Sashe 78
Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
k'arasa titi mu samu abin hawa, babu damuwa" "Amma da ka bari na sauke ku d'in" Abbu ya sake fad'a. "Hanyar ta baud'e, kamar zamu 6ata maka lokaci idan akayi hakan, shiyasa gwara mu hau ta haya. Se da safe kenan?" Abba ya k'arasa maganar cikin sigar tambaya. "Toh Allah ya kaemu" Abbu ya fad'a ba dan ya so ba. Yana kallo Abban da Yah Sadeeq suka fice daga cikin Asibitin sannan ya sauke ajiyar zuciya ya koma ya hau motar sa shima ya bar cikin Asibitin. .. Idar da Sallahr Umma kenan ta mik'e daga kan daddumar da take kae ta k'arasa gaban gadon. Sosae ta tsaya tana kallan d'iyar ta ta da har lokacin bata farka ba, ta d'an runtse idanun ta kad'an cike da fatan ba wata matsalar bace kuma. Dae_dae lokacin Rk ya turo k'ofar d'akin, se dae sa6anin d'azu yanzu farar riga ce a jikin sa irin ta likitoci wadda ta matuk'ar yiwa k'irar jikin sa kyau. Da sallama ya shigo cikin d'akin idanun sa akan gadon, ba dan yana da tabbaci ba amma ze so ya shigo yaga Ayrahn idanun ta biyu akan gadon, ko da ze samu suyi farin ciki sosae shi da ita akan abin da Allah ya azurta su da shi. Amsa sallamar Umma tayi ya k'araso cikin d'akin, se a lokacin ya maeda duban sa kan Umman bayan ya d'an samfe daga kallan da yake mata yace "Barka da wannan lokacin Umma" "Barka dae, ya aekin?" Umma ta fad'a. "Alhamdulillah" ya bata amsa lokacin da ya dakata daga inda yake. Matsawa Umma tayi zuwa baya sannan tace tana kallan sa "Ka duba ta" tayi maganar dan ta lura da ganin ta da yayi ne ya sanya shi dakatawa. Se da ya d'an yi murmushi, dan tun da abin nan ya faru ya rasa walwalar sa hakan nan dae yake iya k'ok'arin sa wajen duba marasa lafiya amma hankalin sa na wajen Ayrah. K'arasawar yayi a nutse ya shiga duba ta. Wajen minti 1 ya sauke ajiyar zuciya sannan ya juya ya kalli Umma da duk ta k'agu taji abin da ze fad'a. "Umma In Sha Allah zata farka ina saka ran haka, bana fata ma ta wuce gobe bata farka ba dan idan hakan ta faru.." se kuma ya yamutse fuska kan sa na sara masa lokaci guda kana ya d'ora da "Zama ta farka In Sha Allah." Rauni ne sosae ya bayyana a fuskar Umman. Se ta shiga jinjina kae lokacin da ya kae k'arshen maganar sa kana tace muryar ta a sanyaye "In Sha Allah" A hankali da muryar sa data d'an shak'e yace "Bari na shiga masallaci Umma" ya fad'a dan baya tunanin a yanzu ze iya cigaba da duba wasu marasa lafiya dan dama kawae k'arfin hali ne yake yi. "Toh, Allah ya tsare" "Ameen" ya amsa da hakan yana ficewa daga d'akin. Komawa kan daddumar Umma ta sake yi ta cigaba da addu'o'i tana nemawa d'iyar ta ta sauk'i daga wajen me duka. .. Wayar sa ya d'auko daga cikin aljihun sa ya danno number Muneerah ya kira kana ya kara a kunnen sa yana cigaba da tafiya a nutse. Daga 6angaren Muneerah kuwa ko da taga kiran Rk na shigowa wayar ta a dae_dae wannan lokacin se da hantar cikin ta ta kad'a, cikin lokaci k'ank'ani taji cikin ta yayi wani mahaukacin juyawa, wanda har se da ta kae hannun ta ta dafe cikin na ta, idanun ta da suka firfito kamar zasu fad'o ta zubawa wayar. Cikin lokaci k'ank'ani zuciyar ta ta raya mata kada ta d'aga wayar, se kuma can ta sake raya mata "idan kuma tak'i d'agawa ba abin da take tunani ne ya faru ba kenan ta cigaba da zama cikin zullumi?" hakan da ta sak'a a ran ta ne ya sanya ta saurin kae hannun ta ta d'aga wayar sanda take dab da tsinkewa. "Hello Muneerah!" jin da tayi ya ambaci sunan ta ya tabbatar mata ba abin da take tunani bane, watak'ila ma Ayrahn ta mutu shine ya kira ya sanar da ita. Hakan ne ya sanya ta aro jarumta ta furta "Na'am Baby" "Kina lafiya?" ya tambaya. Hakan da taji ya tambaya ne ya sake kore mata duk wani zullumi da take ciki, se dae kuma ta k'agu taji a wane hali Ayrah take, dan daga jin yanayin maganar sa ta san ba mutuwa tayi ba. "Lafiya k'alau.. Ka ga tun d'azu na gama shiryawa inje in duba Yayar tawa, se dae dole na hak'ura saboda ban san wane asibiti kuka je ba, kuma nayi k'ok'arin kiran wayar ka amma bata shiga ba." tayi k'ok'arin fad'in hakan cikin k'arfin hali. Sam be kawo komae a ran sa ba, se yaji hakan da tayi ta burge shi hakan ne ya sanya shi fad'in, "Eyyah Sorry, kin kyauta.. Allah ya bada ladan niyya, amma zuwa yau baze yiwu ba se dae ko zuwa gobe idan Allah ya kaemu se ki duba ta." Cikin sauri ta tare shi yana k'are maganar sa, dan ita ba wannan take da buk'atar ji ba. "Ya jikin na ta? Ina fatan ta farfad'o koh?" ta tambaya k'irjin ta na bugawa, cikin kuma tsoron amsar da zata fito daga bakin sa. Ajiyar zuciya ya sauke yana d'an lumshe idanun sa sannan yace "Tukunna dae. Muna saka rae In Sha Allah." Wata k'atuwar ajiyar zuciya ta sauke wadda har seda ta sauka a cikin kunnuwan Rk. Tuna abin da tayi ne ya sanya ta saurin fad'in cike da waskewa "Toh Allah ya tashi kafad'un ta." ta fad'a ba dan tana nufin abin da ta fad'a d'in ba. Da "Ameen" ya amsa yana jin dad'in yadda Muneerahn ta nuna kulawar ta akan Ayrahn. Ko babu komae hakan ya masa dad'i dan alama zaman lafiya ze samu a tsakanin matan na sa. "Amm.. Bazan samu damar dawowa gida ba, anan zan kwana. Kiyi addu'a sosae kafin ki kwanta zuwa gobe idan Allah ya kaemu ko da safe ne se ki taho nan d'in. Muna Asibiti na ne." "Toh.. Toh Allah ya kaemu" tayi saurin fad'a. Ko da suka ajje wayar har lokacin jikin ta be dena rawa ba, yanzu idan Ayrahn ta farka ya zata yi? Idan ta farka ta tona mata asiri ya zata yi? Yau kam ta shiga uku ta lalace, anya kuwa ba zata yi wani yunk'uri akan wannan al'amarin ba? Ta d'auka ta kashe miciji ne gaba d'ayan sa, ashe bata sani ba ta kashe shi ne amma bata sare kan sa ba, ya zama dole ta samarwa kan ta mafita. Ta tsara hakan a ran ta. ... Washe_gari da safe Umma na zaune kan kujerar d'akin kamar ko da yaushe tayi shiru tana kallan Ayrah da yanzun an samu cigaba dan kuwa da kan ta take numfashi ba tare da taemakon komae ba. Turo k'ofar da akayi ne ya sanya ta d'aga kae ta kalli me shigowar. Ummee ta shigo bakin ta d'auke da sallama. Amsawa Umma tayi kana ta mik'e da murmushi kan fuskar ta tace, "Sannu da zuwa" "Yawwah sannu ka dae" Ummee ta fad'a tana k'arasowa cikin d'akin. Mik'a mata wata kujera Umma tayi, ta kar6a ta zauna akae sannan tace "An tashi lafiya? Ya me jikin?" "Jiki Alhamdulillah, dan cikin yaddar Ubangiji an samu cigaba" Umma ta fad'a. "Toh Alhamdulillah, Allah ya k'ara lafiya" "Ameen" Umma ta amsa da hakan. Daga nan suka d'an cigaba da magana jefi_jefi duk da Ummee ce ke yi duk dan ta sake wanke kan ta a wajen su Umman baki d'aya. Can bayan wasu mintuna Ummee tace "Amm Umman Sadeeq idan akwae abin da zaki yi a gida, ina ganin tun da gani na zo kije koh?" Kallan ta Umma tayi sannan ta d'auke kae tace bayan tayi murmushi "Toh kada kuma a d'ora miki nauyi" Umma ta fad'a har ran ta taji dad'i, dan ko babu komae za taso taga tsakanin Ayrah da sirikar ta akwae mutunci da sabo. Se gashi yanzu Ummeen na neman samar da hakan ta wannan hanyar. Girgiza kae Ummee tayi tace "Ahh haba haba, idan kika fad'i haka ae se naga kamar kina nufin ni ba d'iya ta bace. Ki je wallahi babu komae, idan ma zaki bari ne se gobe ki sanar min se na kwana anan d'in." Murmushi sosae Umman tayi tana mik'ewa daga kan kujerar da take tace "Toh Allah ya bada lada, bari naje na dawo zuwa anjima" "Ameen" Umma ta amsa da hakan. Umma bata k'ara mintuna da yawa ba ta bar Asibitin zuwa gida, sosae ta ji dad'in abin da Umman tayi dan haka koda ta shiga gida ta samu Abba ya gama shiryawa ze wuce Asibiti take fad'a masa abin da ya faru. Shi ma murmushin yayi kana yace "Yanzu wani abun zaki yi kenan ki koma?" jinjina kae Umma tayi kana tace "Ehh zuwa anjima kenan ba" "A'ah haba Ruk'ayya, kada ki nuna son d'iyar ki a fili mana. Tun da har ita sirikar ta ki da kan ta ta miki magana akan kwanan da zata yi, ina ganin ki bar ta yau d'aya ta kwana acan d'in, idan yaso gobe ko da Asuba kika ga damar tafiya se ki tafi." ya k'are maganar yana murmushi dan ya san shi ma ya fad'a ne kawae, amma ba zata tafi da Asuba d'in ba, dan idan akae hakan an yi ba'a yi ba kenan. Sauke ajiyar zuciya Umma tayi, dan ita sam a halin da Ayrah ke ciki bata so tayi nesa da ita ko kad'an. Amma tun da Abban ya saka baki ya sanya ta fad'in "Toh Allah ya kaemu goben" "Ameen Ameen.. Kin dawo ni kuma zan shiga na duba jikin ta." Tun kafin Umman tace komae Yah Sadeeq ya shigo cikin gidan, dan be dad'e da fita ba wani Abokin sa yazo wajen sa. "Abba, Abbun Raj ne a k'ofar gida.. Wae wajen ka yazo." Kallan Umma Abba yayi sannan ya maeda kan Yah Sadeeq "Kabeeru kuma? Ikon Allah" ya fad'a dan yayi mamakin abin da ya kawo shi yau d'in bayan jiya suka rabu a Hospital. "Yi masa iso cikin soro, mu k'arasa.." Abba ya fad'a yana soma tafiya, ganin haka ne yasa shima Yah Sadeeq d'in yin gaba. A soron gidan na su da ke