← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 90

Sashe 70

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nufin iyayen sa?" se ta jinjina kae gami da d'orawa da "Ehh Abba" kallan juna Abba da Umma suka yi, yayin da Yah Sadeeq dake gefe shi kuma ya kalle su, can yace "Abba ayi musu iso?" da sauri Abba ya kalle shi yana girgiza kae kafin yace "A'ah, wanene ya san da wacce suka zo? Zan je naji ko menene ya kawo shi gida na!" da sauri Umma ta mik'e tana kallan Abba tace "A'ah Abban su, ka bari koma menene su shigo d'in, se muji abinda ya kawo su" kamar ba zece komae ba se kuma ya jinjina kae yana sauke ajiyar zuciya, Umma ta kalli Yah Sadeeq tace "Fad'a musu su shigo" da "Toh" ya amsa yana ficewa daga cikin d'akin, babu wanda ya sake cewa komae bayan fitar ta sa kowa da abinda yake sak'awa. Shi kuwa Yah Sadeeq yana fita ya gan su dukan su a wajen motar, kowa da abinda yake sak'awa suma a cikin ran sa, ya kalli Ummee da Abbu ya gaeda su sannan ya k'arasa ya mik'awa Rk hannu suka gaesa kana yace "Zaku iya shigowa" jinjina kae Rk yayi yana amsawa da "Toh" Yah Sadeeq be jira wani ya sake cewa komae ba ya wuce cikin gida, yayin da Rk ya kalli Abbu yace "Abbu.." "Mu je" kawae Abbun ya fad'a cikin k'arfin hali da matuk'ar sanyin jiki, bece komae ba kawae yayi gaba, Ummee da Abbu suka rufa masa baya har zuwa cikin gidan. Sosae jikin Abbu ya sake yin sanyi tun zuwan su gidan, kawae dae ya dinga samawa kan sa k'warin gwuiwa ne dan idan ya rasa tun yanzun be kuma san da wanne ido ze kalli Abba yayi masa magana ba. Da sallama dukan su suka shigo cikin gidan, se dae gaba d'ayan su a ciki_ciki suka yi ta sakamakon yadda kowanne jikin sa ke a sanyaye. D'aga idanu Abba yayi daga inda yake tsaye ya kalli inda ya ji sallamar, inda yake da tabbacin daga nan ya jiyo sallamar, so yake ya tabbatarwa kan sa da gaske Kabeerun ne a cikin gidan sa? Da gaske Kabeerun nan ne da suka rabu tsawon shekara da shekaru? Da gaske ne Kabeerun ne ya tako yazo inda yake babu kunya babu tsoron Allah? Toh me yazo ya fad'a masa kenan? Menene zece masa wanda ze kare kan sa? Menene zeyi amfani da shi wajen goge tarin laefin sa a wajen sa? Da wane ido ze kalle shi bayan abinda ya aekata masa?. Tunanin na sa ya katse sanda suka ida shigowa cikin d'akin, dae_dae lokacin da Abbu ya d'aga idanun sa cike da kunya ya kalli cikin gidan, yayi dae_dae da lokacin da Abba ma yake kallan sa dan sake tabbatarwa da kan sa Kabeerun ne, se kuwa suka yi four eyes, jikin Abbu ya sake matuk'ar yin sanyi sanda ya lura da tabbas wannan d'in Alhaji Ibraheem Khaleel ne, Abban Sadeeq ne, Uban gidan sa a wasu shekaru can da suka shud'e, me gidan sa me son cigaban sa, wanda ya d'auki nauyin sa da na karatun d'an sa kafin yazo yayi fatali da duk wad'annan abubuwan ya watsa masa k'asa a ido, ya wofantar da komae yaci amanar sa. D'auke kae Abba yayi daga inda Abbun ke tsaye, se yake ganin kamar wancan Kabeerun yake gani a gaban sa, mutum me matuk'ar amana da kuma kirki kafin yazo yayi amfani da kirkin na sa ya da6awa Abban wuk'a a ciki.. Toh jama'a ga fa Abbu ga kuma Abba, ko ya zata kasance? Ayi hutun kwana 2 lpia, se Allah y kae mu ranar laraba. Mhiz Innocent... https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* Page 052 ___Cigaba da takawa suka yi zuwa cikin tsakar gidan, kafin suka yi cirko_cirko dukan su cikin rashin sanin abin yi. Yah Sadeeq ne ya fito daga cikin d'akin fuskar sa babu yabo babu fallasa dan tun lokacin da ya fahimci wanda suke tare da Rk Abbun sa ne y aji jikin sa yayi sanyi. "Ku k'araso" Yah Sadeeq ya fad'a yana nuna musu tabarmar dake shimfid'e a tsakar gidan. Kallan Abbu da Ummee Rk yayi ganin har lokacin babu wanda yayi ko da alamar ze zauna d'in, ya d'an lumshe idanun sa yana sake jin tausayin su cikin ran sa, cike da k'arfin hali yace "Abbu.." kafin ya kae ga k'arasawa Abbun yace, "Wuce muje" Babu musu yayi gaba ya nemi waje ya zauna, yayin da Abbu ya rufa masa baya shima ya zauna, kusan tare suka zauna da Ummee. Komawa d'aki Yah Sadeeq yayi ya kalli Abba da idanun sa ke a rufe fuskar sa a had'e babu annuri ko kad'an. Kamar ba zece komae ba se kuma yayi k'arfin halin fad'in "Abba suna jira a tsakar gida.." bud'e idanun sa Abba yayi yana jin yadda 6acin rae ke taso masa yace "Shin ni ka manta tsawon shekarun da nayi ina jiran ganin Kabeeru yazo ya k'arya ta abun da nake zargin sa da aekatawa? Ka manta kwanakin dana d'iba ina jiran sa? Se yau dan yayi zaman da be wuce na minti 1 ba shine za'a ce jira yake?" ya k'arasa maganar yana maeda duban sa kan Umma data kafe shi da idanu, tana jin babu dad'i har cikin ran ta, dan ko ba'a fad'a ba Abban fushi yake yi shiyasa yake irin wad'annan kalaman. Kafin ta k'arasa tunanin ta jiyo muryar sa yana fad'in, "Ke kika ce su shigo dama, ki tashi ki je wajen su, bana buk'atar ganin kowa a cikin su" Lumshe idanu Ayrah tayi k'irjin ta na bugawa, zata so ace komae ya gyaru a tsakanin Abbun da kuma Abba, zata so ace komae ya wuce tsakanin su a yau d'in ba se wani lokacin ba, se dae kuma tana da yak'inin tabbas hakan me yiwuwa ne, saboda yadda ta san halin Abban, da farko ze nuna fushin sa, amma daga baya komae me wucewa ne. Tashi Umma tayi daga inda take ta k'arasa wajen Abba a nutse kuma cikin kwantar da murya ta soma fad'in "Abban su kayi hak'uri don Allah, ka san me hak'uri baya ta6a fad'uwa, na san kome zaka yi kana yi ne saboda abinda yayi maka kuma dole ne ka nuna fushi akan hakan, se dae kuma tunda har shi da kan sa yazo bamu sani ba k'ilan ya gane abinda yayi ba dae_dae bane, yayi nadama shiyasa yazo neman gafara. Ina ganin saboda hakan kayi hak'uri muje se muji da wadda yazo" ta k'arashe maganar a raunane. Girgiza kae Abba yayi ba tare da ya kalli Umma ba kafin yace komae Umman ta sake tarar numfashin sa da fad'in "Don Allah Abban su, ba dan halin sa ba se don Allah da kuma sirikantakar dake tsakanin ku yanzun" ajiye numfashi Abba yayi kamin ya d'aga ido ya kalli Umma, ta ji jinjina masa kae tana lumshe idanun ta dan sake bashi k'warin gwuiwa. "Shikenan.." Abban ya fad'a. Ba Umma kad'ae ba hatta Yah Sadeeq da Ayrah da ke gefe seda ta sauke ajiyar zuciya cike da jin dad'in yadda Abban ya amince ze fita. Umma ce ta fara yin gaba sannan Abban ya rufa mata baya. Yah Sadeeq ya kalli Ayrah da ta bi su da kallo yace bayan ya mata murmushi "Mu fita koh?" girgiza kae tayi da sauri tana d'an cuno bakin ta kana tace "A'ah Yah Sadeeq, mu zauna muyi hirar mu kawae" "Hira kuma Auta?" ya fad'a yana rik'e ha6ar sa. "Ehh fa" ta bashi amsa itama, girgiza kae yayi kana yace "A'ah ina so na ga da idon ze kalli Abba ne, saboda haka bari ki ga yanda za'ayi" yayi maganar yana soma tafiya, kamar kuma wanda ya tuna wani abun se ya juyo yana kallan Ayrahn yace bayan ya bud'e baki "Aou na manta fa ashe yanzun Mahaefin mijin ki ne, Sorry Lily" ya k'arashe maganar yana murmushi. Kwa6e fuska tayi kamar zata yi kuka tace "Kae Yah Sadeeq.." yanzu kam dariya yayi sosae kafin yace "Toh shikenan, ni dae bari na fita tunda ke kunya kike ji" be jira tace komae ba ya fice daga cikin d'akin. Bin sa tayi da kallo se kawae taji murmushi ya su6uce mata, se kuma ta ja pillow ta cusa kan ta a ciki tana jin wata kunya na kama ta kamar da wani a kusa da ita. .. A hankali Umma da Abba suka nemi waje suka zauna. Ajiyar zuciya Rk ya saki kamin ya soma mik'ewa, kallan sa Abbu yayi cike da mamakin inda ze je, tun kafin yace komae Rk d'in ya fahimci abinda zece dan haka se ya d'an dakata kamin yace k'asa k'asa, "Abbu zan baku waje ne.." Tun kafin ya k'arasa Abbun ya shiga girgiza masa kae se dae ya gaza furta komae. Komawa Rk yayi ya zauna yana d'an fesar da iska daga bakin sa cikin rashin sanin abin yi, dan yau d'in haka kawae ya tsinci kan sa da mugun jin kunyar Abba, yana kuma jin kunyar yadda abubuwa zasu faru a yau d'in. An d'au wajen minti 1 bayan fitowar su Abba babu wanda yace komae, kowa da abin da yake sak'awa a cikin ran sa. Ta 6angaren Abbu kuwa ya rasa ta inda ze fara, ya rasa abinda ya kamata ya fara fad'a, ya kasa d'aga ido ya kalli Abban, ya kasa d'aga ido bare ya bud'e baki yayi wa Abban magana. A nutse Abba ya soma mik'ewa dan barin wajen, cikin sarewa da kuma sanyin jiki Abbu ya d'aga idanun sa ya kalli Abban a karo na biyu, da k'yar ya iya tattara wasu kalmomi a cikin k'wak'walwar sa sannan yace muryar sa a k'asa kamar ba Abbu ba. "Ka yiwa Allah da manzon sa ka zauna kaji abinda ke tafe da ni" shine abinda ya iya fad'a d'in dan hana Abba matsawa daga wajen. Bece komae ba ya koma ya zauna se dae har lokacin bece komae ba. Gudun kada ya kuma tafiya d'in ya sanya Abbu gyara zama sannan ya soma fad'in "Ban san da wane ido zan kalle ka na nemi yafiyar ka ba, ban san da wane baki zan yi magana na nemi yafiyar ka ba, ban san ya zan yi ba, ban san ta ina zan fara ba, hak'ik'a ni
Chapter 70 · 0% Book details