Sashe 76
Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kana tace "Uhmm" daga haka bata sake cewa komae ba, dan haka kawae take jin ta a takure, ta k'agu ma ta koma kawae dae dan kada ta gwasale ta ne duk da ta dad'e da fahimtar komae Muneerahn ke yi kawae tana yin sa ne ba har cikin ran ta ba, amma bata nuna ba suka cigaba da takawa. Bud'e idanu Muneerah tayi sanda ta hangi madaedaecin Swimming pool dake ke6ance a gefe guda wato idan aka zagaya bayan gidan, ta lumshe idanun ta tana jin wani irin farin ciki mara misaltuwa, lallae Allah na son ta, tun a rana ta farko har ta samo mafita, hakan da ta raya a zuciyar ta ne ya sanya ta sake sakin murmushi, dae_dae lokacin da suka iso wajen, "Wow, mu d'an lek'a koh? Ina so na ga yanayin zurfin sa ne ko da na tashi shiga" Muneerah ta fad'a tana k'arasawa bakin wajen, ta d'auka itama Ayrah zata biyo ta ne amma se ta ji tace "Haka ne" ta fad'a kawae fuskar ta babu yabo ba fallasa tana kuma dakatawa a inda take, se da ta lek'a sannan ta juyo ta kalli Ayrah tace "Ki k'araso ki gani mana, se kin lek'a zaki gane yanda yake gwanin birgewa" kallan ta kawae Ayrah tayi dan wannan abin da Muneerahn ke yi sam ba birge ta yake ba hasalima ya ginshe ta, da zata gane da ta hak'ura. Zuwa lokacin Muneerah ta fusata da yadda take ta yiwa Ayrahn magana tana share ta, hakan ne yasa tayi shiru kawae ta baro wajen zuwa gefen Ayrah fuskar ta a had'e kamar ba Muneerahn d'azu ba dake ta Pretending, d'auka da Ayrah tayi cigaba da tafiya zasu yi shine ya sanya ta soma takawa hakan ya bata kusanci da swimming pool d'in, hakan ne ya bawa Muneerah damar sanya hannun ta ta tunkud'a Ayrah inda take da tabbacin daga yau ta ta ta k'are. Ayrah bata ankara ba se ji tayi an jefar da ita gefe, tana shirin jin ta a k'asa se ta tsinci kan ta dumu_dumu cikin swimming pool babu zato babu tsammani, rashin iya ruwan ne ya sanya ta soma k'ok'arin k'watar kan ta daga cikin wannan ruwan, se dae ta kasa aekata komae sanadiyar ruwan da ya soma shige mata cikin baki, hanci har ma da idanun ta, cikin k'ank'anin lokaci ta soma kokawa da numfashin ta da take da tabbacin yana dab da barin gangar jikin ta, se dae ina ko kad'an ta kasa, se cigaba da tayi da motsi a cikin ruwan cike da fatan ta bud'e idanun ta ta gan ta a waje, ko kuma ta bud'e idanun ta ta ga cikin mafarki ne. K'arar fad'awar Ayrah cikin ruwan ne ya sanya Muneerah sakin murmushi cike da jin dad'in yadda komae yazo mata cikin sauk'i, yanzu ya ragewa Rk ya je ya nemi matar sa idan ya dawo, ita kuma yanzu haka d'akin ta zata koma ta cigaba da farin ciki ta kuma kira Mummyn ta ta sanar da ita yanda tayi maganin Ayrahn cikin k'ank'anin lokaci. Hannun ta ta dinga karkad'ewa kamar wadda ta ida tankad'e garin masara, duk da yadda take hango Ayrahn na mutsu_mutsu cikin ruwan hakan be hana ta sakin wata dariya ba kana ta juya dan barin wajen cike da jin dad'i, se dae me? Tana juyawa yayi dae_dae lokacin da Rk ya k'araso wajen kamar a d'an dame, rikicewa gami da rud'ewa da kuma tsoro suka kamata bata san sanda ta dakata a wajen da take ba ilahirin jikin ta na d'aukar rawa kamar gangar da ake kad'awa, ganin ta da yayi ya sanya shi fad'in "K'arar me na ji haka?" Bata san sanda ta fashe da kuka ba kawae jikin ta na cigaba da d'aukar rawa da k'yar ta iya bud'e baki tace "Ayrah ce ta fad'a cikin ruwa, babu yadda ban yi da ita ba kada ta shiga ruwan nan tace min ae ta iya, ta saba shiga, duk da yadda na hana ta amma bata hanu ba se ganin ta nayi kawae a ciki, yanzu ma haka juyowar da nayi zuwa zan yi na kira mak'ota azo a fito da ita tunda baka nan.." Sam be ma san abin da ta cigaba da fad'a ba tun da ta ambaci sunan Ayrah, kawae dae ya tsince shi a bakin Swimming d'in, da yanzu haka babu ko da motsi ne wanda ze nuna maka akwae alamar abu me rae a cikin ruwan, cikin sakannin da basu wuce 2 ba ya fad'a cikin ruwan cike da k'warewa k'irjin sa na wani irin bugawa, irin bugun da tun da yake ze iya cewa be ta6a jin kamar sa ba. A can gefe ya samo ta, cikin sauri ya k'arasa ya janyo ta yana k'arya ta kan sa na yadda ya ji jikin ta ya saki, cikin sauri ya fito da ita daga cikin ruwan sanda bugun zuciyar sa ya k'aru, jikin sa ya d'auki rawa, kawae se ya shimfid'e ta a wajen, ta kuwa zube idanun ta a lumshe babu ko numfashi kad'an ne a jikin ta, cikin sauri ya kae bakin sa kan na ta ya soma zuk'o ruwan da ta sha na tsawon sakanni, sannan ya saki bakin na ta ya zubar da ruwan a gefen sa kana ya dawo da duban sa kan ta inda take kwance babu alamar rae a tattare da ita. K'irjin sa ya buga sanda ya sake kallan na ta har kuma lokacin jikin sa rawa yake yi kamar mara gaskiya, yana shirin saka hannu ya d'aga ta idanun sa ya sauka akan farar k'afar ta da rigar jikin ta ta yaye, ya d'an runtse idanun sa dan sake gasgata abin da idanun na sa ke gani, wanda hakan ya tabbatar masa da lallae abin da idanun sa ke gani d'in ba gizo bane, jini ne ke sakkowa zuwa kan k'afar ta ta yana sauka a k'asa, cikin wani irin yanayi na kid'ima, rud'ewa gami da gigicewa ya saka hannun sa ya d'auke ta gaba d'ayan ta ya sa6a ta a kafad'ar sa sannan ya soma takawa yana barin wajen, duk wani taku da zeyi haka gudun zuciyar sa ke k'aruwa, fargabar sa ke dad'uwa haka kuma tsoro ke shigar sa.. Mhiz Innocent... https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* Page 055 __Shimfid'e ta yayi a bayan motar har lokacin bugun numfashin sa be koma dae_dae ba. Da sauri ya zagaya ya koma driver seat ya figi motar da gudun gaske, cikin zuciyar sa yana karanto duk wata addu'a da ta zo cikin ran sa. .. A 6angaren Muneerah kuwa komawa tayi tayi zaman da6aro a tsakiyar d'akin sanda taji ficewar sa daga cikin gidan. Kuka ta cigaba da yi cikin rashin sanin abin yi, ga shi kuma har lokacin jikin ta be dena rawa ba kamar wadda ke jin sanyi na musamman. Gaba d'aya ta rasa abin da zata yi, ita dae ta san burin ta be wuce kada Ayrah ta farka ba, dan idan kuwa ta farka ta san babu abin da ze hana ta fad'in gaskiyar abin da ya faru, idan hakan ya faru kenan me ze biyo baya?. Se ta sake fashewa da kuka tana d'ora hannun ta aka lokaci d'aya tana fad'in, "Na shiga 3 ni en nan, meyasa nayi gaggawa?" ta tambayi kan ta kamar akwae wanda ze bata amsa. Ta kae wajen minti 1 tana cigaba da kukan se can ta jiyo ringing d'in wayar ta dake kan kujerar da take kusa da ita, duk da taji ringing d'in hakan be sanya ta d'auka ba ta share tana cigaba da kukan ta cike da fatan Ayrahn kada ta farka. A karo na barkatae aka sake kiran wayar ta ta, se ta janyo ta da sauri kamar zata rufe ta da duka dan kashe ta gaba d'aya ta huta da wannan kiran da yake shigowa, se kawae ta ga kiran Mummyn ta, cikin lokaci k'ank'ani jikin ta ya sake yin wani rauni wani sabon kukan ya taho mata se ta d'aga da sauri tana karawa a kunnen ta, tun kafin Mummyn tace komae ta soma fad'i cikin kuka kamar ran ta ze fita. "Mummy na shiga 3 na 6ata komae, na 6ata komae Mummy" Cikin mamakin maganar ta ta Mummy tace "Bangane ba? Me kika 6ata? Me kuma ya same ki kike kuka?" ta fad'a daga inda take tana mik'ewa tsaye. A hankali Muneerah ta shiga labartawa Mummyn abin da ya faru tun daga farko har k'arshe. "Inna lillahi wa inna ilaehi rajiun" Mummy ta fad'a cikin matuk'ar tashin hankali, sannan ta d'ora da "Ashe baki da hankali Muneerah, yanzu duk irin zaunar da ke da nayi na fad'a miki yanda zaki yi, a haka kamar kin d'auka ashe duk a banza nayi komae? Yanzu da kika jefa ta cikin ruwa idan kuma ta farka ta fad'i wacece ta jefa ta fa?" se da tayi sheshshek'a sannan tace "Abin da ya hana ni sukuni kenan Mummy, ina cikin bala'i, ya zanyi ni kam?" ta k'are tana kuka. Shiru Mummy tayi na en wasu sakanni kamin can tace "Kin ga alamar akwae rae a tattare da ita?" da sauri ta girgiza kae kamar tana gaban Mummyn sannan tace "A'ah ban gani ba, amma haka kawae tsoro nake ji" sauke ajiyar zuciya Mummy tayi, dan ita dae da asirin d'iyar ta ya tonu gwara ko me za'ayi ayi shi. "In Sha Allah ma ba zata farka ba, Allah ya ji k'an ta.. Amma duk da haka ki sani kin bani haushi, kuma daga yau ina ga bazan sake baki shawara ba" Mummy ta fad'a. Kalaman Mummyn sun matuk'ar sanyayar da zuciyar Muneerah har seda ta d'an murmusa kad'an sannan tace "Kiyi hak'uri Mummy, na kasa hak'uri ne" "Yanzu dae ki ajje waya ki kwanta ki huta, zuwa anjima zan kira ki" da "Toh" ta amsa sannan ta ajje wayar tana komawa ta kwantar da kan ta akan kujerar dake kusa da ita. .. Ta 6angaren Rk kuwa kae tsaye asibitin sa ya wuce da ita, cikin sauri yayi parking motar sa, ya fito still dae cikin saurin ya sa6ata a kafad'ar sa yayi cikin asibitin da ita. Kae tsaye emergency room ya wuce da ita dan bata taemakon gaggawa, a lokacin be