← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 90

Sashe 24

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sam tak'i dannuwa, ga dae ta ta kawo amma kwata kwata tak'i dannuwa "Kashhh! Shegiyar waya seda ta kwafsa min wallahi" ta fad'a tana dafe kan ta, Bahijja ce ta d'auki wayar itama ta ta6a, ganin da tayi babu abinda ke motsi a wayar ya sanya ta fad'in "Kinga fad'a mana da baki kawae pls" Khadeejah da ta gama k'uluwa dan takaeci da haushi tace bayan ta ja k'aramin tsaki sannan ta maeda duban ta kan su Bahijja "Doctor Rk" sunan sa suka ji ta ambata ne ya sanya dukan su kallan ta, Abeeda ta d'ago ba tare da ta kalli Khadeejah ba tace, dan gaba d'aya ita kan ta seda taji ta muzanta da abinda wayar ta mata bayan cika bakin da ta gama yi "Ina Ayrah ta cikin d'akin kun nan? Toh soyayya suke da Doctor.." dukan su suka cigaba da kallan ta kowannen su na ganin kamar zarewa tayi yasa take wannan maganar, Jidda tayi k'arfin halin fad'in "Wait mana hajiya! Wane Doctorn kike magana kuma wace Ayrahn kike magana akae?" tayi maganar cikin tsare ta da idanu, murmushi Abeeda ta saki sannan tace "Dama nasan ba yadda za kuyi ba shiyasa na d'auko muku hoto, amma kada ku damu zan kae a duba min wayar, idan ta gyaru zan dawo na nuna muku hoton dana d'auka na shi shi da ita yau da suka fita.." daga haka ta mik'e ta fice Khadeejah tabi bayan ta, kusan a tare suka bita da kallo kamar wasu dolaye, ta bar su da tunani kala kala, sun kae wajen minti 1 a hakan sannan Bahijja tayi k'arfin halin fad'in bayan ta kalle su "Kada fa ace da gaske Abeeda take" wani murmushi Ruks tayi sannan tace "Haba Bahijja kada ki zama shashasha mana, Doctor Rk fa take magana wae yana soyayya da wannan yarinyar? Dududu ma nawa take?" shiru Bahijja tayi na d'an wani lokaci kafin can tace "Ke wallahi ba tun yau nake zargin yarinyar nan ba, dama na dad'e ina tsoron kada kyawun ta ya rinjaye shi mu shiga 3" se a lokacin Jidda tace "Hmmm, kuna tunanin kyawu ze rud'i kyakykyawa ne? Bana tunanin haka gaskiya" tayi maganar tana d'an k'ank'ance idanun ta kamar me tunani "Toh koma dae menene akwae wata a k'asa" Bahijja ta fad'a, kafin wata a cikin su tace komae sallamar Ayrah ta ratso cikin d'akin, babu wanda ya iya amsa mata se bin ta da suka yi da kallo dukan su, kallo irin na tuhuma, ganin irin kallan da suke mata ne ya sanya ta sake had'e kyakykyawar fuskar ta ta k'araso cikin d'akin "Daga ina kike?" Bahijja tayi k'arfin halin fad'in hakan, kallan ta Ayrah tayi da mamakin jin furucin ta, kafin Bahijja ta gama fahimtar irin kallan da Ayrahn ke mata ta jiyo k'aramar muryar ta tana fad'in "Toh ina ruwan ki?" ta fad'a tana hararar gefe gami da murgud'a baki sannan tayi wucewar ta kan gadon ta, dukan su suka bita da kallo kafin Ruks ta jinjina kae tana ta6e baki cike da mamakin halin Ayrahn "Cha66 d'i jam!" Jidda ta fad'a tana cigaba da kallan Ayrah. Ta 6angaren Ayrah kuwa ba ta bi ta kan kowa ba ta zura hijab ta shige toilet, kamar wasu sokaye suka sake bin ta da kallo, yarinyar ta chanja musu sosae, duk da dama tun can sun fahimci miskila ce ta k'in k'arawa, amma yanzu abin yayi gaba sosae, dole su jira Abeeda dan su tabbatar da abinda ta fad'a musu, duk da abin ne akwae wuyar yadda. ... Babu nisa su Ayrah suka yi last paper d'in su ya zamana se komawa gida kenan. A 6angaren Abba kuwa se Allah ya taemake shi lokacin da ze je d'auko Ayrahn ya kar6i albashin sa, dan haka ba k'aramin dad'i yaji ba. Ranar daze tafi ya gama shiryawa cikin manyan kaya na wani yadi, daga d'aki ya fito lokacin Umma na d'akin Yah Sadeeq ta kae masa abinci, ta kalle shi tana murmushi tace "An fito kenan?" shima murmushin ya maeda mata sannan yace "Wallahi kuwa zamu wuce" yayi maganar yana d'ora hular sa samfurin zanna bukar akan sa "Toh Allah ya tsare.." "Ameen Ameen.. amma kafin nan zan biya nayi wa Baban Zaenab ya me jiki, saboda jinjirar da aka haefa masa da aka sallamo su daga asibiti" "Toh ayi mata sannu, gobe idan Allah ya kaemu se mu shiga mu duba ta" "Toh madallah" Abba ya fad'a yana yin gaba, seda ya shiga d'akin Yah Sadeeq dake zaune akan gadon sa yana danna er k'aramar wayar sa, Abba yace "Sadeeq!" "Na'am Abba zaka wuce ne?" "Ehh ba kaci abincin ba" d'an murmushi kad'an yayi sannan yace "A'ah yanzun dae zan ci, Allah ya dawo daku lafiya Abba" "Ameen_Ameen" Abban ya fad'a yana mik'ewa ya fice daga d'akin. Kae tsaye seda ya fara zuwa ya gaeda mara lafiyar sannan ya dawo ta hanyar gidan sa dan wucewa titi ya nemi abin hawa, a k'ofar gidan nasu yaga wata mota me kyau, tunda suka gan shi suka sauke glass d'in motar, wani malamin su Ayrah ya sauko ya k'arasa da murmushi kan fuskar sa yace "Barka da wannan lokacin Alhaji" yayi maganar yana mik'awa Abba hannu, shima Abban mik'a masa hannu yayi suka gaesa yana amsawa da "Barka dae, ashe kae ne?" "Wallahi kuwa, ina zuwa haka ne?" Abba yace "Zan je d'auko Ayrah ne kasan da yake sun gama exam" murmushi malamin nasu yayi sannan yace "Ahh toh ae dama daga makarantar ne aka aeko mu muzo mu d'auke ka a motar nan mu wuce can makarantar" "Toh Ikon Allah" Abba ya fad'a yana bin motar da kallo, dan sosae abin ya cigaba da bashi mamaki, tabbas makarantar tasu Ayrah mutane ne masu karamci da sanin ya kamata "Allah ya saka da alkhaeri" Abba ya fad'a "Ameen Ameen.. Muje koh?" ya fad'a yana yin gaba sannan Abba ya rufa masa baya zuwa wajen motar, shi malamin ya shiga gaba yayin da Abba ya shiga baya, a haka driver ya soma driving babu dad'ewa suka d'auki hanyar Zaria. ... Ayrah ta gama had'a komae nata ta kammale shi inda ya kamata, wani irin d'oki ne keta d'awaeniya da ita, ji take kamar tayi tsuntsuwa ta gan ta a Kano taga Abban ta, Umman ta da uwa uba kuma Yah Sadeeq d'in ta, gaba d'aya ta kasa sukuni tun d'azun wayar ta ke hannun ta tana jiran kiran Yah Sadeeq ko Abba, Jidda ce kawae a d'akin tun d'azu su Bahijja suka fita ko sallama ba suyi ba, bata k'ara minti 5 ba kuwa sega kiran Abba a wayar ta ta, zumbur ta mik'e dan dama k'iris take jira ta d'aga wayar tana karawa a kunnen ta "Abba kunzo?" ta fad'a tun kafin Abban yace komae, murmushi Abba yayi kana yace "Qwarae kuwa ke muke jira yanzu haka" jin da tayi yace suke ya sanya ta tunanin tabbas shi da Yah Sadeeq suka zo dan haka da sauri ta kalli Jidda tace "Mu dae mun tafi" ta fad'a tana Allah Allah Jidda ta amsa ta fice daga d'akin "Ba zaki tsaya kiyi sallama dasu Ruks ba?" 6ata fuska tayi sannan tace bayan ta girgiza kae "A'ah ki fad'a musu na tafi ni dae, se an dawo hutu bye.." ta fad'a tana ficewa daga d'akin "Toh Allah ya kaemu" shine abinda Jidda ta fad'a tana bin Ayrah da kallo sanda ta fice daga d'akin cikin d'oki kae seka rantse tafi shekara ba taga Abban ba. Sosae taji dad'in ganin Abban dan murna gaba d'aya ta kasa dena murmushi se dae tayi mamakin rashin ganin Yah Sadeeq tare da Abban, dan haka ta kasa shiru seda tace "Abba Yah Sadeeq fa?" "Yah Sadeeq na gida, kin san yanayin aekin su hutu yake shiyasa.." se tayi murmushi, a yanzu da taga Abba se d'okin nata kuma ya koma na son ganin Yah Sadeeq da Umma, suna tafiya a hanya suna hira sosae cike da farin ciki da kewar juna, Abban ya zage yana jan d'iyar ta sa da hira, se dae da yake basu kad'ae ne a cikin motar ba ya sanya yawanci hirar tasu bata wuce akan karatu. ... Da wani sauri Bahijja ta turo k'ofar d'akin hannun ta d'auke da wayar Abeeda, Abeeda da Ruks suka biyo bayan ta, idanun ta a warwaje ta furta "Ina Ayrah take?" tayi maganar cikin d'aga murya, da mamaki Jidda ke kallan ta yadda take a wani birkice kamar mahaukaciya tace "Meya faru?" "Ke dae ina take kawae?" "Yanzun nan aka zo aka d'auke ta" Jidda ta fad'a sannan ta d'ora da "Pls meya faru?" komawa Bahijja tayi ta zauna, tana tuna yau da taga Ayrah a cikin d'akin nan babu abinda ze hana ta shak'e ta ko zata ji sauk'in abinda take ji a cikin zuciyar ta, kar6ar wayar hannun ta Ruks tayi sannan ta mik'awa Jidda tace "Kalla ki gani" hannu Jidda ta saka ta kar6i wayar sannan ta shiga kallan hoton sannu a hankali, tana kae hannun ta tana zooming, ta kae wajen minti 1 tana kallan hoton sannan ta d'ago ta kalle su cike da mamaki akan fuskar ta "Kenan abinda Abeeda ta fad'a gaskiya ne?" tayi tambayar tana kallan su su duka, kamar wata k'adangaruwa Bahijja ta shiga girgiza kae tana jin kamar ta rusa ihu "Shegiyar yarinya ta cuce mu, dama seda nayi tunanin kyawun ta ze iya rud'ar shi, ashe mu bamu sani ba ma sun dad'e suna soyayyar su amma shegiyar yarinya seta dinga nuna kamar ma tsanar sa tayi, bamu sani ba ashe wawaye sakarkaru ta maeda mu, k'aramar yarinya tayi wasa da tunanin mu kenan?" ajiyar zuciya Jidda ta sauke kana tace "Lallae kam, ni kae na abin ya bani mamaki wallahi, yaushe muna zaune har hakan ta faru bamu sani ba? Ya akayi hakan?" tayi maganar cike da mamakin dae, girgiza kae Ruks tayi kafin tace "Wallahi ku bari kawae, ni dan mamaki ma na rasa wane tunani ya kamata nayi" Abeeda tace "Ahh toh, ni kae na nasan amanar ku akaci shiyasa naga bazan k'yale ba gwara na sanar daku" "Aekuwa wallahi za taci uwar ta yarinyar nan" Bahijja ta fad'a dan tana ganin kamar duk tafi su takaeci da abinda Ayrahn ta aekata musu, ta shammace
Chapter 24 · 0% Book details