← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 90

Sashe 69

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mata cikin k'ank'anin lokaci ta ji jikin ta ya mata dad'i se d'an abinda ba'a rasa ba. Fitowa tayi daga wankan da ya bar ta tayi cikin toilet d'in bayan k'aramar dramar da suka yi, hakan ne ya sanya shi k'yale ta ya fito ya bar ta dan baya so lokaci ya k'ure basu isa gidan na su da wuri ba, dama tun d'azun ya d'auko mata wata abaya me kyau ya ajje mata kan gadon, se da ta gama shafa mae ta saka kwalli duk yana ankare da ita amma be je inda take ba saboda tsaro, sannan ta tashi ta k'arasa ta d'auki rigar dake ajje gefen sa, tana k'ok'arin komawa dan shigewa toilet d'in ta saka a ciki yayi saurin rik'o ta yana dariyar yadda take ta sauri dan kada ya lura da ita, se dae bata san tun fitowar ta yake ankare da ita ba. "Ki saka anan ko kuma na saka miki" ya fad'a bayan ya tsaeda dariyar da ya ke yi, se da ta murgud'a bakin ta sannan tace ciki_ciki "Toh zan saka ae" "Iyee!! Wato har da murgud'a baki koh? Lallae kam na yadda kin warke" yayi maganar yana jinjina kan sa gami da cije lips d'in sa na k'asa, se tayi saurin zamewa daga jikin sa tana d'auke kan ta daga kan fuskar sa, a ran ta tana sak'a yadda shi sam ba shi da kunya, d'aukar rigar tayi ta zura kana ta zame towel d'in ta maeda shi cikin toilet d'in kana ta dawo cikin parlourn. Matsowa kusa da ita yayi hannun sa d'auke da mayafin rigar yace "Zauna na d'aura miki" dariya ce ta k'wace mata, se dae har lokacin bata kalle shi ba dan idan ta tuna abinda ya faru d'in nan se taji kamar k'asa ta tsage ta shige "Ba fa d'aurawa ake yi ba" "Ohh" ya fad'a yana bud'e idanun sa cikin shagala da kallan ta sanda take dariyar, se ta saka hannu ta kar6a daga hannun sa kana ta yafa a kan ta sannan ta juyo ta kalle shi tace "Toh mu tafi na shirya" Kallan ta yayi sosae har se da ta d'an kautar da kan ta tana 6ata rae, yayi murmushi kana ya mik'e daga inda yake zuwa inda take, babu 6ata lokaci ya rungume ta kafin a hankali yace "Kin yi kyau sosae Baby gurl" ba tace komae ba se murmushi kawae da tayi. "Kin tabbatar bakya jin komae a jikin ki, zaki iya tafiya?" yayi maganar cikin kunnen ta, d'aura hannun ta duka biyun tayi akan fuskar ta duk da baya ganin fuskar ta, ba tace komae ba kawae tayi shiru tana ji kamar kada ta d'ago fuskar ta, tambayar ta sa ta sake tuna mata da inda zasu je d'in, bata jin komae a jikin ta se d'an abinda ba'a rasa ba, kafin ta kammala tunanin ya d'ago ta daga jikin na sa kana ya koma cikin d'akin ya d'auki abinda ze d'auka sannan suka fito daga cikin d'akin. Se da ya bud'e mata k'ofar ta shiga ta zauna sannan ya koma part d'in Muneerah, a parlour ya tarradda ita, tana ganin sa ta taso da sauri ta rungume shi, yanzu kam be hana ta se shima rungume tan da yayi duk da yadda k'amshin fatar ta baya masa dad'i amma haka ya maaze, sake rik'e shi tayi sosae se ya d'an janye ta daga jikin sa kana yace "Zamu fitan ne" se ta kalle shi cike da buk'atar k'arin bayani, ganin hakane ya sanya shi fad'in "Zamu je gidan su ne, saboda haka ki zauna zuwa anjima In Sha Allah zamu dawo, kema idan kina so se ki shirya na kae ki gida" jinjina kae kawae tayi kafin tayi k'arfin halin fad'in "Toh" se dae zuciyar ta fall take da haushi, dan ta d'auka yau d'in ze bar su su kad'ae ne a gidan, tayi amfani da wannan damar ta aekatawa Ayrahn abinda tayi niyya. Se da ya ajje mata kud'i sannan ya fice daga d'akin, ta bi shi da kallo tana jin kamar ta bi shi har gidan su Ayrahn, tana kuma ji kamar ta lek'a ta ga Ayrah, se dae ta san se dae ta shak'o bak'in ciki, hakan ne ya sanya ta komawa kawae ta zauna tana cigaba da sak'a abinda zata yi. Hannun ta d'aya na cikin na sa sanda yake driving d'in, duk da yadda tayi k'ok'arin zamewa amma yak'i bata dama, hakan ne ya sanya kawae ta hak'ura, a haka har suka k'arasa gidan. Kae tsaye part d'in Ummee suka wuce, yana gaba yayin da take bin sa a baya, suna shirin shiga d'akin yayi dae_dae da lokacin da Abbun da Ummeen suka fito daga cikin d'akin a shirye, Abbu ya kalli Rk yace "Ka zaunar da mu" se da ya shafi gefen kan sa sannan yace "Amin afuwa Abbu" Har k'asa ta tsuguna haka kawae taji k'irjin ta na bugawa musamman da ta tuna Ummee, tace muryar ta a sanyaye "Barka da wannan lokaci" kusan tare suka amsa da "Barka dae.." ba zata iya cewa ga a yanayin da taji muryar Ummee ba se dae ta sake jiyo Abbu na fad'in "Kuna lafiya?" "Alhamdulillah" ta fad'a har lokacin kan ta a k'asa "Toh Madallah" ya fad'a yana yin gaba Ummee ta rufa masa baya bayan sun gaesa da Rk, se a lokacin ta tashi duk jikin ta na rawa, ya kalle ta yanda duk ya ga ta wani rikice lokaci guda, kamar ba zece komae ba se kuma ya k'arasa dab da ita yace bayan ya saka hannu ya rik'o k'ugun ta. "Meya faru?" da sauri ta girgiza kae kafin murya na d'an rawa tace "Ba..komae" "Kin tabbatar?" nan ma dae jinjina kan tayi kawae. Ba dan ya yadda ba ya cika ta se dan ya san su Abbun jiran sa suke yi, hakan ne ya sanya shi k'arasawa zuwa wajen motar sa, Ayrah ta bi bayan sa. Se da su Abbun suka fara shiga motar su sannan ya bud'e mata murfin motar, kunya kamar ta nutse, shi kuwa ko a jikin sa, ta hau sannan ya rufe k'ofar ya zagaya ya tashi motar suka fice daga gidan, Abbu da ke driving da kan sa ya ja motar sa ya bi bayan Rk d'in. .. Tun kafin ya k'arasa parking ta kae hannun ta da nufin bud'e motar, se taji ta a rufe, ta juya ta kalle shi fuskar ta a narke, dan ba k'arya ta k'agu tayi tozali da iyayen na ta da kuma Yah Sadeeq d'in ta, shima maraeraece fuskar yayi kamar yanda tayi sannan yace "Yanzu fita zaki yi?" buga k'afar ta tayi a k'asa kafin tace "Don Allah ka bud'e min kaaji?" "Se kin sunbace ni" yayi maganar cikin basarwa yana komawa ya zauna hannun sa sak'ale a k'irjin sa, kallan sa tayi da sauri, ganin da gasken bashi da niyyar bud'e mata k'ofar, kamar zata saka ihu haka ta sake kallan sa, se ya matso kusa da ita sosae kana ya rufe idanun sa yace "Uhm humm" itama runtse nata idanun tayi kana ta k'arasa cike da kunya dan dae ta k'agu ta sauka ne ta sumbaci gefen bakin sa, tana shirin janyewa yayi saurin rik'o bakin na ta ya bata zazzafan kiss dan ya san yau d'in kafin ya sake samun wannan damar may be se dare kuma, waro ido tayi jin yadda yayi mata wayo, se da yayi son ran sa sannan ya sake ta ya koma gefe yana sauke ajiyar zuciya, rau rau tayi da idanun ta tana rik'e bakin ta da har lokacin rinewar da yayi tana nan. "A'ah pls kada ki yi kukan nan Uhmm? So kike su Umma suyi tunanin wani abun?" seda ta tura bakin ta gaba sannan tace "Kalli fa yadda baki na yayi ja, idan aka gane fa?" dariya yayi son ran sa hadda rik'e ciki kamar ba shi ba kana yace "Se dae idan ke kika fad'a, amma babu me ganewa" "Toh bud'e min" tayi maganar ba tare da ta kalle shi ba, dan ita dae har yanzu wannan rashin kunya ta sa ta kasa sabawa da ita, yanzu kam babu musu ya bud'e mata, bata jira komae ba kuwa ta sauka da saurin ta ta k'arasa cikin gidan, saboda har lokacin jikin ta be gama komawa dae_dae ba da gudu zata saka. Kae tsaye d'akin Umma ta fad'a tana k'wala mata kira. Yah Sadeeq dake zaune shi da Umma da Abba ya kalli Umma yace "Da alama fa yau Autar ki ta yiwa gidan nan tsinke" ya fad'a yana murmushi, suma dukan su murmushi suka yi kowannen su cike da jin dad'in zuwan na ta. Dae_dae lokacin da ta shigo cikin d'akin babu 6ata lokaci ta fad'a jikin Umma ta rungume ta, itama Umman rungume ta tayi cike da kewar d'iyar ta ta, jin da Umma tayi ta fara sauke k'walla ya sanya ta fad'in "Zaki fara koh? Bana so" se tayi murmushi tana tashi daga jikin Umman tace "Nayi kewar ki sosae Umma ta" kallan ta Umma tayi sosae ganin yadda fuskar ta tayi fayau idanun ta sun d'an ta sa se dae farin ta ya sake fitowa kamar ka tsaga jini ya fito. "Nima haka Auta, kina lafiya?" seda ta goge idanun ta sannan tace "Ehh lafiya k'alau Umma" ta fad'a tana juyawa ta koma wajen Abba dake zaune har lokacin yana kallan d'iyar ta sa, har gaban sa ta k'arasa ta tsuguna tana murmushi tace "Abba barka da wannan lokaci" "Barka dae Ayrah, duk kuna lafiya?" ya fad'a bayan ya kae hannun sa kan ta ya shafa sannan ya d'auke dae_dae sanda ta furta "Ehh Abba.. Yah Sadeeq barka da wannan lokaci" tayi maganar a had'e se dae ta kae k'arshen maganar tana kallan Yah Sadeeq, murmushi yayi kana yace "Barka dae lily, kin zo lafiya?" Maganar Abba ce ta katse su daga cigaba da gaesawar da suke yi sanda yake fad'in "Ke kad'ae kika zo ne?" bud'a baki tayi dan har ga Allah shaf ta manta ba ita kad'ae bace. "A'ah Abba, tare muka zo hadda Abbun sa da Ummee" kallan ta su duka suka yi cike da mamakin abinda ta fad'a d'in, kafin Abba yayi k'arfin halin fad'in "Abbun sa kuma? Kina
Chapter 69 · 0% Book details