Sashe 42
Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mummy ta fad'a tana kallan ta "Mummy, Yah Suraj ne mana, Mummy har yanzun fa baya d'aga waya na ya yake so zuciya ta tayi?" ta k'are maganar kamar zata fasa ihu, tsaki Mummy taja sannan tace "Dallah rabu da shi, kwana nawa ya rage ya shigo hannun ki? Ke dae kawae ki maeda hankalin ki wajen gyaran jikin nan, dukkan magungunan nan ki tabbatar kina shan su kamar yadda suke a tsare, baki ga har kin fara chanjawa ba kina ta cika tako ina? ina me tabbatar miki a hannun ki zaki kama shi, dan kuwa da kan shi ze dinga bibiyar ki ba dae ke ki bi shi ba.." _*Ina fatan yanzu kun fahimci abinda nake k'ok'arin nuna muku, kowanne abu idan kaga writer tayi akwae dalilin yin sa, akwae dalilin rubuta shi, babu yadda za'ayi kayi abu babu dalili, nayi hakan ne dan janyo hankalin wasu iyayen masu saurin yankewa 'ya'yan su hukunci ba tare da sun yi dogon bincike b duk kuwa sa irin yaddar da kayi musu, su kan su ae gashi nan yanzu sun yi nadamar hakan da suka yi, dama kuma shi novel ya gaji haka, na san dukan ku baku yi tsammanin Umma ko Abba wani a cikin su ze d'auka Ayrahn da kan ta guduwa tayi ba, dukan ku nasan kun ta'allaqa ne akan zasu zata sace ta akayi, wannan dalilin ne yasa na juya muku kwanya, babu yadda za'ayi abinda readers ke tunani kae kuma kayi shi a wani lokacin, dan kuwa littafin ze zama lami ne, ze zamana kowa da kowa yasan abinda ze faru a gaba kenan, wannan ba shine kyakykyawan novel ba wanda tun farkon fara karantawa kasan abinda ze faru a gaba. Ina fatan za'a dena tambaya ta dalilin da yasa nayi hakan.*_ Kuyi manage da wannan pls.. https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* Page 037 ___"Allah ko Mummy na?" Muneerah ta fad'a tana murmushi cike da jin dad'in zancen Mummy, murmushin itama Mummy ta maeda mata dashi kana tace "Kada ki saka kokwanto a ran ki, kamar yadda na fad'a haka ne ze kasance" farr tayi da idanun ta dake d'auke da lashes na kanti, wanda da tasan yanda ya sake shigar da k'ananun idanun ta da bata saka ba, amma ita gani take haka zalika ji take baya ita, mik'ewa tayi tana kallan Mummy tace "Yunwa nake ji Mummy kin gama abinci ne?" yamutsa fuska Mummy tayi sannan tace "Se dae idan yunwar kike ji ki dafa ko indomie ce ki ci" bata sake cewa komae ba se hanyar kitchen data wuce kawae. ... Sanye yake cikin k'ananan kaya, fuskar sa ta sake yin wani shahararren kyau kamar wanda ake k'arawa kyau, haka zalika kwantacciyar sumar kan sa ta sake yin bak'i da sake kwanciya, jikin sa babu abinda ke tashi se k'amshin sassanyan turaren sa me dad'in shak'a, a nutse yake takawa zuwa part d'in Abbu cike da fata a cikin ran sa, cikin sa'a kuwa k'ofar parlourn nasa a kulle take, lumshe idanun sa yayi sannan ya bud'e ya d'an kalli gefe da gefe sannan ya sanya spare key d'in daya d'auko daga d'akin Ummee ya bud'e k'ofar, a hankali ya tura kan sa cikin d'akin, kamar wanda ya fara ganin d'akin yau haka ya soma wuwwulga idanun sa ko ina na cikin d'akin, cikin sauri ya shige bedroom d'in Abbun sannan babu 6ata lokaci ya soma bincika inda yasan Abbun na ajiye abubuwa masu amfani a cikin wajen, ya kae wajen minti 30 yana binciken be samu abinda yake nema ba, har cikin ran sa ya d'an ji sanyi kad'an akan zargin daya soma yiwa Abbun nasa, se kuma ya dakata abu na k'arshe dabe duba ba shine saman wardrobe, cikin sauri yanzun ma ya soma bincikawa har zuwa sanda ya d'akko wata leda, be bud'e ba seda ya sakko da ita k'asa, cikin k'ank'anin lokaci ya shiga fito da abinda ke cikin ta, bayan ledar akwae wata ledar a ciki sannan wata jaka, seya tsaya ya bud'e madaedaeciyar jakar dae_dae lokacin da wani envelope ya bayyana, haka nan kawae yaji jikin sa yayi wani mugun sanyi duk da har zuwa lokacin be san menene a ciki ba, a nutse ya shiga zaro takaddun dake ciki, be tsaya ba seda ya fiddo su duka kana ya saka hannu ya d'ago su cikin hannun sa ya shiga karantawa, a hankali yake karantawa kamar me tsoron karantawa ko kuma me koyon karatu, abinda dae yake guda d'in shine ya faru, wato sunan Abban su Ayrah daya fito 6alo_6alo a jikin takaddar, runtse idanun sa yayi na tsawon minti 1 yana jin 6acin rae, zafi gami da wani irin takaeci mara misaltuwa, meyasa Abbun sa yayi haka? Meyasa Abbun sa ya zamo cikin mutanen da za'a kiran su da butulu? "Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" shine abinda ya shiga maemaetawa a cikin bakin sa har lokacin kuma bugun da zuciyar sa ke yi be saitu ba, ya kae wajen minti 2 a hakan sannan ya mik'e dan tuna a inda yake, beyi k'asa a gwuiwa ba wajen d'aukar ledar ya maeda ta saman wardrobe sannan ya d'auki envelope d'in ya fito dashi, karo suka kusa yi da Ummee dake shirin shigowa cikin d'akin, da mamaki take kallan sa "A'ah Raj! dama kana nan? Abbun naku ya dawo ne?" seda ya d'aga idanun sa da suka yi d'an ja saboda 6acin rae sannan yace "A'ah.." ya fad'a yana shirin wucewa "Kae lafiyar ka kuwa a kwana biyun nan?" baya a mood d'in yin magana sosae, musamman kuma a yadda yake jin 6acin rae na taso masa haka nan ya sanya shi saurin girgiza kae sannan yace "Lafiya ta k'alau.." daga nan yayi gaba yana cigaba da kare envelope d'in hannun sa "A'ah wannan envelope d'in fa?" seya dakata da sauri kamar baze juyo ba se kuma ya d'an lumshe idanun sa sannan yace har lokacin be juya ba "Takaddu ne akan asibiti, nazo d'auka ne saboda naga baya nan" jinjina kae Ummee tayi ba tare data kawo komae a ran ta ba kawae ta k'arasa cikin bedroom d'in yayin da shi kuma ya cigaba da tafiya, yana shirin fita daga d'akin Abbu ya shigo cikin d'akin sanye cikin farar dakakkiyar shadda, kallan sa yayi da mamaki yace "A'ah Raj!.." "Wajen Ummee nazo, tana bedroom.." shine abinda ya furta kawae ba tare daya kalli Abbun ba kuma be jira cewar sa ba ya fice daga d'akin, da kallo kawae Abbu yabi shi dashi sannan ya dawo da duban sa cikin d'akin yana girgiza kae. Kae tsaye d'akin sa ya wuce, babu 6ata lokaci ya jefar da envelope d'in hannun sa sannan ya nemi kan side drawer ya zauna, gaba d'aya kan sa ya matuk'ar kulle, ashe maganar Yah Sadeeq gaskiya ce? Ashe iyayen Ayrah basu yi laefi ba da suka hana shi auren ta? Tabbas Abbu ya shammace su ya yaudare su sannan ya saka k'afa yayi fatali da yaddar da Abba yayi masa bayan irin tarin hallacin da Abban yayi musu su duka, meyasa Abbun yayi haka? Abba mutum ne me kirki wanda ya d'akko su daga rana zuwa inuwa, amma Abbun daya tashi se ya d'auki Abban ya maeda shi cikin ranar shi kuma ya koma cikin inuwar "Yah Allah! Why Abbu? Why?" ya fad'a a hankali yana cusa hannayen sa duka cikin sumar kan sa, gaba d'aya ji yake inama ace wannan abun ba gaskiya bane ba? Inama ace mafarki ne kawae yake yi, idan kuwa gaske ne ya zama dole ya nemowa kan sa da kuma shi kan sa Abbun mafita kamin lokaci ya k'ure musu, ranar gaba d'aya sukuku ya wuni, ko bacci be iya yi ba saboda wannan al'amari daya hargitsa masa kwanya. .... A d'aya 6angaren kuwa kwanakin da suka biyo baya seya zamana wata kulawa ta musamman iyayen ke bawa Ayrah, kamar ma k'ara musu soyayyar ta akayi dan hatta kulawar data ke samu a yanzun tafi ta da, ita kam farin ciki take ji kamar tayi mene, tana kuma iya bakin k'ok'arin ta wajen ganin ta faranta musu ran su ba tare data 6ata musu ba. .. Suna zaune su duka a tsakar gidan suna hira cikin farin ciki da k'aunar junan su, Ayrah na daga gefen Umman ta cikin doguwar rigar wani yadi me matsakaecin kyau fuskar ta yanzun babu laefi ta d'an samu albarkacin kwalli data saka, dan haka ya 6oye kaso da yawa daga yanda tayi zuru zuru, tayi kyau sosae duk da bayan kwallin babu wani abu data k'ara a fuskar ta, se kuma mayafi data yafa shi a kan ta ta zubo dashi kan kafad'ar ta, kallan Yah Sadeeq daya d'an rik'e k'afar sa tayi kana tace "Yah Sadeeq k'afar ce?" murmushi yayi sannan ya girgiza kae kana yace "A'ah Auta, ba k'afar bace ba.." "Ayrah.. Je ki d'auko masa maganin nan ya shafa, kin san halin sa dae.." babu musu ta mik'e zuwa cikin d'akin dan d'akko masa maganin, dae_dae lokacin da wani yaro yayi sallama cikin gidan, dukan su suka amsa masa sallamar "Wae a waje wani yace ayi masa iso.." Abba ya kalli yaron kana yace "Waye?" "Yace wae Raj sunan sa.." tana shirin fitowa taji sunan da aka ambata, seta dakata da sauri tana jin yanda bugun zuciyar ta ya k'aru, ko taku d'aya ta kasa k'arawa daga inda take kamar me tunani. Kallan Umma Abba yayi sannan ya maeda kan yaron yace "Fad'a masa ya shigo" fita yaron yayi, ita kuma Umma ta koma d'akin ta ta d'auko babban mayafin ta ta yafa sannan ta fito ta nemi waje ta zauna, tunda taji Ayrahn shiru tak'i fitowa tasan taji wanda akace ze shigo, Ayrahn har mamaki take bata a kwanakin nan, duk irin yadda take k'aunar Raj d'in amma tun dawowar ta gida bata sake maganar sa ba, bata sake koda maganar abinda ya shafe shi ba, kuma duk Umman tasan hakan ya ta'allak'a ne da tun farko data fahimci basa k'aunar sa, toh amma yanzu kam yaya zasuyi tunda har igiyar aure ta ratsa tsakanin su?. Da sallama ya shigo cikin gidan sanye cikin bluen shadda jamfa da wando wad'anda suka matuk'ar yi masa kyau, se dae yanzu ma babu hula a kansa, kusan tare suka