← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 90

Sashe 56

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta sake bud'ewa, still dae shi d'in ta sake gani, girgiza kae ta shiga yi k'irjin ta na bugawa, ga kuma kan ta da ya sake kullewa, bata ankara ba se fitar sa data gani, wanda tunda tayi ido biyu da shi bata sake fahimtar komae ba, bata sake sanin abinda suke tattaunawa ba, kallan ta ta maeda kan Muneerah da ta bi Rk da kallan k'auna, bata san sanda bakin ta ya furta cikin tsananin kullewar kae "Muneerah wane ne wannan?" da mamaki Muneerah ta kalli Bahijja tana jin tambayar ta ta kamar ta raenin hankali "Kamar yaya?" "Ehh don Allah" ta fad'a "Wane ne ze shigo min har cikin d'aki na idan ba miji na ba?" Muneerah ta fad'a a d'an fusace "Mijin ki kuma?" ta fad'a a raunane kuma cike da tashin hankali, dan a yanzu tama manta da k'aunar sa da take, gaba d'aya hankalin ta ya tafi ne akan ganin sa da tayi acan a matsayin mijin Ayrah, yanzu kuma gashi anan Muneerah na fad'a mata mijin ta ne, me yake faruwa kenan? Mhiz Innocent... https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* Page 044 ___Komawa tayi ta zube kan kujera tayi zaman da6aro cikin rashin sanin abin yi, hannun ta ta d'auka ta d'ora a kan ta tana jin gaba d'aya komae ya cukurkud'e mata, gaba d'aya kan ta ya kulle, k'wak'walwar ta ta rikice, kamar ma tunanin ta na so ya kwance, ta rasa tunanin abinda ya kamata tayi, dan taga alama gaba d'aya mutanen nan so suke su haukata ta. "Anya kuwa ban haukace ba?" ta tambayi kan ta cikin sarewa da abubuwan da suke faruwa kusufa_kusufa. "Meyasa kika tambaya?" tambayar da Aunty Zeenah tayi itace ta soma dawo da ita hankalin ta, ta kalli Aunty Zeenah tana ji kamar ta saka ihu ko da zata ji sassaucin abinda take ji cikin zuciyar ta, se a lokacin ta iya bud'e bakin ta sannan ta fara magana "Ita tace min mijin ta ne Aunty, itama Ayrah tace min mijin ta ne, so kuke ku haukata ni ne ko menene?" tayi maganar a gajiye kamar wadda tayi aekin wahala, wani banzan kallo Muneerah ke bin ta da shi tun sanda ta ambaci sunan wata matar take had'a sunan kuma da na Rk, seda ta k'araso kusa da Bahijjan tana ji kamar ta shak'o wuyan ta sannan tace cikin d'aga murya "Kar ki k'ara Bahijja, ina ganin mutuncin ki, kada ki bari ya tsiyaye a cikin ido na har ta kae ga na rufe ido na na nuna miki wacece ni, miji na ni kad'ae ce matar sa, idan ma k'yasawa kika yi toh wallahi ahir d'in ki dan kuwa baki ishe shi kallo ba, ni kad'ae ce matar sa ta har abada" ta k'arasa maganar tana fidda huci saboda tuk'uk'in da take ji a cikin zuciyar ta, tana k'ok'arin juyawa ta bar wa Bahijja wajen ta sake jiyo muryar ta "Kina nufin ki ce min baki san da zaman wata ba bayan ke? Ko kuwa me kike so ki ce? Toh wallahi tallahi mijin ki na zaune da wata matar a wani gidan, abinda ban sani ba dae shine matar sa ce ko akasin hakan, amma abinda na sani a gaba na ya rungume ta kuma ita da kan ta ta fad'a min cewa mijin ta ne wanda hakan ne yasa nima nake sanar dake abinda na sani" wata muguwar shak'a Muneerah ta yiwa Bahijja lokaci d'aya tana laelayo wani uban ashar ta maka mata sannan ta cigaba da fad'in lokacin da idanun ta suka yo waje suka kuma yi ja kamar an watsa musu garwashi "Uban ki ne ya d'aura masa aure da wata? Ashe dama da wata manufar kika biyo Aunty, toh wallahi ki tattara ya naki ya naki ki bar min gida munafuka algunguma" "Sake ta mana Muneerah" Aunty Zeenah ta fad'a cikin d'aga murya ran ta a matuk'ar 6ace, ta san halin er ta ta in dae akan abinda take so ne, amma ba tayi tunanin soyayyar ta sa zata rufe mata idanu har ta kasa gano tsantsar gaskiyar dake tattare da Bahijja ba. Tsawar da Aunty Zeenahn tayi mata itace ta sanya ta sakin rigar Bahijja da ta cukwikuye a hannun ta, Aunty Zeenah ta jata gefe sannan tace ran ta a d'an 6ace "Ke wae yaushe zaki girma ne Muneerah? A yanda take maganar nan me ya kamata ki yi? Tsayawa zamu yi mu bi komae a sannu, aka fad'a miki yanzu ana wani yadda da d'a namiji ne, musamman ma kamar wannan mijin naki ke kan ki kin san dole ne mata suyi ta kawo masa hari" seda ta dinga sauke numfashi a jere a jere kamar wadda tayi tsere ko kuma wani aekin wahala sannan ta samu 6acin ran da take ji ya d'an ragu kana suka taka zuwa inda Bahijja ke zaune har lokacin kamar wadda aka dasa. Zama Aunty Zeenah tayi kusa da Bahijja cikin kwantar da murya tace bayan ta dafa kafad'ar ta "Ki tsaya ki min bayanin abinda ke faruwa Bahijja, Me kike k'ok'arin cewa?" runtse idanun ta Bahijja tayi duk da yadda ran ta ya 6aci akan Muneerahn amma albarkacin Auntyn ya sanya ta fara fad'in "Aunty gidan k'awa ta da naje jiya anan na ga Doctor, ba yau na fara sanin sa ba saboda ya koyar damu a A.B.U ballantana nace ko me kama da shi ne, wallahi Aunty shi ne na gani a gidan jiyan kuma yau gashi na gan sa anan, ni abinda na kasa fahimta idan da gaske kishiyar ta ce ya akae ba ta san da zaman ta ba?" "Tirk'ashi" Aunty Zeenah ta fad'a tana jinjina kae lokaci d'aya kuma tana maeda duban ta kan Muneerah da ta zube akan k'afafun ta ta saka wata k'ara tana d'ora hannun ta a kan ta "Na shiga 3 ni ennan" ta k'are maganar tana fashewa da kuka, kafin Auntyn tace komae se kuma ta mik'e kamar wadda aka tsikara ta wuce d'akin ta buguzum buguzum, can se gata ta fito d'auke da wani yalolon mayafi "Tashi ki kae ni gidan, yau sena nunawa ko wacece ke k'ok'arin bin miji na ita er iskar k'arya ce wallahi, ki tashi ki kae ni" tayi maganar tana kallan Bahijja zuciyar ta na cigaba da tafasa, rik'o hannun ta Aunty Zeenah tayi "Ki tsaya tukunnah.." kafin ma Auntyn ta k'arasa fad'in abinda tayi niyya ta fuzge hannun ta sannan tace cikin d'aga murya "Wallahi ban ga uban da ya isa ya hana ni zuwa gidan in ci mata uwa da uba ba, miji na zata dinga bibiya? Na san halin miji na baya bin mata dole wani abun ta masa, toh wallahi yau sena nuna mata nima er kwalta ce" kallan ta Aunty Zeenah tayi ta girgiza kae kana tace "Jira ni muje.." ta fad'a tana yin gaba, gwara ta bi Muneerahn kome za tayi tayi shi a gaban ta dan ta san halin Muneerahn, idan ran ta yana a 6ace babu abinda ba zata iya ba. Ba dan ta so ba haka ta tsaya a bakin k'ofar tana cigaba da fidda huci kamar mayunwaciyar zakanya, ita kad'ae ta san yadda za tayi da matar, dan wallahi seta kusa kashe ta. Babu dad'ewa Auntyn ta fito sanye da Mayafi ba wani babba ba, dan ita d'in ma babu laefi ba duniya ce, ta jefawa Bahijja nata mayafin kana tace "Ku wuce muje" Tare suka fito Compound d'in gidan, Muneerah ta kasa furta komae saboda yanda zuciyar ta ke tafasa, suna dab da shiga motar Muneerah Aunty Zeenah tace "Ba zaki tambayi mijin naki ba?" "Dallah k'yale shi, hankali na gaba d'aya yayi gaba bani da wannan lokacin" ta fad'a a fusace tana shigewa cikin motar tama manta dawa take magana, itama Auntyn bata matsa ba dan sau da dama itama ta kan fice daga gidan ta ba tare da ta sanarwa da mijin ta ba. .... A d'aya 6angaren kuwa tana zaune kan gadon ta tayi shiru kamar me nazarin wani abu, tunda ya fita ya bar ta take zaune a wajen ta kasa motsawa ko da nan da can ne, ita kad'ae ta san rauni da kuma wani zafi da take ji a cikin zuciyar ta. Wayar ta ce ta soma ringing, kasancewar tana kusa da wayar ya sanya ta kallan ta da narkakkun idanun ta, bata san sanda murmushi ya su6uce mata ba, tayi saurin saka hannu ta d'aga wayar tana karawa a kunnen ta. "Hello Yah Sadeeq" shine abinda ta furta cike da farin cikin ganin kiran nasa "Na'am Auta, ya kike? Ya gidan?" "Alhamdulillah" "Madallah, Albishirin ki?" ya tambaya yana murmushi, cike da zumud'i tace "Goro" seda ya d'an yi jimm kad'an kafin yace "Gani a k'ofar gidan ki.." wani irin farin ciki ne ya ratsa kafatanin jikin ta, har bata san sanda ta mik'e tsaye ba sannan cikin farin cikin dae ta furta "Don Allah da gaske Yah Sadeeq?" kamar tana gaban sa ya jinjina kae yana murmushi "Ki fito ki tabbatar.." bata sake cewa komae ba ko kuma ta jira ya sake fad'in komae ba ta fita da gudu daga bedroom d'in zuwa harabar gidan, hannun ta har rawa yake dan farin ciki ta saka hannu ta bud'e k'ofar, seda ya saki murmushi sannan ya sako k'afar sa zuwa cikin gidan, cike da farin ciki da kuma kewar d'an uwan na ta ta fad'a jikin sa tana fashewa da kuka, shima rungume ta yayi se dae sa6anin ita shi murmushi yake yi "Auta rigima dae.." se a lokacin ta d'ago itama tana murmushin me had'e da kuka wanda hakan ze alamta maka cewa kukan na farin ciki ne "Nayi kewar ka sosae Yah Sadeeq d'i na" dariya sosae yayi kana yace "Nima haka Lily" ya fad'a yana maeda duban sa cikin gidan, seya shiga jinjina kae kafin ya juyo ya kalli Ayrah "Wae yanzu nan gidan Auta ne? Lallae Ayrah ta girma" "Kae Yah Sadeeq" ta fad'a tana rufe fuskar ta, murmushi yayi kana ta kama hannun sa zuwa cikin gidan, nan ma seda ya kalli parlourn sosae ya kuma yaba da tsarin sa sannan ya zauna, nan take ta fara ajiye masa abin sha ne, na ci ne da duk abinda ta san tana da shi
Chapter 56 · 0% Book details