Sashe 33
Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yayi ya kalli inda Ayrah ke zaune, be ta6a tunanin tun yanzu Me gari ze kira su yayi tambayar k'arshe ba, gashi yayi sake saurayin na nan be kae gayi masa komae ba, meya kamata yayi a yanzu? "Ranka ya dad'e ina ganin kawae a bani ita zan maeda ta gidan su!" Alhaji Mato ya fad'a yana kallan Me gari, d'aga kyawawan idanun sa Rk yayi ya sauke su kan Alhaji Mato, kafin a hankali ya saki wani miskilin murmushi, dama seda yayi tunanin hakan zata kasance, shiyasa ya maza yayi wa tufkar hanci, girgiza kae Me gari yayi yana tuna maganar da suka yi da Rk, lallae shima yayi wannan tunanin, ze iya yiwuwa Alhaji Maton be yadda da wannan hukuncin ba ya d'auki Ayrah su tafi wani wajen a d'aura musu aure "Kace kuma ba anan garin iyayen ta suke ba?" cikin in'ina Alhaji Mato yace cike da danasanin abinda ya fad'a d'in "Ehh.. Ehh.. Ranka ya dad'e" jinjina kae Me gari yayi kana yace a nutse "Yanzu ba matar ka bace, shima ba matar sa bace saboda haka baze yiwu a had'a ku ku tafi a haka ba, dan haka kamar yanda muka saba, zan d'aura mata aure da wanda ta za6a, shi seya d'auke ta su koma gidan... Kae sake gwada layin nan muji" Me gari ya k'arasa maganar yana kallan wani dake gefen sa, seya fiddo da waya daga cikin aljihun sa ya sake danna wata number ya kira, kira wajen 3 number daya kira bata shiga ba, ya kalli Me gari yace "Yalla6ae kamar jiyan dae yau ma bata shiga" ya fad'a cike da ladabi, gyaran murya Me gari yayi sannan yace "Babu matsala, zamu yi abinda ya dace.. Cikin su biyun wa kika za6a?" Me gari ya k'are maganar yana kallan Ayrah "Raj!" ta furta ba tare data kalli kowa ba, ba kuma tare data bud'e idanun ta ba, har kuma lokacin hannun ta na dafe da kan ta ne daya cigaba da sara mata, daga inda yake ya lumshe idanun sa yana cigaba da kallan inda take kan ta a k'asa haka zalika idanun ta a rufe "Toh madallah, idan an idar da Sallahr azahar ni da kae na zan d'aura auren nan, Allah yasa albarka" Me gari ya fad'a, huci Alhaji Mato ke fitarwa daga bakin sa zuciyar sa na cigaba da tafarfasa, shi kad'ae yasan abinda ze yiwa Rk, dan ya riga yaci alwashin baze ta6a barin sa yaci bulus ba, baze ta6a k'yale shi ba, baze ta6a rangwanta masa ba. Matar nan ce dae ta kamata ta mata jagora zuwa cikin gidan, a lokacin kawae zubewa tayi akan gadon, daga kukan har hawayen yanzu babu ko d'aya dake fita, kawae ta cigaba da kwanciyar ne cikin rashin sanin abinyi, kuma cikin rashin sanin mafita, se a lokacin ta tsaya tayi tunani, shin wanene wannan mutumin? Meyasa ya sato ta daga gidan su? Meyasa yake son auren ta bayan ita ko sanin sa bata yi ba? Meyasa ya rabo ta da gidan su? Meyasa beje ya nemi auren ta wajen Abban ta ba kamar yanda Addini ya tanadar? Meyasa yake son neman auren ta ta wannan sigar? So take ta tabbatarwa da kan ta amincewa auren Rk da tayi ba kuskure bane amma hakan ya citira, kawae ji take kamar ta tafka wani babban kuskure ne auren sa data amince zata yi, nan take kuma wani tunanin ya fad'o mata "Auren kwangila ne ae, kwangilar ma ta yini d'aya, daga zarar ya sawwak'e miki babu wanda ze san kin aure shi, taemakon ki yayi ba komae ba..." abinda zuciyar ta keta sak'a mata kenan amma har y anzu ta kasa yafewa kan ta, musamman idan ta tuna Abban ta, ta tuna irin amincewar da yayi wa su Raj amma suka ci amanar sa, ta tuna yanda yace ba zata auri Rk d'in ba amma yanzu idan suka ji labarin ta aure shi na yini d'aya fa? "In har kin so baza suji labarin ba" abinda ta sake sak'awa kenan a cikin ran ta, se kawae ta lumshe idanun ta tana sake dafe kan ta da dukkan hannayen ta. ... Har aka idar da Sallah yana cikin masallaci, ya kasa motsawa ko nan da can ne, idanun sa a lumshe suke tunani barkatae na yawo cikin k'wak'walwar sa, tun jiyan nan daya kashe wayar sa be sake kunnawa ba dan baya son a kira shi ko kad'an. K'arfe 2:25 mutanen dake cikin masallacin suka shaeda d'aurin auren RAJ KABEER da AYRAH IBRAHEEM KHALEEL akan sadaki mafi k'ank'anta wato mafi alkhaeri.. Mhiz Innocent..... https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* Page 032 ___Wani irin sanyi ne ya shiga ratsa ilahirin jikin sa lokacin da yaji zancen d'aurin auren, a hankali ya lumshe idanun sa, se dae ga mamakin sa sosae bugun zuciyar sa ya k'aru, seya dakata yana tuna kasadar da yayi da kuma k'alubalen da yasan dole seya tunkaro shi, amma tunda dae ya gama da wannan koma wanne k'alubale ne yana ganin me sauk'i ne, a hankali kuma se yaji wani rauni na son shigar sa, cikin sakannin da basu gaza 2 ba ya bud'e manyan idanun sa da hakan yasa zaka iya fahimtar yadda yanayin fuskar sa take, sosae annuri ke fita daga kyakykyawar fuskar sa, seya fesar da iska daga bakin sa sannan ya cigaba da kar6ar hannun mutane dake mik'a masa suna gaesawa, wasu da gasken dan taya murna ne suke mik'a masa hannun su gaesa yayin da wasu suna so ne kawae su gaesa da shi d'in saboda yadda yake, d'an birni, had'ad'd'e kuma kyakykyawa, kwata kwata baya lura da yanayin mutum kawae ze mik'a tattausan hannun sa ne su gaesa duk da ba kallan fuskar mutanen yake ba. ... Ayrah na cikin gida sam bata san abinda ke faruwa ba, ita gaba d'aya tana jin komae ne kamar a mafarki ko kuma wani wasan film, dan haka ta gaza amincewa kan ta wannan abinda yake faruwa gaskiya ne, a yanda tafi d'auka wani mummunan mafarki ne take yi wanda yake nuni da tana neman bijirewa maganar Abban ta, dan haka take fatan tayi maza ta farka daga baccin, se dae me? Har yanzun tak'i farkawa, tun tana cigaba da yadda mafarkin ne har tazo ta fara tunanin shin ko gasken ne? Duk abinda ke faruwa a yanzun da gaske ne? Ba ita ta tashi daga kwancen da take ba seda taji ana kiran sallah, a hankali ta fara k'ok'arin mik'ewa se dae jirin daya kwashe ta ta sanya ta saurin komawa ta kwanta tana sakin wani kuka, ita kad'ae tasan abinda take ji a jikin ta, ita kad'ae tasan yanda take jin kan ta da gangar jikin ta, gaba d'aya jin kan ta take yi ya mata wani gingirin kamar ba'a jikin ta yake ba, ga jikin ta da gaba d'aya ta rasa gane a wane yanayi ma zata saka shi, ta kae wajen minti 1 a kwancen seda jirin ya d'an yi sauk'i sannan ta mik'e duk da yanda take kallan abinci da ruwa a ajiye hakan be sanya tabi ta kan su ba, kae tsaye ta fice daga cikin d'akin zuwa ban d'akin dake kusa da d'akin da take ciki, alwala kawae tayi ta dawo cikin d'akin ta tada sallah. ... "Toh kae Allah ya baku zaman lafiya, Alhaji Mato kuma Allah ya baka hak'uri, dama kasan ance ba komae ne idan aka rasa ake kuma samun sa ba, Allah ya musanya maka da wadda ta fi ta" Me gari ya fad'a yana kallan su su duka "Ameen ranka ya dad'e, Allah ya k'ara girma" Rk ya fad'a ba tare daya d'aga ido ya kalli Alhaji Mato dake jifan sa da wani kallo na gargad'i da kallan nan irin na zaka sani, Alhaji Mato be iya cewa komae ba saboda yasan idan ya bud'e baki komae ka iya fitowa daga bakin sa, k'ila ma yayi maganar da zata iya tona masa asiri a cikin k'auyen, dan haka yaga shirun nasa yafi masa alkhaeri "Ayi mata magana ta fito se ku tafi koh?" Me gari ya fad'a yana kallan Rk, jinjina kae Rk yayi lokaci d'aya yana lumshe idanun sa se kuma ya bud'e bakin sa a nutse ya furta "Ehh" babu 6ata lokaci Me gari ya aeka wani daga cikin yaran sa zuwa cikin gidan cewar a fito da Ayrah. ... Lokacin da matar nan ta sake shigowa cikin d'akin da k'yar take iya bud'e narkakkun idanun ta da suke wani lumshewa da kan su kamar er maye, sanyi sosae take ji a jikin ta wanda hakan ya sanya ta takurewa cikin hijab d'in ta tana jin kamar k'asusuwan ta zasu tsage, ciwon da kan ta yake yi kuwa se abinda yayi gaba, gaba d'aya jikin ta yayi wani irin tsami "Ki taso zaku tafi" maganar da taji matar tayi ya sanya tilas ta bud'e lumsassun idanun ta ta jefa su kan matar da take gani biyu biyu, ta d'auka ma ba taji abinda tace ba dan haka ta sake maemaetawa a karo na biyu, a hankali ta zura k'afar ta daga kan gadon da take, tilas ta sake runtse idanun ta saboda yadda taji kamar ginin gidan gaba d'aya ze fad'o a kan ta, bata so ma wasu su fahimci bata da lafiyar ballantana ace za'a d'aga tafiyar tasu, burin ta d'aya kawae ta bud'e idanun ta ta gan ta cikin gidan su, gata ga Umman ta, ga Abban ta ga kuma Yah Sadeeq d'in ta, seda matar tayi gaba sannan ta mik'e tabi bayan ta a nutse tana tafiya tana dafa bango saboda kada ta fad'i, sosae tayi da gaske dan kada ta zube kafin ta isa wajen, cike da k'arfin hali ta cigaba da takawa har zuwa wajen Me garin. Bin ta yayi da kallo sanda ta zube a k'asa idanun ta a lumshe, daga yanayin yadda ta zauna d'in kawae zaka fahimci ba'a lafiyar ta take ba "Toh yanzu dae zamu damk'aki hannun mijin ki, Allah ya bada zaman lafiya" shine abinda ta tsinto Me garin na fad'a, ta sake lumshe idanun ta a karo na barkatae tana jin wani irin yanayi, kenan da gaske an d'aura mata aure da Raj? da Me gari yasan tashin hankalin da take