Sashe 71
Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
butulu ne, butulu ma na k'arshe kuwa, na yadda kowanne suna ne zan iya kiran kae na da shi tun kafin a kira ni. Na san na cuce ka, na cuce ka naci amanar ka, na yaudare ka da sifa ta, daga k'arshe na bar ka a cikin ruwa tsundum. Hak'ik'a zan iya kar6ar sunan mutumin banza, maci amana, kuma maha'inci, se dae daga lokacin da abubuwa suka fara juya min, d'ana ya auri d'iyar ka ba tare da sani na ko sanin ka ba naji komae ya fara chanja min, komae ya sauya min, na soma tuna yadda akayi na tara dukiya ta, na kuma tuna kae d'in kana cikin wane hali? Daga wannan lokacin naji duk duniya bani da burin da ya wuce ace na had'u da kae kafin na koma ga Ubangiji na, na nemi yafiyar ka, dan na san idan na mutu da alhakin ka a kae na ban san ya zanyi ba, na san se Allah ya bi maka hak'k'in ka, shiyasa na taso nazo na nemi yafiyar ka, don girman Allah ka yafe min, ka yafe min, bama se ka fad'a min a cikin halin da kuke zaune ba ta sanadiyya ta ba, na gani da ido na kuma hakan ya sake karyar min da zuciya, ya sa na sake gane lallae ni d'in maci amana ne kuma mugu" Abbu ya k'arasa maganar yana goge hawaye. Rk da Ummee gaba d'aya kallan sa suke yi cike da mamaki da kuma tausayi, dan kuwa sun riga sun san abinda ze saka Abbun kuka babba ne, abin da ze saka Abbun kuka abu ne me matuk'ar wuya, dan ba ga Rk ba hatta Ummee zata iya cewa bata ta6a ganin Abbun na kuka ba, se ga shi yau d'in yana kuka yana neman yafiya, tabbas har cikin zuciyar sa yake neman wannan yafiyar. Shiru ne ya wanzu na tsawon sakanni, kowa ya cigaba da sak'a da warwara. Ba zaka ta6a tunanin Abban ma na jin Abbu ba sanda yake maganar, se da Abban ya d'aga kae ya kalli Abbu lokacin da idanun sa suka chanja kala abinda ba kasafae hakan ta fiye faruwa ba yace "Kenan kana nufin kace da gasken gaske guduwa kayi ba zargi ba Kabeeru?" duk da tambayar bata da dad'i amma a wajen Abbu shi ta masa dad'i, ko babu komae Abban ya kula shi, ya nuna kuma ya ji maganganun da ya fad'a masa. Cike da danasani da kuma tirr da halin sa shi kan sa yace yana jinjina kae "Gaskiya ne wannan, ba zargi bane Alhaji kayi hak'uri, wallahi guduwa nayi saboda son zuciya da kuma son abin duniya.." Yanzun ma cike da takaeci Abbun ke magana. "Mun san abin da muka yi bamu kyauta ba, mun cuce ku kuma mun cuci kan mu, mun wulak'an ta kan mu, amma gamu kan mu bisa wuyan mu, gwuiwoyin mu a k'asa muna neman yafiyar ka, don Allah, don Allah kayi hak'uri ka yafe mana" Sosae Rk yake kallan Ummee dake magana, dan sosae yayi mamakin abin da ke fitowa daga cikin bakin ta, be ta6a tunanin Ummeen ka iya sakkowa cikin k'ank'anin lokaci haka ba. "Dama shine abin da ya kawo ku?" Abba ya tambaya yana kallan su su duka. Da sauri suka jinjina kae kusan a tare kafin Abbu ya soma magana, "Shine muhimmin abin da ya kawo mu, bayan haka kuma wallahi wallahi a yanzu haka ni me iya sadaukar maka da duk abin da na mallaka ne matuk'ar hakan ze saka ka manta da abin da na maka ka yafe min, sannan takaddun ka ma duka mun zo da su, ina fatan hakan ze saka ka yafe mana se dae ba dan su ba ba kuma dan darajar su ba se don Allah" Murmushin yak'e Abba yayi kafin yace bayan ya girgiza kae, "Har abada bana buk'atar wani abu daga wajen ka, takaddu na dae ka ajiye min su, kud'i kuwa kae suka dama bani ba, ni kullum cikin godiyar Allah nake tunda gashi ina rayuwa ta a hakan babu kud'in kamar yadda ka tara kuma cikin kwanciyar hankali, saboda haka ina ganin yanzu zaku iya bar min gida koh?" Da sauri Rk ya kalli Abba, be so ace ya tanka ba tun fara maganar se dae yana ganin a wannan ga6ar ya kamata ya tofa albarkacin bakin sa dan haka yace "Abba don Allah kayi hak'uri, ba dan halin mu ba ba kuma dan wani abun ba, wallahi Abbu yayi nadama ya kuma yi danasanin abin da ya aekata" d'aga ido Abba yayi ya kalli Rk har seda hakan yasa Rk d'in sauke kan sa k'asa yana jiran jin amsar da zata fito daga bakin sa. Ya d'auki wajen minti 1 bece komae ba se kuma can ya d'aga kae ya kalli Umma dake kusa da shi, ta jinjina kan ta lokaci d'aya tana rufe idanun ta ta kuma bud'e su, shima lumshe nasa idanun yayi kafin yace a nutse, "Ba dan kae d'in ba, ba kuma dan halin naka ba, na yafe maka, dama bana tunanin ko da ka zo ko baka zo ba zan mutu ne ba tare da na yafe maka ba, ba kuma dan wani abun ba se dan sanin da nayi Allah na son masu yafiya, yanzun kuma da kazo se ka hutashe ni da rik'on abu a cikin zuciya ta, dan haka ina ganin daga wannan babu wani ragowar abu daya rage kaje na yafe maka.." Babu wanda be ji dad'in abin da ya faru ba ciki kuwa hadda Yah Sadeeq da Umma. Se dae farin cikin da Abbu ke ciki ya ninka na kowa, ya ri6anya na kowa, ji yake kamar yayi kuka ko ze ji dad'i, haushin kan sa da kuma takaecin abinda yayi na cigaba da dawo masa, musamman idan ya tuna mutumin da ya yaudara d'in yaci amanar sa, mutum me wankakkiyar zuciya da kyawun hali, mutum me dattako da sanin ya kamata. A hankali Abbu ya d'aga kan sa ya dubi Abba hannun sa dafe da saetin zuciyar sa dake zillo kamar zata faso k'irjin sa yace "Allah ya saka maka da gidan Aljanna, Allah ya biya maka buk'atun ka na alkhaeri, Na gode, na gode sosae, Allah ya saka da alkhaeri, ina kuma amfani da wannan damar wajen sake baka hak'uri, Allah ya k'ara girma, Na gode Nagode" shine abin da Abbu ya fad'a yana ji kamar ya kwanta a wajen ya nemi yafiyar Abba (abinda yafi tsugunawa kenan). Shi dae Abba bece komae ba ya mik'e ya shige d'akin sa, babu kuma wanda yace komae har ya shige d'akin. Mik'ewar da Umma tayi ne ya sanya Ummee fad'in "Pls ki sake yi mana godiya wajen sa" "In Sha Allah" Umma ta fad'a tana bin bayan mijin ta. ... "Ina ganin zuwa gobe idan Allah ya kaemu zamu shiga Zaria, ina so na gama komae cikin satin nan, na had'a komae na tattarawa Abban Sadeeq komae na sa da kuma takaddun sa In Sha Allah" Abbu ya fad'a bayan d'aukar tsawon mintuna da suka yi babu wanda yace komae sanda suka fito daga cikin gidan. Ajiyar zuciya Rk ya sauke kafin yace "Toh Allah ya kaemu" "Ameen, amma matan na ka fa?" Abbu ya fad'a a hankali dan har lokacin be gama komawa dae_dae ba. Iska Rk ya d'an furzar daga bakin sa yana lumshe manyan idanun sa yace "Duk yadda kace Abbu" girgiza kae Abbu yayi kafin yace "A'ah ka yanke komae da kan ka, amma dae idan ta ni ne ina ganin ka bar su anan d'in tunda aeki zamu yi acan d'in" jinjina kae Rk yayi kafin cikin k'arfin hali yace "Toh" daga haka be sake cewa komae ba, hankalin sa duk se ya tafi kan yadda zeyi wasu kwanaki ba tare da Ayrah a kusa da shi ba. .. A d'aya 6angaren kuwa tana zaune kan kujera ta d'ora kan ta tayi shiru, Umma ta shigo d'akin, ta bi ta da kallo na en wasu sakanni kafin tace "Ayrah" se ta d'aga idanun ta ta kalli Umman sannan ta gyara zaman ta. "Ki tashi ku tafi mana, ko anan zaki kwana?" Umma ta tambaya tana cigaba da kallan ta. "Umma ban sani ba nima fa" ta fad'a tana d'an 6ata fuska, girgiza kae Umma tayi kafin tayi murmushi tace "Toh maza tashi kije ki ji, idan tafiyar ce se kizo muyi sallama ki wuce, idan kuma kwanan ne kuyi sallama ki shigo gida" har ta mik'e se kuma taji kunya ta kamata bata san sanda tayi wani murmushi ba tana rufe idanun ta. Fahimtar abin da take nufi ya sanya Umman taya ta murmushin, se dae kawae tayi k'arfin hali ta fice daga cikin d'akin a nutse. Bin ta da kallo Umma tayi, ita dae tunda taga d'iyar ta ta taga kamar ta chanja, kamar an chanja mata ita, yanzu kuma da ta sake ganin ta se ta fahimci tabbas akwae wasu sauye_sauye a tattare da d'iyar ta ta, tabbas zata so ace bar mata ita za'a yi tayi kwana ko da 2 ne zuwa 3 ta samu damar gyare ta ko da ba me yawa bane, ta samu damar da bata samu ba da farkon kae ta gidan ta, se dae duk hakan da take tunani ita kad'ae take abin ta se idan mijin na ta ya bar ta tukunna. .. A hankali take takawa sanda ta fito daga cikin gidan, tun daga nesa ta hango ta ya kuma bi ta da mayataccen kallo yana ji kamar ya k'arasa ya rungumo ta, se dae ya kama kan sa, har zuwa sanda ta k'araso, bece uffan ba se bud'e mata k'ofa da yayi babu musu ta shiga sannan ya zagaya d'aya 6arin ya shiga shima ya zauna, idanun sa gaba d'aya a kan ta ya zube su kafin tace komae yace "Wato shi ne kika 6uya a d'aki saboda kada na gan ki koh?" ya tambaya yana kafe ta da idanun sa lokaci d'aya kuma yana langa6ar da kan sa gefe kamar k'aramin yaro, se ta d'an kalle shi kana ta d'auke kae tace bayan ta d'an turo baki "Ni a'ah.." "Toh ya ne?" ba tare da bawa maganar ta sa muhimminci ba tace "Umma ce tace na tambaye ka tafiya