← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 90

Sashe 68

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da taga yana bin ta da shi shine ya sake sanyawa jikin ta ya k'arasa mutuwa gaba d'aya.. Mhiz Innocent... https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* Page 051 ___Hannu ya saka ya kar6i kwalbar da take a rufe sannan ya sake aza mata idanun sa yace "Menene wannan Muneerah?" ya tambaya cikin sarewa da al'amarin Muneerahn. Duk se ta duburburce ta rasa me za tace, se kawae ta d'auke kan ta daga kallan sa kafin cikin k'arfin hali tace ciki ciki "Nima ban sani ba, kawae ganin sa nayi anan.." "K'arya kike yi!" ya katse ta da fad'in hakan tun kafin ta ida kae k'arshen maganar da tayi. Shiru tayi dan bata san kuma abinda za tace d'in ba, tunda dae ta san ya riga ya gama kama ta, ya kuma gane meye a hannun na ta. Tsaki ya ja yana girgiza kae bece komae ba ya fice daga cikin d'akin, ta bi shi da kallo cike da haushin kan ta da ta bari ya kama ta. Tana nan tsaye ya shigo cikin d'akin, zuwa lokacin ta gaji da tsayuwar ta nemi waje ta zauna akan gadon, d'aukar blanket d'in yayi ya wuce kan gadon, ya d'ora bayan sa akan pillow cike da takaecin Muneerahn, ya fahimci abinda take so, amma kuma mamakin ta yak'i barin sa, wata iriyar budurwa ce ita haka? Wane irin bud'ewar ido ne da ita haka da har zata iya d'aukar turare me jan hankali tayi amfani da shi dan janyo hankalin mijin ta a matsayin ta na budurwa? gudun kada ya tauye mata hak'k'i se ya kalli inda take zaune duk itama ta sha jinin jikin ta, se ya mik'a mata hannu alamar tazo, murmushi ya su6uce mata kana ta mik'a masa hannun har lokacin tana kallan sa, se ya ja ta zuwa cikin jikin sa, kana ya gyara kwanciyar sa akan gadon, luff tayi a k'irjin na sa wani irin farin ciki mara misaltuwa na ziyartar ta, abinda ta dad'e tana nema ne yau d'in ya samu, damar data dad'e tana jira yau ta samu, dan haka bata ganin zata bari wannan damar ta tafi a banza, fuskar ta ce ta d'an sauya sanda ta tuna wata ma tana kwanciya a k'irjin sa kamar yadda take haka d'in nan. "Ya zama dole nayi maganin ta da wurwuri" ta ayyana hakan a cikin ran ta. A fili kuma se ta d'an tashi daga jikin na sa cikin sakannin da basu wuce 5 ba ta soma aeka masa da sak'onni kamar itace namijin shi mace, k'yale ta yayi se ya d'an soma taya ta, ita kuma tayi amfani da wannan damar ta fito da zulamar ta a fili, nan take ta cigaba da aeka masa da sak'onnin a zafafe, mamaki gami da tantama akan Muneerahn ya shige shi, anya kuwa yarinyar nan? Tabbas ya san Muneerah bata ta6a aure ba, amma kuna gashi tana acting kamar bazawara ko kuma wadda ta san d'a namiji, haushi gami da takaeci, mamaki gami da tsoron kada abinda yake zargi ya tabbata yace ganin Muneerahn na cigaba da fito da zilamar ta a fili. "Muneerah!" ya fad'a a kausashe yana bin ta da kallan tuhuma, cakk ta tsaya se ta d'aga idanun ta da suka chanja kala ta kalle shi, ya sake tamke fuska kana yace "Me kike yi haka?" sake duburburcewa tayi ta rasa me za tace, se kuma can wata dabara ta fad'o mata hakan ya sanya ta fad'in "Baby kae ne ka rikita ni" ganin kallan da ya sake bin ta da shi ne ya sanya ta saurin fad'i har tana in'ina "Amm gaba d'aya jiki na ya soma ciwo" ta fad'a tana sauka daga jikin sa cike da haushin kan ta na wannan zak'ewar da take yi, sam idan tana tare da shi manta kan ta take yi, se dae bata san hakan ka iya janyo babbar matsala ba, tuna hakan ne ya sanya ta kama kan ta dan ta san Rk d'in akwae shi da fahimta, dad'in dad'awa kuma likita ne kuma wanda yake da wata matar bayan ita, ze iya fahimtar wani abun musamman yadda take zak'ewa d'in nan. Kallo ya bita da shi sanda ta koma gefen na sa ta kwanta, har lokacin mamaki yak'i barin sa, se kokawa yake da zuciyar sa kada zargi yayi tasiri a zuciyar sa amma hakan ya citira, se kawae ya runtse idanun sa yana d'an sauke numfashi a hankali. Gudun kada ya fahimci wani abun ya sa bata sake koda kuskuren ta6a shi bane tayi shiru cikin blanket tana fatan bacci ya d'auke ta duk da yadda Rk d'in ya d'an motso ta amma ta maaze. ... Washe_gari tunda ta tashi taji jikin ta yayi mata dad'i babu laefi, sosae taji dad'in hakan, dan haka wajen k'arfe 7 ta fad'a toilet tayi wanka, hakan ya kuma sakawa ta sake jin dad'in jikin ta fiye da ko yaushe. D'aure da towel ta fito daga band'akin sanye cikin hijab, se ta k'arasa inda ta tabbatar kayan ta na nan ta d'auko doguwar rigar wani yadi mara nauyi ta k'arasa bakin gadon, zame hijab d'in tayi sannan ta soma saka rigar, kawae se taji an rungume ta ta baya, da sauri ta saki rigar saboda yadda ta tsorata, dan sam bata ji shigowar sa ba, jin yadda jikin ta ya d'auki rawa lokaci guda ne ya sanya shi juyar da ita ta koma kallan mirror kana yace kan sa akan dokin wuyan ta "It's me!" ajiyar zuciya ta sauke tana lumshe idanun ta kafin ta bud'e tace bayan ta tura baki. "Amma ka tsoratar da ni Allah kuwa" murmushi yayi kana yace bayan ya kama kunnen sa d'aya da hannun sa "Sorry..!!" ba tace komae ba se d'aga kan ta da tayi ta kalli cikin mirror, se a lokacin ta tuna towel ne kawae a jikin ta, hakan ne ya sanya ta saurin runtse idanun ta tana had'e jikin ta waje d'aya kafin tace "Shiryawa fa nake" "Ohh really?" ya fad'a yana d'age girar sa sama idanun sa a kan ta yana kallan ta ta cikin mudubin, jinjina kae tayi har lokacin bata bud'e idanun ta ba, yace "Ohk, amma kafin nan ya jikin na ki?" "Na warke fa dama" ta fad'a tana d'an bud'e idanun ta, cigaba yayi da kallan ta har lokacin tana jikin sa kana yace "Anya kuwa? Ta yaya zan yadda kin warke?!" yayi maganar wani miskilin murmushi na wanzuwa akan fuskar sa, tura bakin ta ta sake yi gaba, kafin tace komae ya d'aga ta zuwa kan gado ya zaunar da ita, ita dae se kakkaucewa take yi amma shi da alama ko a jikin sa dan kuwa se cigaba da kallan ta yake yi yana kuma nanik'e ta kamar ze maeda ta cikin sa, daga k'arshe ma se ji tayi ya furta "Pls Babe lem me kiss u a little" ya fad'a bayan ya matso da fuskar ta dab da ta shi, bud'e idanun ta tayi kafin ta bud'e bakin ta da niyyar yin magana yayi amfani da wannan damar wajen cafke bakin na ta ya shiga kissing na ta na tsawon mintuna, se da ya gaji dan kan sa sannan ya cigaba da shak'ar k'amshin sabulu da kuma na turaren da ke tashi daga jikin ta, sosae hakan ya rikita shi, se kawae ya zame ta kan gadon ya soma aeka mata da zafafan sak'onni masu wuyar fassaruwa cike da k'aunar ta. Tsoro gami da fargaba ne suka tarar mata lokacin da ta ga yana k'ok'arin sake maemaeta abinda yayi rannan, se kawae ta rungume shi da iya k'arfin ta wasu zafafan hawaye na zubowa akan kuncin ta tace muryar ta a sark'e kuma a raunane "Don Allah.." lumshe idanun sa yayi bugun zuciyar sa na cigaba da fita da sauri kafin ya kae kunnen sa saetin na ta kunnen yace muryar sa a cunkushe kamar ba ta sa ba "Sorry my.. Baby gurl.." ya fad'a a d'an rarrabe. ... Yau ma seda ta sha kukan ta ta godewa Allah, shi kam ya dinga rarrashin ta musamman da ya lura yau d'in ma ta ji jiki, da kukan gasken da na shagwa6ar duka ya shanye su tass ya dinga biye mata kamar jinjira. Yanzun ma tana kwance akan k'irjin sa tayi shiru se dae har lokacin hawaye na zuba daga cikin idanun ta. "Idan kika yi shiru, yau d'in nan zan kae ki wajen Umma" yayi maganar yana kallan yadda idanun ta suka yi ja. Cakk kukan na ta ya tsaya ta kafe shi da narkakkun idanun ta da shi a ganin sa kamar kyau suka k'ara saboda kukan da tayi, se ya jinjina mata kae alamar tabbatarwa. Bata san sanda murmushi ya k'wace mata ba har ta furta "Don Allah da gaske?" "K'warae kuwa, amma idan kika cigaba se kiyi ta zama anan in cigaba da kallan ki" hannun ta dake cikin na sa tayi saurin zamewa tana kaewa kan fuskar ta ta shiga gogewa tana cigaba da murmushin da yafi kama da na yak'e, se ya shagala da kallan ta yanda murmushin ya mata kyau sosae. "Ae dae na dena" ta fad'a tana kallan sa kafin ta soma k'ok'arin tashi, lokaci d'aya kuma ta kwa6e fuska tuna yadda ta sha fama da jikin ta a waccan ranar, kenan a haka za taje gidan salon a fahimci abinda ya faru tsakanin su? Tuna hakan ya sanya ta share k'wallar da ta tarar mata a ido tana kallan sa. Kallan ta yayi cike da mamakin abinda kuma ya sake faruwa yace "Menene Uhmm?" ya tambaya yana kafe ta da idanun sa, sake maraeraece fuska tayi kana tace "Ba kae ne ba..!" se kuma tayi shiru bata k'arasa ba "Ni ne nayi me?" yayi maganar cike da damuwa, se kawae ta kautar da kan ta gefe tana matse k'walla, murmushi ya saki dan ya lura yau d'in kawae rigima take ji, dan haka kawae ya sake biye mata ya cigaba da rarrashi. Sosae yau d'in ya tsaya tsayin daka wajen ganin ta ji dad'in jikin ta sosae ko dan fitar da za suyi, haka ta dinga lafkewa shi kuma yana rarrashi cike da tausayin ta dan yau d'in ma ya san ta ji jiki babu laefi, sosae kuma hakan ya taemaka
Chapter 68 · 0% Book details