← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 90

Sashe 53

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wanda ze 6alla ta gida biyu, er k'ara ta saki tana zamewa daga jikin sa, se ya kae bakin sa cikin kunnen ta kamar me rad'a ya furta "Sanyi kike ji ae, kiyi baccin ki, ga d'umin da yafi na bargo nan" yayi maganar cikin wani irin salo yana sake shigar da ita cikin jikin sa lokaci d'aya yana lumshe idanun sa saboda yanda jikin sa yayi wani mugun sanyi, ga wani sanyin k'amshi dake ta tashi daga jikin ta har ma da gashin kan ta "Kiyi bacci.." ya sake fad'a yanzun ma a hankali, se tayi shiru kawae tana cigaba da sauke numfashi da sauri, seda numfashin na ta ya soma komawa dae_dae sannan tayi shiru ta lumshe idanun ta tana shak'ar daddad'an turaren sa me sanyi. Da safe ya riga ta tashi saboda ba wani baccin kirki yayi ba yanda ta kasance kane_kane a cikin jikin sa ta hana shi sukuni, a nutse ya sauke lumsassun idanun sa a kan ta sanda take baccin ta a nutse tana kuma sauke numfashi shima a nutse, fuskar ta ta sake yin fayau fiye da jiya, d'an k'aramin bakin ta ya sake tsukewa, sosae kyawun ta ya sake bayyana a lokacin da take baccin, se ya samu kan sa da lumshe idanun sa, a hankali ya kae bakin sa kan nata ya d'an sumbata kad'an gudun kada ta tashi sannan ya zame ta daga jikin sa ya mik'e ya fad'a toilet. ... Tun safe Muneerah ta tashi ta fad'a wanka ta fito ta shirya cikin doguwar riga irin me bin jikin nan, ta bi jikin ta da tsadaddun maya mayan ta na bleaching sannan ta d'ora da wasu mayukan akae, gaba d'aya jiyan da kewar sa ta kwana, shiyasa tana tashi ta shirya tun yanzun dan kuwa tana da tabbacin da safe ze dawo cikin gidan, yanzu kam tana ganin ko menene zece mata ba zata bar shi ba dole ya bata hak'k'in ta, koda shi baya buk'atar ta ae ita tana buk'atar sa yadda baya zato. Tana shirin fita daga d'akin wayar ta dake kan side drawer tayi k'ara, seta dakata ta koma da baya ta d'auki wayar, da sauri ta d'aga wayar tana karawa a kunnen ta lokaci d'aya kuma tana neman waje ta zauna gefen gadon ta "Aunty Zeenah" ta fad'a cike da jin dad'in ganin kiran ta, dan ta san in dae Aunty Zeenahn ta kira baya wuce k'aruwa ce "Na'am Autar Mummy ya kike? Ya amarci?" ta6e baki tayi kamar Auntyn na gaban ta, kasancewar Aunty Zeenahn k'anwar Mummy ce kuma tana kallan ta ne kamar Mummyn yasa tasu tazo d'aya, suna d'asawa sosae "Auntyy, babu fa wani amarci" "Bangane ba?" Aunty Zeenah ta tambaya cike da mamaki, seda ta gyara zaman ta sannan tace "Yadda dae kika ji na fad'a" tayi maganar kamar wadda take magana da sa'ar ta "Wae kina nufin babu wani abu daya shiga tsakanin ku ko kuma me kike nufi?" Aunty Zeenah ta tambaya har lokacin cikin mamaki "Haka dae nake nufi" "Ehh lallae na yadda yaron nan tantiri ne, duk irin abubuwan da muka yi miki baki ja hankalin sa ba?" kamar zata yi kuka tace "Wallahi Aunty, ko kusa dani ma bezo ba, nice ma naje wajen sa fa, amma duk da haka.." "Muneerah!!" Aunty Zeenah ta katse Muneerah daga fad'ar abinda take niyyar fad'a "Na'am Aunty" cikin 6acin rae Aunty Zeenah tace "Yanzu duk irin fad'an da muka miki ashe baki ji ba? Wato kyace kuyi ku gama abinda kika yi niyyar yi shi za kiyi koh? Kae kan ki kike yi wajen namiji tun ranar farko Muneerah ashe baki da wayo?" shiru tayi tana harare harare daga inda take zaune, jin tayi shiru ya sanya Auntyn fad'in "Ki bud'e kunnen ki kiji da kyau, cikin satin nan zamu shigo Kano, kada ki sake zuwa wajen sa, kada ki sake neman sa, akwae wani turare zan kar6o miki shi, shafawa kawae zaki yi se kije ko da giftawa ta kusa dashi ne kika yi wallahi se wani abun ya shiga tsakanin ku, dan kuwa in dae ya shak'i wannan turaren baze iya kwana ba tare da mace ba, daga nan kuma shikenan ya zama naki ke d'aya, se yanda kika ga damar yi dashi, idan dae nazo zan miki dogon bayani..." cike da farin ciki, jin dad'i mara misaltuwa tace bayan ta mik'e hadda tsallen ta "Don Allah da gaske Aunty?" murmushi Aunty Zeenah tayi jin yanda farin cikin Muneerahn ya bayyana har cikin muryar ta "K'warae kuwa, ke dae kawae ki jira ni cikin satin nan komae ze kammala, muma ma huta da k'orafin ki" "Se dake Aunty na ta kae na, ina godiya Aunty na, Allah ya k'ara miki lafiya da nisan kwana" "Ameen_Ameen" daga haka suka cigaba da tattaunawa kafin daga bisani suka yi sallama, zaunawa tayi kan gadon farin ciki kamar ya kashe ta, ita kad'ae tasan yanda taji dad'in wannan al'amari, burin ta na mallakar Rk d'in na dab da cika, abubuwan farin ciki kala_kala. ... Fitowar ta kenan daga wanka ta d'ora hijab akan madaedaecin towel d'in dake jikin ta, a nutse ta k'arasa gaban mudubin d'akin taja stool ta zauna sannan ta fara mitstsika vaseline d'in data gani a ajje, k'aramar wayar ta data yasar da ita ta manta da rayuwar ta itace ta shiga ruri, da mamaki ta kalli inda wayar take, kafin a hankali ta mik'e ta taka zuwa inda wayar take, seta tsaya tana kallan numbers d'in dake yawo akan wayar, bata san number ba, kamar ba zata d'aga ba se kuma ta d'aga ta kara a kunnen ta, yana daga cikin sarar ta, in dae bata san number ba aka kira ta ta d'aga bata fara yin magana se daga d'aya 6angaren anyi magana "Hello, Ayrah Ibrahim Khaleel" taji an ambata daga d'aya 6angaren, hakan ne ya sanya ta fad'in "Salamu Alaek" "Wslm" daga can 6angaren aka amsa "Ina ta neman number ki bana samu, se yau Allah yayi na samu.." kamar taso ta gane muryar amma bata san ta wacece ba, hakan ne ya sanya yin d'an murmushi kana tace "Eyyah, amma bangane me magana ba?" "Bahijja ce fa, Bahijja A.B.U" "Ohhh, Bahijja ya kike?" ta fad'a bayan ta sake fad'ad'a fuskar ta da murmushi "Lafiya k'alau, ya kuma mantawa da mu?" se tayi murmushi kawae ba tare da tace komae ba "Toh ni ban yi zuciya dake ba, ina son zuwa gidan ku dan kuwa cikin satin nan zamu shigo Kano, kuma In Sha Allah zan zo gidan ku" "Allah Sarki na gode" Ayrah ta fad'a, dan tun dawowar ta daga A.B.U wad'annan abubuwan suka dinga faruwa, hakan ne ma ya sanya ta manta da su, amma gashi su basu manta da ita ba "Yanzu zaki tura min address d'in ne ko yaya za'ayi?" Bahijja ta tambaya "Bari na tura miki ta message.." Ayrah ta fad'a, murmushi Bahijja tayi kana tace "Toh na gode, ina jira" daga haka ta katse wayar. Seta cigaba da zama a wajen tana juya wayar a hannun ta, kamar ta bari ya dawo ta tambaye shi k'awar ta ta A.B.U zata zo, se kuma kawae ta yanke hukuncin da kan ta ba tare da tsayawa dogon nazari ba ta rubuce kwatancen tsaff cikin message kasancewar gidan bashi da wahalar kwatance, babu 6ata lokaci ta tura shi zuwa number Bahijjan.... Mhiz Innocent.... https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* Page 043 ___Dae_dae lokacin da ta ajje wayar ta koma gaban mirror ya turo k'ofar d'akin ya shigo, ta san shi d'in ne ya shigo hakan ne ya sanya bata juya ba se dae ta kasa cigaba da abinda take yi, ya kae wajen minti 1 a tsayen hannayen sa duka biyun sak'ale a k'irjin sa, yana k'are mata kallo duk da ba shi take kalla ba sannan ya soma takawa a nutse zuwa cikin d'akin, shirun da taji yayi yawa ne ya sanya ta juyowa dan ganin ko ya bar d'akin ne, dae_dae lokacin da ta juyo d'in yayi dae_dae da lokacin da ya iso dab da ita, hakan ne ya bawa jikkunan su damar had'uwa waje d'aya, se tayi saurin yin baya da k'afar ta saboda kusancin su da yayi yawa aenun, hannu ya saka ya rik'o ta gaba d'ayan ta ya sake manna ta da jikin sa sannan yace k'asa k'asa kamar baya so aji abinda yake fad'a d'in "Ina kuma zaki je?" tura baki tayi tana jin yadda k'irjin ta ke d'an bugawa "Ni fa shiryawa nake yi?" "Shiryawa kuma?" yayi maganar yana kafe ta da idanun sa gami da d'age duka girar sa guda biyun, jin tayi shiru se cigaba da k'ok'arin zamewa daga rik'on da yayi mata take ya sanya shi sake birkito ta ta kuma shigewa jikin sa "Bari na taya ki!" ya fad'a a hankali yana d'ora hannun sa kan hijab d'in ta ya fara zame shi, hannun sa tayi saurin rik'owa idanun ta sun yi rau rau ta kalle shi sannan ta girgiza kae "A'ah don Allah ni dae bana so" kafe ta yayi shima da nasa idanun kana yace "Meyasa?" shiru tayi tana cigaba da tura bakin ta, jin yana sake zame hannun sa alamar ze cigaba da abinda yake yi ne ya sanya ta fad'in "Towel ne fa kawae.." se kuma tayi shiru, murmushi yayi yana sanya hak'orin sa ya d'an ciji gefen lips d'in sa na k'asa sannan yace a hankali "Toh menene?" "A'ah ni dae fa.." ta fad'a tana sake dafe hannun sa tana kuma kallan sa da narkakkun idanun ta "Ko yaushe ya zama d'an iska haka oho?" ta fad'a akan la66an ta, dariyar da ta su6uce masa ce ta sanya ta cigaba da kallan sa cike da mamakin abinda ya saka shi yin dariyar hakan bayan ta san shi ba ma'abocin ta bane "Aou ni ne d'an iskan koh?" ya fad'a yana bin ta da wani irin kallo wanda ya tilasta mata saurin janye nata idanun tana sake kumbura baki, bata ta6a tunanin yaji abinda ta fad'a d'in ba, amma kuma ae laefin sa ne kwana biyun nan duk ya chanja ya koma wani mara kunya, seda ya sake sakin wani shu'umin murmushi a ran sa yana sak'a yanda zata kira shi komae taga dama ranar daya
Chapter 53 · 0% Book details