Sashe 59
Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yau d'in nan, ze ga kuma da wane ido zata kalle shi idan yazo ya gan ta ta dawo. Tunda ya shigo layin yake kallan motar dake k'ofar gidan, be gane ta wacece ba se dae mamaki ya kama shi sosae, a ran sa yake sak'a wanene a gidan nasu? Be bawa hakan muhimmanci ba ya k'arasa yayi parking motar ta sa saboda yadda motar Muneerah tayi blocking hanyar da zebi ya shiga cikin gidan, wani mamakin ne ya sake kama shi sanda yaga k'ofar ma kan ta a bud'e, da sauri ya k'arasa parking d'in ya fito daga cikin motar cike da sassarfa ya durfafi gidan. "Karuwar banza karuwar wofi" Muneerah ta fad'a dae_dae lokacin da Ayrah ta isa bakin Gate d'in kuma a dae_dae lokacin daya sako kan sa cikin gidan, gaba d'aya idanun ta sun cika taff da k'walla ta yadda ko gaban ta da k'yar take gani, hakan ne ya sanya ta d'an runtse idanun ta ko da hakan ze bata damar gani da kyau har ta iya juyawa ta fad'awa Muneerah maganar da duk tazo mata a cikin zuciyar ta, dan a yanzu kam yadda take ji ba Muneerah ba ko wacece ta kira ta da Karuwa seta fad'a mata magana, bare kuma Muneerah d'in ce ta fad'a mata magana, tana k'ok'arin juyawa se kawae suka yi karo da shi, sam be lura da wad'anda ke cikin gidan ba, saboda yadda yaga Ayrahn gaba d'aya ya rud'a shi, ashe ba'a banza ba hankalin sa ya gaza kwanciya tun acan d'in ba, hakan ne ya sanya shi saka dukka hannayen sa ya mata wata kyakykyawar runguma cike da fargabar abinda ya sanya ta kukan, haka kurum yaji bugun zuciyar sa ya k'aru duk da be san aenahin abinda ya faru ba, jin ta cikin jikin sa da kuma shak'ar k'amshin turaren sa da tayi ne ya sanya taji w ani rauni ya sake ziyartar ta, itama rungume shin tayi kawae tana fashewa da wani marayan kuka, cikin rikicewa yace a nutse kuma a hankali "Babe me ya saka ki kuka?" ya fad'a yana lumshe idanun sa cike da fargabar abinda ze fito daga bakin ta "Hasbunallahu wa ni'imal wakeel, Inna lillahi wa inna ilaehi rajiun" shine abinda Ummee ta fad'a cikin d'aga murya gaba d'aya duk wani fata nata da kuma kokwanto da take yi yana zagwanyewa k'asa yana yin nasa waje, cike da mamaki, gami da wani tsoro daya ziyarce shi ya d'aga idanun sa ya jefa su zuwa inda yaji muryar na tashi, cikin lokaci k'ank'ani suka yi 4 eyes da Ummee da take kallan sa tana ji kamar ta bud'e baki ta furta duk wata kalma da ta fito daga bakin ta, se dae abinda ta sani ita uwa ce, zata iya fad'a masa magana kuma ta bi shi, dan haka ta kwa6i kan ta da yin maganar, Raj d'in ya shammace ta, ya cuci tarbiyyar da ta bashi, meyasa zeyi mata haka? Muneerah kuwa suman tsaye tayi sanda taga Ayrahn kane_kane a jikin Rk, ta kasa furta komae ta kuma kasa aekata komae, se jikin ta daya d'auki rawa kamar mazari. A hankali ya soma zame Ayrah daga jikin sa yana jin yadda jikin sa yayi wani mugun sanyi, ya d'an lumshe idanun sa a ran sa yana tabbatarwa da kan sa komae yazo k'arshe, duk wani 6oye_6oye ya k'are tunda gashi yana ganin yau d'in asirin sa na dab da tonuwa, komae ya k'are, se ya shiga takawa zuwa cikin gidan dae_dae lokacin da idanun sa suka sauka akan Muneerah dake tsaye kamar an dasa ta, seya d'auke kan sa ya maeda kan Ummee da duk yanayin ta ya nuna damuwa muraran "Ummee.." d'aga masa hannun da Ummee tayi shine ya sanya shi dakatawa da fad'in abinda yayi niyyar fad'a "Kada ka sake kace min komae, kada ka soma Suraj" shine abinda Ummeen ta fad'a jikin ta a matuk'ar sanyaye, bata jin zata iya furta wani abun bayan wannan d'in, shi kuwa runtse idanun sa yayi k'irjin sa na bugawa da sauri da sauri yama rasa meya kamata yace, wace kalma zeyi amfani da ita wajen kare kan sa a wannan lokaci? Wuce shi da Ummee tayi ne ya sanya shi d'aga ido ya kalle ta kafin yace komae ya jiyo muryar ta har lokacin a sanyaye se dae kamar a fusace take "Ka wuce muje.." nan ma tana gama fad'a tayi gaba, Muneerah, Aunty Zeenah da Bahijja suma suka bi bayan ta kamar rak'umi da akala, a haka suka zo suka wuce Ayrah dake tsaye a wajen da ya barta, bata ta6a tunanin Ummee zata kalli inda take ba se dae abinda tayi mamaki shine jiyo muryar Ummeen da tayi tana fad'in "Kema ki biyo ni" daga haka tayi gaba, bata iya bin bayan su da kallo ba se jinjina kae kawae da tayi, Ummee suka fice daga gidan aka bar su saura su kad'ae, seya shiga takowa zuwa inda take tsayen, a hankali muryar sa a cunkushe yace "Mu je" bata tanka ba har lokacin kawae se kallan sa da tayi, ya lumshe mata idanun sa dake cikin na ta yana jinjina mata kae dan ya bata k'warin gwuiwa duk da nasa k'arfin gwuiwar ma a yanzu kad'an ne, daga haka duka suka fito daga cikin gidan, Ummee ya hanga a jikin motar sa hakan ya alamta masa cewar a motar sa zata tafi kenan, dan haka da sauri ya k'arasa ya bud'e mata frontseat, ba tare da ta kalle shi ba ko tace uffan ba ta shiga fuskar ta a had'e se dae cikin zuciyar ta rauni ne fall, bud'e backseat yayi ya kalli Ayrah dake tsaye dake a d'arare ya mata alama da ta shiga, a hankali ta sanya k'afar ta cikin motar tana lumshe idanun ta, se a lokacin ya shiga driver seat ya zauna, be jira Ummeen tace komae ba kawae ya tashi motar ya soma ficewa daga layin, Aunty Zeenah dake driving tabi bayan sa saboda yadda Muneerah yanzu ma ta kasa driving dan yanzu kam ta kasa rik'e kan ta kuka take ta shar6a kamar ran ta ze fita, ta kasa gane dalilin da yasa karuwa ta fita a wajen mijin ta, mafita kawae take nema, dan haka jira take a gama da wannan matsalar a yau d'in nan tayi amfani da turaren wajen Aunty Zeenah. Da k'yar ya iya kallan Ummee da har lokacin ba tace komae ba yace a hankali "Ummee ina zamu je?" "Gida na" ta furta ba tare data kalle shi ba, be sake cewa komae ba ya cigaba da driving d'in har zuwa sanda ya isa cikin gidan. Ummee ce ta fara sauka daga cikin motar sannan ya sauka, ganin haka ya sanya Ayrah ma sauka har lokacin fargaba bata barta ba, seda dukan su suka sauko sannan Ummee ta soma takawa zuwa part d'in Abbu, babu wanda yace komae se bin bayan ta da suka yi su duka kowa da abinda ke sak'awa, take jikin Rk ya sake yin sanyi, lallae tabbas yau d'in dubun sa ta cika, wasa ya k'are, a nutse ya lumshe idanun sa wani 6angare na zuciyar sa na raya masa gwara ma hakan ta kasance ko da shi kan sa ze koma rayuwa da Ayrahn ba tare da fargabar wani ya san da zaman su ba, ita kuwa Ayrah a d'arare take tafiya hakan ya k'arawa tafiyar ta ta sanyi kamar mara laka a haka suka k'arasa parlourn Abbun da har Ummee dasu Muneerah sun riga sun shige, tun kafin su ida shigowa cikin d'akin muryar Abbu ta soma tashi daga cikin parlourn "Fatima ina takaddun da na ajje su shekara da shekaru cikin d'akin nan, ban gan su ba, ke kad'ae kika san da zaman su saboda haka ki sanar da ni ko kin chanja musu waje ne ban sani ba?" Abbun ya fad'a cike da rikicewa yana fatan ba wani ne yasan da wannan 6oyayyen sirrin ba "Abbun Raj takaddu kuma? Wad'anne?" Ummee tayi k'arfin halin fad'in hakan, dafe kan sa Abbu yayi yana komawa ya zauna kan kujera k'irjin sa na bugawa cike da sarewa, gaba d'aya ya d'auka Ummeen ce ta chanjawa takaddun wajen zama saboda ita kad'ae ta san da zaman su, se dae gashi a yadda take nunawa bama ta gane akan abinda yake magana ba "Lallae babu shakka wani ya san da wannan dad'ad'd'den al'amari, tabbas bayan su biyu akwae na uku da ya san da wannan al'amari" ya raya hakan a cikin ran sa, ita kuwa Ummee neman waje tayi ta zauna har lokacin al'amarin Rk yak'i barin kan ta shiyasa ma maganar da Abbun ya mata sam ta kasa bashi muhimmancin daya kamata, dae_dae lokacin da kowannen su ya ida shigowa cikin d'akin, Abbu ya d'aga ido ya kalle su duk da tashin hankalin da yake ciki hakan be hana shi mamakin abinda ya shigo dasu cikin d'akin sa ba a lokacin da yafi buk'atar kad'aeci yayi tunanin abinda ya kamata..... Mhiz Innocent... https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* Page 046 ___"Wad'annan fa me ya shigo da su?" Abbu ya fad'a yana kallan Ummee dake zaune kusa da shi, a hankali ta d'an runtse idanun ta tana tuna maganar da0 zata fito daga cikin bakin ta, dae_dae kuma lokacin da Rk ya nemi k'asa ya zube a wajen, ganin haka ne ya sanya Ayrah da take ji kamar zuciyar ta zata faso k'irjin ta ta fito itama ta nemi waje ta zauna a takure "Ku d'an ara mana wajen" Ummee ta fad'a tana kallan Aunty Zeenah da Bahijja da suka zauna suka yi shiru suna jiran jin abinda ze faru, gaba d'ayan su babu wadda taso hakan, amma se suka mik'e kowacce rae a 6ace suka fice daga d'akin, bin su da kallo Abbu yayi shi kam har yanzu mamaki yak'i barin sa, ya kasa gane abinda yake faruwa, idan kuma wani abun ne ya faru tsakanin Rk da matar sa kamata yayi yaga shi kad'ae da matar ta sa, se dae kuma daga lokacin da ya sake kallan cikin d'akin se ya hangi wata bak'uwar fuska a gefe, rashin fahimtar musabbabin zuwan nasu ya sanya shi sake fad'in "Fateema..!!" Tun kafin ya ajje numfashi tace a sanyaye "Abbu ban san abinda