← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 90

Sashe 52

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bata ta6a tunanin zasu kae i yanzu babu wani abu daya gifta tsakanin ta da Rk d'in ba bayan uban gyara da maganungunan da tayi ta d'irkawa cikin ta, dan haka zata samarwa kan ta mafita. .. Tura k'ofar d'akin Ummee tayi sannan ta saka kan ta cikin d'akin, har zuwa lokacin Abbu na zaune kan kujera yayi shiru hannun sa akan ha6ar sa yana d'an motsi da hannun sa kamar me tunani, k'arasawa tayi ta zauna kan kujerar gefen sa sannan tace "Abbu wae dama Raj ya koma asibiti ne?" kamar ba zece komae ba se kuma ya juyo ya kalle ta "Hala bakya ganin a yanayin da nake ciki?" "Yanayi kuma Abbu? Meya faru?" jin da tayi yayi shiru ya sanya ta fad'in "D'azu Muneerah ta kira ni take sanar dani wae ya koma aeki, shi haka akeyi? Kwana d'aya da yin biki seya bar amarya a gida ya.." mik'ewar da Abbu yayi tsaye gami da d'aga mata hannu shine ya sanya ta dakatawa da niyyar k'arasa abinda ta soma fad'i "Kin san abinda Mukhtar ya aekata min kuwa? Yaudara ta fa yayi? Million 50 ya cinye min yazo ya had'a k'araerayin sa ya fad'a min, ke kuma kin zo kina min wasu tambayoyi, meya hana ki tambayar sa inace yanzu ya bar gidan koh?" kallan Abbu kawae take yi yanda yake maganar da alama ran sa a 6ace yake, dan kuwa magana makamanciyar wannan ba kasafae take shiga tsakanin su ba "Ki tashi ki je ina so na samu nutsuwar yin tunani sosae" "Amma ae ko shawara na baka kamar yadda aka saba koh?" tayi maganar a nutse "Ki je kawae, rae na a 6ace yake, idan na huce zan kira ki.." bata sake cewa komae ba ta mik'e ta bar d'akin zuciyar ta fall tunani kala kala, gana wannan abinda ya faru akan kud'in Abbun, ga kuma yanda maganar Abbun ke nuna kamar Rk ya shigo cikin gidan amma bezo wajen ta ba? Meke faruwa kenan?. ... A k'ofar wani madaedaecin gida yayi parking motar ta sa, ya sauka ya saka mukulli ya bud'e gidan sannan ya dawo ya tashi motar ya shigar da ita zuwa cikin harabar gidan dake da yalwar girma, ko daga harabar gidan ya isa ka gane yanda gidan ya had'u saboda yadda aka k'awata ta da abubuwa masu kyau. Kallan fuskar ta yayi yanda take kallan gidan kamar ne nazari, se dae abinda be sani ba gidan ya birge ta ko be birge ta ba, murmushi ya wanzar akan fuskar sa kana yace har zuwa lokacin yana kallan kyakykyawar fuskar ta "Nan ya.." kafin ya k'arasa maganar wayar sa dake ajje ta shiga ruri, kallan me kiran yayi, se yayi saurin saka hannun sa ya d'auki wayar ya kara a kunnen sa "Hello Ummee barka da wannan lokaci" ya fad'a kafin Ummeen tace komae "Barka.." shine kawae abinda ta fad'a, se da ta d'an numfasa sannan tace "Ashe har nayi lalacewar da zaka shigo gidan nan ba tare da ka zo ka gaeshe ni ba?" cike da mamaki yace "Ummee ni kuma?" "A'ah ni" ta fad'a tana jin takaeci, seda ya gyara zaman sa sannan ya d'ora hannun sa akan fuskar sa kana yace "Ummee na shigo fa, Hadeeza tace min kin yi sammakon fita ne.." "Ohh.. Lokacin ka zo?" se da ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "Ehh fa" "Ohk ina ka tafi ka bar Amaryar ta ka?" shiru yayi cike da mamakin tambayar Ummeen, kenan tun yanzu Muneerahn ta fara nuna wacece ita? K'arar sa ta kae wajen Ummeen ko kuma me take nufi? "K'ara ta ta kawo miki kenan Ummee?" ya tambaya 6acin ran dake cin sa na bayyana cikin muryar sa "A'ah A'ah kada ma wannan ya shiga kan ka, babu wani k'arar ka data kawo, ni na tambaye ta inda kake tace ka fita.." sake lumshe idanun sa yayi, ya d'an yi jimm kafin yace "Ehh Ummee ina d'an wani aeki ne, zuwa gobe zan koma.." "Toh Allah ya taemaka.." daga haka ta katse wayar, shima kuma ya saka ta cikin aljihun gaban rigar sa, a nutse kuma ya shiga juyawa zuwa inda Ayrah ke zaune dan dama tun d'azun yake jin idanun ta a kan sa, se kuwa caraf ya kamata dumu_dumu tana kallan sa, dan kuwa 4 eyes suka yi, se tayi saurin kauda kan ta gefe, duk jikin ta a matuk'ar sanyaye, dan kuwa duk da bata san akan wace magana suke yi ba amma haka nan kawae taji wayar sam bata kwanta mata ba, ya d'an soma lumshe idanun sa kamar ze rufe su se kuma ya bud'e su yace a nutse "Babe.." ya fad'a cikin wani irin salo, juyar da kan ta tayi tana kallan harabar gidan ta jikin glass d'in kusa da ita tana jin yanda zuciyar ta ke sake yin rauni, seya saka hannun sa ya kamo tattausan farin hannun ta da yafi kusa da shi ya sanya cikin nasa ya rik'e gam "Ni dae ka sakar min hannu" ta fad'a bayan ta juyo tana saka d'ayan hannun ta kan nasa dan cire nata dake cikin nasa, se hakan ya bashi damar d'ora d'ayan hannun nasa kan wanda ta d'ora d'in "Sorry my luv.." ya fad'a a narke yana karyar da wuya, lokaci d'aya kuma yana yin k'asa da kan sa yana lek'a fuskar ta da tayi k'asa da ita, idanun ta ta runtse kawae hakan ne ya sanya shi sakin murmushi yana tashi zaune ya sake matsa hannun ta duka dake cikin nasa, dae_dae lokacin da hawayen da suka zubo a idanun ta suka samu damar zuba akan hannun nasa "Oh my god, kuka kuma?" ya fad'a yana d'ago ta, ganin har lokacin tak'i bashi damar ganin fuskar ta ta ya sanya shi jan ta cikin jikin sa yana jin yanda bugun zuciyar ta ke fita da gudu "Wannan yarinyar akwae kishi, ranar kuma dana had'a su gida d'aya ko ya zata kasance?" ya tambayi kan sa cikin zuciyar sa, a fili kuma se cewa yayi "Ya isa haka kin ji, ni fa ba tafiya zan yi ba, zan dae je in kwana a can sannan se in dawo nan ma in kwana, ba wae dan hakan na nufin wani abun ba" ya fad'a yana d'an bubbbuga bayan ta alamar rarrashi, runtse idanun ta tayi lokaci d'aya tana jan numfashi dan bata so kukan ya fito, ita kan ta bata san sanda hawayen suka zubo ba, kawae dae ta san wani irin zafi take ji a cikin zuciyar ta, sun kae wajen minti 1 a haka sannan ya sake ta, ta mik'e zaune ya sake bin ta da idanun sa wanda take ta k'ok'arin kaucewa, da kan ta ta saka hannu ta fita daga motar, shima be matsa ba ya fito daga cikin motar, shine yayi gaba zuwa aenahin inda parlourn da sauran d'akunan gidan suke yayin da ta rufa masa baya jikin ta a sanyaye. Parlour ne me yalwar girma da kyau gami da tsari, furniture d'in cikin sa sun yi matuk'ar dacewa da kalar painting d'akin, komae na ciki abin kallo ne saboda yanda aka tsaya aka k'awata parlourn da kayan alatu, saboda yadda take jin jikin ta a sanyaye hakan ne yasa bama ta tsaya 6ata lokaci wajen kallan yanda tsarin parlourn yake ba "Ki shiga wannan ki watsa ruwa, bari na shiga wannan" ya fad'a yana mata nuni da wani d'akin, babu 6ata lokaci ta fad'a cikin d'akin da shima ya gaji da had'uwa, nan ma bata tsaya wani kalle_kalle ba ta fad'a toilet d'in tayi wanka sannan ta fito, a gaggauce ta saka wata doguwar riga me taushi sannan ta d'ora madaedaecin hijab akae, babu abinda ta shafa a jikin ta kawae ta nemi waje ta zauna cikin rashin sanin abin yi. ... Wajen k'arfe 9pm tana kwance kan gadon, taji dad'i daya kasance tana iya jiyo motsin sa cikin d'akin sa, duk da yanda bata so ya bar gidan amma gwara ya zauna a d'akin sa itama ta zauna a nata, dan haka ta d'an lumshe idanun ta ko baccin ze zo ya d'auke ta, dae_dae lokacin ya turo k'ofar d'akin, seta d'aga idanun ta a hankali kamar wata munafuka ta kalle shi sanda shima nasa idanun ke kan ta, da sauri ta runtse idanun ta tana jan blanket ta lullu6e har saman kan ta saboda yanda ya bata kunya, dan kuwa boxer ne a jikin sa dududu da k'yar ya rufe cinyar sa, se singlet dake jikin sa wadda ta fallasa halittar murjajjen jikin sa me matuk'ar kyau da d'aukar hankali, murmushi ya saki sanda ta rufe fuskar ta ta, ya k'araso yana girgiza kae gami da k'arasawa shima ya hau kan gadon, daga inda take kwance tana jin sanda ya hau kan gadon, hakan ne ya sanya ta sake curewa waje d'aya tana sake duk'unk'une kan ta cikin bargon. Pillow ya ja ya kwanta akae sannan ya kae hannun sa kan bargon da take sake cukwuikuye shi waje d'aya, ya d'an ja, se kuwa ta sake rik'ewa "Nima ae lullu6a zan yi.." ya fad'a cikin karyar da murya yana kuma cigaba da jan bargon, rik'ewa ta sake yi kamar ta fashe da kuka "Toh ayi raba dae_dae, ki ja rabi in ja rabi" "Toh ae kae ma kana dashi a d'akin ka, ka d'auko mana" ta fad'a bayan ta tura bakin ta kuma a shagwa6e, ya d'an lumshe idanun sa sannan yace "Ni wannan nake so, saboda idan na lullu6a da shi zan dinga jin k'amshin ki.." wata irin kunya ce ta kamata, har bata san sanda ta cika bargon ba tana rufe fuskar ta kamar yana ganin ta, sakin da tayi ne ya sanya shi saurin jan bargon ya yaye shi gaba d'aya kana ya sauke idanun sa akan fuskar ta dake a rufe, iskar sa taji ta soma ratsa ta ne ya sanya ta bud'e fuska se taga wayam, babu bargon babu alamar sa, ya kanne mata idanun sa guda d'aya yana murmushin gefen baki, sake curewa waje d'aya tayi sannan tace kamar zata yi kuka "Allah ni dae ka bani, sanyi fa nake ji" "Uhmm sanyi? Bari kiga yanda za'ayi" ya fad'a yana sanya hannun sa ya birkitota zuwa cikin jikin sa, ya k'ank'ame ta sosae kamar
Chapter 52 · 0% Book details