← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 90

Sashe 58

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kira uwar sa tazo taga abinda d'an nata yake aekatawa, hadda kamawa wata banza gida suna abinda suka ga dama bayan ga matar sa ta sunnah a gefe" fuzge hannun ta Muneerah tayi dan tana ganin idan ta k'yale Ayrahn bata ta6a lafiyar jikin ta ba ta fad'i k'asa warwass, mutuncin ta ya gama zubewa a idon wannan yarinyar "Aunty babu ruwan ki a wannan maganar, ki rabu dani in nuna mata banbancin dake tsakani na da ita a matsayin ta na matar dadiro, Aunty idan ban ta6a lafiyar jikin ta ba hankali na baze ta6a kwanciya ba, so nake ta tabbatar ta kuma gane nima na k'ware a tashanci.." ita dae Ayrah yi tayi kamar ma bata san abinda suke cewa ba, ta bar su su gama haushin nasu idan sun gaji suyi gaba, tayi tsaye hannayen ta hard'e a k'irjin ta tana jira taga abinda zasu yi next bayan sun gama haushin, a nutse ta sake maeda duban ta kan Bahijja da itama ta saci kallan ta, wata uwar harara Bahijjan ta jefa mata tana janye idanun ta, mamaki ya sake kashe Ayrah, bata san su d'in su waye ba, amma kuma Bahijjan tafi bata mamaki, "ko dae matar sa ce?" ta tambayi kan ta a cikin zuciyar ta, anya kuwa matar sa zata kasance mahaukaciya kamar wannan? Wadda take k'ok'arin nuna mata tayi karuwanci a da? Anya kuwa? Seta girgiza kae a fili kamar wadda ke magana da wata. "Ke baki da hankali? So kike ki nunawa kowa wacece ke? Lallae yau na sake tabbatar da ke d'in wawiya ce kuma shashasha" Aunty Zeenah ta fad'a ran ta a 6ace, se a lokacin kuma jikin ta yayi sanyi tace "Toh Aunty ya zanyi? So take ta nuna min duniyanci bana so kuma ta ci ni wasa shiyasa nake k'ok'arin nuna mata wacece ni nima" "Toh wannan ba dabara bace, d'auki waya ki kira uwar sa" maraeraece fuska tayi kana tace "Aunty don Allah ki bar komae a hannu na zan magance kowacce matsala ce da kae na, naga tana fama da rashin kunya shiyasa nake so na koya mata hankali, Aunty ki bari muci uwar ta sannan mu tafi mu bar ta tunda bata san mu d'in su waye ba, idan hakan ta faru nasan zata fita a rayuwar sa" tsaki Aunty Zeenah ta ja har yanzu Muneerahn bata da hankali, seta sakko da jakar ta sannan ta d'auko wayar Muneerahn ta mik'a mata "Maza kira Babar sa ki bani" ba dan taso ba haka ta kar6i wayar bayan ta d'aga ido ta watsawa Ayrah hararar da ta kasa denawa kamar idanun ta zasu tsinko, ta danna kiran sannan ta mik'awa Aunty Zeenah tana ji kamar kafin Auntyn ta gama waya ta k'arasa ta yiwa Ayrah shegen dukan da ze illa ta ta har ta kae ga tayi jinya, da da yadda za tayi ma har kyawun nan nata ma se ta san yadda za tayi ta illa tashi ko yaya ne yadda ba zata sake birge wani d'a namiji ba dan kuwa ta san wannan kyawun shi ne ya rud'i Rk, bata sake jin wani bak'in cikin se ta tuna yadda Rk d'in ya kasa had'a jiki da ita ashe akwae wadda yake da ita a ajje a gefe, dan wani k'arfin hali ma hadda kama mata gida, se kawae taji wani kuka ya taho mata me cike da takaeci, 6acin rae gami da zafin zuciya. Bata san me Aunty Zeenah suka tattauna da Ummeen Rk ba dan gaba d'aya hankalin ta baya wajen, gefe d'aya kuma hankalin ta yafi ta'allak'a ne ga Rk d'in shi kan sa, bata ta6a tunanin haka yake ba, bata ta6a tunanin ze iya ajjiye mace a wani gida ba wadda ba matar sa ba. "Mun ci sa'a unguwa ma za taje, da har tace seta fara zuwa unguwar na sake tunzura ta yanzu zata taho nan d'in, na tura mata address, gwara tazo ayi komae a gaban ta a wuce wajen" daga nan Muneerah bata sake cewa komae ba itama kuma Auntyn bata sake cewa komae ba, suka cigaba da tsayuwa a wajen suna jiran zuwan Ummee, ita kam Ayrah neman waje tayi ta zauna fuskar ta a had'e kamar d'azun, se dae yanzun har tafi fusata musamman yadda taga sun sake neman waje sun tsaya alamar basu da niyyar tafiya kenan.. Bayan wajen minti 10 aka turo k'ofar gidan, dukkan su suka d'aga idanu suka kalli me shigowar, Ummee ce sanye cikin shadda da mayafi babba da kuma jaka sak'ale a kafad'ar ta, gaba d'aya zuciyar ta ta kasa sukuni tunda Aunty Zeenah ta mata wannan wayar, sam bata lura da Ayrah ba hankalin ta gaba d'aya yana kan Muneerah ne, ta k'arasa jikin ta a sanyaye tace "Muneerah meya faru?" kuka Muneerah ta fashe dashi sanda tazo dab da Ummeen, Ummee ta rungume ta tana sake jin yadda jikin ta ya k'ara yin sanyi "Ummee Yaya ne ya kamawa wata yarinya gida tana zaune a ciki, shima kuma yake rayuwa da ita kamar matar sa, ga wannan nan sheda ce Ummee na shiga 3" ta k'arasa maganar cikin kuka tana me nuna Bahijja, kasa furta komae Ummee tayi saboda yadda ta sake jin abin wani banbarakwae, amma dan ta sake tabbatarwa se cewa tayi "Kin tabbatar Muneerah? Wacece yarinyar kuma ina take?" "Ga tsinanniyar can Ummee" Muneerah ta fad'a bayan ta tashi daga jikin Ummeen tana nuna Ayrah da har lokacin tak'i kallan su dan bata san kuma wa suka sake d'akkowa ba, k'ank'ance idanun ta Ummee tayi tana kallan Ayrahn sosae, kamar ta ta6a ganin fuskar, hakan ne ya sanya ta cigaba da kallan ta dan son tuna inda ta san fuskar, se dae sam ta kasa tunawa, ita kan ta Ummeen sheda ce akan d'an ta, ko da wasu za suce yana neman mata ba zata yarda ba, se dae gashi matar sa da kan ta ta gano hakan, gasu kuma a cikin gidan daya ajje wata yarinya yake kuma zuwa cikin gidan "Inna lillahi wa inna ilaehi rajiun" Ummee ta furta a fili tana runtse idanun ta cike da 6acin rae da kuma takaeci. "Kee!!" shine abinda Ummee ta fad'a tana kallan Ayrah, yadda Ummeen tayi magana ne ya sanya ta saurin d'aga kan ta ta kalli Ummeen, se dae ta kasa furta komae se cigaba da kallan Ummeen tayi wadda ta mata wani irin kwarjini, haka kawae taga kamar fuskar Rk take gani a gaban ta, kafin ta k'arasa tunanin ta jiyo muryar Ummee tana fad'in "Waye ya kawo ki cikin gidan nan? Zaman wa kike yi?" Ummee ta fad'a ran ta a matuk'ar 6ace, gaba d'aya tambayar ce tazo mata a bazata haka kawae ta rasa abinda za tace ta kuma kasa tankawa matar da take tambayar ta "Zo ki fice daga gidan nan kafin na saka hannu na a jikin ki, duk tarbiyyar dana yiwa d'a na ashe ke kina daga gefe kina warware ta? Zo ki fice shashasha mara tarbiyya, watsatstsiya" zafin kalaman da Ummeen ta fad'a mata ne ya sanya ta runtse idanun ta tana jin yadda zuciyar ta tayi wani irin rauni, kafin ta bawa hawayen da suka taru cikin idanun ta damar zuba ta sake jiyo muryar Ummeen na fad'in "Zaki fice ne ko kuma na kira k'attan samari su fitar min da ke?" "Ummee ae dama ita haka zata so ki had'a ta da wasu mazan tunda aekin ta kenan, gwara ki bari ni nan zan iya fitar miki da ita" Muneerah ta bawa Ummee amsa tana ji kamar ta janyo Ayrahn kafin kowa ya bata umarni ta nad'a mata na jaki. Mik'ewa ta soma yi a hankali kamar zata shige d'akin dan d'aukar wayar ta kota samu ta kira Rk d'in kada yazo yaga bata nan seta sake jiyo muryar Ummee wadda yanzu ta gama tabbatar da cewa mahaefiyar Rk ce "Kee!!" kafi Ummeen ta d'ora da komae Muneerah ta kar6e maganar sa fad'in "Gidan uwar wa zaki je? Uban me zaki koma kiyi a ciki? Zo ki wuce a hanya kya had'u da wanda ze taemaka miki ya baki wajen kwana kamar yadda kike buk'ata" Muneerah ta fad'a bayan tayi gaba kamar zata rik'o Ayrah, ba dan tunda Ummeen ta shigo ta cika mata ido ba babu abinda ze hana ta d'aga ido ta fad'a mata zazzafar maganar da zata dad'e bata manta da ita ba, se dae ta soma takawa a hankali cikin harabar gidan zuwa bakin gate. ... A karo na barkatae ya sake kiran layin na ta se dae yanzun ma bata d'aga ba, haka kawae yaji hankalin sa yak'i kwanciya, dan ya saba ba kasafae yake kiran ta babu amsa ba, se dae yau d'in ya kira ta har ya manta sau nawa amma bata d'aga ba, takaddun daya shigo dasu kawae ya ajiye akan gadon d'akin, sannan ya zura wayar cikin aljihu kana ya fito daga d'akin, yana dab da wuce part d'in ta ya d'an dakata, kamar idan ya mata haka be kyauta ba, idan ya fita ba tare daya sanar da ita ba kamar be kyauta ba tunda dae ko babu komae yau d'in kwanan ta ne, tuna hakan ne ya sanya shi durfafar part d'in na ta cikin takun nan na sa, a nutse ya saka kan sa cikin parlourn yayi tunanin ze sake samun su kamar yadda ya bar su se dae ga mamakin sa babu kowa cikin parlourn shiru kamar ma babu mutane cikin kowanne d'aki, cigaba da takawa yayi zuwa cikin d'akin nata ya saka hannu ya tura k'ofar nan ma dae babu kowa, ta6e baki yayi gami da d'aga kafad'a ya soma takawa ya fito daga cikin parlourn zuwa harabar gidan, da mamaki yake cigaba da kallan parking space d'in, kamar d'azu daya shigo yaga motar Muneerah ajje a wajen, se dae yanzu babu ita a wajen, kenan hakan na nufin fita tayi daga cikin gidan ba tare da ta sanar da shi? Ya zama dole ya nuna mata shi ba lusarin namiji bane da zata d'auki jiki haka kawae ta fice daga gidan ba tare da izinin sa ba, kae tsaye motar sa ya hau ya tashe ta ya fice daga gidan bayan ya kulle gate d'in, ze nuna mata iyakar ta
Chapter 58 · 0% Book details