irin k'arfi har seda ta dakata daga inda take tafe na wasu en mintuna kafin ta lumshe manyan idanun ta kana ta bud'e su tana mamakin yadda bugun zuciyar ta ya sauya cikin k'ank'anin lokaci. Da sallama akan la66an ta ta sanya k'afa cikin ajin nasu ba tare data kalli kowa ba, dan bata jin zata iya kallan kafatanin en ajin dan tasan duk idanun su na kanta ne "Hey!" nutsatstsiya, sanyayyiya kuma daddad'ar muryar sa me dad'in saurara ta daki dodon kunnen ta, a take kuma a lokaci guda k'afar ta ta d'auki rawa wanda har yanzun ta kasa gane dalilin wannan rawar da jikin nata ke yi "Ko dae da ita ake?" ta tambayi kan ta, gudun kada taje tayi laefi ya sanya ta dakatawa daga inda take, a hankali kuma ta shiga juyowa zuwa inda yake tsaye sannan ta d'aga raunannun idanun ta ta aza su inda ta tabbatar yana tsaye, ba ita yake kalla ba idanun sa na kan wani littafi dake gaban sa ne, kyakykyawa ajin farko, fari me kyakykyawan jiki kuma cikin kyakykyawar shiga, sanye yake cikin wasu riga da wando da suka dace da k'irar jikin sa, a saman kayan kuma suit ce itama me kyau, kansa babu komae se kwantacciyar bak'ar suma da tasha gyara na musamman, kamar yadda take a gyare haka kyakykyawan bak'in sajen sa ma yake a gyare kuma a kwance wanda hakan ba k'aramin k'arawa kyakykyawar fuskar sa kyau yayi ba, ganin da tayi ba ita yake kalla ba dan ita kanta bata ganin fuskar sa se gefen fuskar ta sa, seta d'an lumshe idanun ta kafin a hankali ta fara k'ok'arin juyawa "Hey, go out!" ya sake fad'a har lokacin be kalle ta ba, kawae se tayi shahada ta tabbatar da ita yake, har lokacin bata kalli kowa ba taja k'afafun ta ta fice daga ajin. Kae tsaye hostel ta koma har lokacin tana tuna sautin muryar sa a cikin kwanyar ta sannan kuma tana hana k'wallar data tarar mata a idanu zubowa, tana shiga ta ajjiye jakar ta ta haye kan gadon ta jinginar da kanta a jikin gado, iska ta fesar daga cikin bakin ta tana d'an jan numfashi kafin ta sanya hannu ta goge hawayen da suka fara sakkowa akan fuskar ta, a hankali ta cigaba da jan sheshshek'a tana jin wani irin zafi wanda da farko bata ji shi ba se yanzun, ta tsani yarfi, ta tsani dizgi, se gashi her first day in University wani yayi embarrassing na ta a baenar nasi, d'an mitsitsin bakin ta ta murgud'a kamar wani na kallan ta sannan tace akan la66an ta "Bashi da kirki". Tafi awa 1 a cikin hostel d'in seda ta kitanci lokacin da tasan ya fita sannan ta mik'e ta fita zuwa ajin nasu, cikin sa'a kuwa babu kowa cikin ajin a lokacin, se students kawae da kowa ke harkar gaban sa, koda ta shiga cikin ajin duk seta ji ta a takure musamman da taji a jikin ta idanun mutane da dama na yawo ne a kan ta, se take ganin kamar kowa kallan ta yake da wadda aka kora d'azu, duk se ta ji tana neman sark'ewa a tafiyar da take, gaba d'aya ma ta rasa inda za taje ta zauna, tsintsiyar hannun ta taji an kama se ta juya da sauri ta d'aga idanun ta ta kalli wadda ta rik'e mata hannun, Jidda ce, seta sauke ajiyar zuciya hadda lumshe idanun ta tana bud'ewa lokaci guda "Muje ki zauna" Jiddan ta fad'a tana cigaba da jan ta zuwa cikin ajin, babu musu kuwa kamar wata doluwa ta bita cike da sassarfa, wani dake zaune kan wani bench yace yana kallan Jidda "Hajiya Jidda an samu wata kenan?" seta juya ta watsa masa harara sannan tace "Shishshigi ba kwarjini" dariya yayi hadda dukan bench yace bayan ta wuce wajen "Yoh shishshigi kuma ya kae wanda kika yi?" ita dae bama taji shi ba suka k'arasa inda suke zaune sannan tace tana Kallan Ayrah "Yawwah ki zauna, nan ne kusan permanent seat namu dan tunda muka zo anan muke zama" murmushin yak'e Ayrah tayi dan har ga Allah wajen be mata ba, dan kuwa a baya ne bench d'in nasu yake, se dae ta nemi waje ta zauna kawae. Basu suka koma hostel ba a ranar se wajen k'arfe 6, dan haka suna komawa Ayrah ce ta fara fad'awa toilet tayi wanka dan sosae ta gaji tana fitowa ta zira doguwar riga mara nauyi ta maeda hijab d'in ta tayi sallah kana ta nemi waje ta zauna still dae da hijab d'in , dan haka kawae tunda tazo d'in tafi jin ta comfortable idan ta saka hijab d'in. "Toh mu dae kinga had'a girkin mu muke, kawae kowaccen mu zata kawo abincin tane duk abinda muke so se mu dafa muci, kema ayi hakan dake?" Ruks ce me maganar tana kallan Ayrah, seda ta d'an yi jimm, saboda haka kawae taji basu wani kwanta mata can ba musamman daya kasance hirar su gaba d'aya rabin ta ta samari ce, tun jiyan kuma da tazo ba taji wata a cikin su tayi maganar karatu ba, amma kuma suna da kirki yadda suka tarbetan kawae ma ya mata dad'i dan haka se tace "Tohm.." "Ohk guys..me zamu dafa?" Ruks ta fad'a tana kallan su su duka, ta6e baki Jidda tayi kana tace "Kawae mu dafa indomie, dan ni yunwa nake ji" "Nima dae kam" Bahijja ta fad'a itama, mik'ewa Ruks tayi ta nufi inda kayan abincin nasu ke ajiye cikin d'an k'ank'anin lokaci ta d'ora musu Indomien, sanda take zuba Maggi a ciki ne ta jiyo muryar Jidda na fad'in "Ke ni tun d'azu nake so mu tattauna akan shigar Doctor RK ta yau, amma wannan Abeedar