← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 90

Sashe 35

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wajen, se a lokacin Rk ya saki ajiyar zuciya yana lumshe idanun sa, se yanzu ya gane shirmen daya aekata na zuwa da ita asibitin nan, me ya shiga kan sa ya kawo ta nan d'in? Hannu ya saka ya bud'e Office d'in ya shiga sannan ya kulle, idanun sa akan ta lokacin da idanun ta ke a rufe tana sauke numfashi a wahalce, daga yanayin yanda ta 6ata rae kawae zaka fahimci ba dad'in baccin take ji ba, ga kuma yanda ta d'an tura red lips d'in ta gaba kamar me shirin yin kuka, seya samu kan sa da lumshe idanu na tsawon second 10 sannan ya bud'e ya k'arasa bakin gadon bayan yaja wata kujera ya zauna, duk da yanda take sake had'e jikin ta waje d'aya hakan be hana gumi tsatstsafowa daga fuskar ta ba, ya sake sauke idanun sa kan fuskar ta sannan ya maeda kan jikin ta da har lokacin ke d'auke da hijab, a hankali ya kae hannun sa kan hijab d'in, kamar me tunanin wani abun ya dakata da hannun sa a sak'ale, ya kae wajen second 30 a hakan sannan ya k'arasar da hannun nasa zuwa kan hijab d'in nata ya fara janye shi sama, be sake shi seda yazo dab da fuskar ta, se a lokacin kuma ya fara tunanin yanda ze cire shi daga wajen fuskar ta dan baya so ya tashe ta dan kuwa be shiryawa abinda ze fad'a mata ba, be kuma shiryawa rigimar ta ba, a hankali ya d'an mik'e tsaye sannan ya rank'wafa ya kae hannun sa k'asan kan ta da nufin d'ago kan nata, dae_dae lokacin data bud'e idanun ta da suka mata nauyi, se rumfar mutum kawae ta gani a kan ta, duk da yanda kan ta ke cigaba da mata ciwo hakan be hana ta sake ware idanun ta ba, duk da bata fahimci menene ba amma ta tsorata matuk'a dan haka bata san sanda ta mik'e zaune ba tana sakin k'ara, lumshe idanun sa yayi yana jin k'arar ta ta har cikin jikin sa, sanda ya ida bud'e idanun sa se nata idanun suka sauka cikin nasa, cikin wata rud'ewar ta saki k'ara tana yin baya gami da sake jan hijab d'in ta ta lullu6e kafatanin jikin ta tana sakin kuka kamar wadda aka daka, lokaci d'aya kuma jikin ta na cigaba da rawa, runtse idanun sa yayi saboda yadda yaji kan sa ya sara da k'arar da tayi har sau biyu, ya d'an dafe kan sa sannan ya bud'e idanun sa ya sauke su a kan ta lokacin da take cigaba da mak'urewa a jikin bango hannun ta rik'e da hijab d'in ta kamar zata maeda shi cikin ta, cikin karyayyiyar murya me had'e da kuka ta furta "Ina takadda ta? Meyasa baka maeda ni gidan mu ba?" tayi maganar sanda wasu hawaye masu d'umi suka samu damar zubowa akan kuncin ta, idanun sa yayi saurin janyewa daga cikin nata narkakkun idanun dake zubar da hawaye kamar an kunna famfo haka kuma sun cika taff da hawaye duk da wad'anda ke zuba, baya so tun yanzu raunin ta yaci galaba a kan sa dan haka ya d'an runtse idanun sa sannan ya bud'e su, ya d'auke su ya aza su a kan ta sanda ta cigaba da mutsu mutsu akan gadon tana cigaba da kukan ta "Me kike ci na baka na zuba Madam? Ae har yanzu yinin be k'are ba!" ya fad'a yana sakin wani miskilin murmushi.. Mhiz Innocent..... https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* Page 033 ___Ganin da yayi tana cigaba da bin sa da kallan tuhuma lokaci guda kuma tana sake kwa6e fuskar alamar koda yaushe zata iya sakin kuka ya sanya shi sake lumshe idanun sa sannan a hankali ya d'aga hannun sa dake d'auke da wani had'ad'd'en agogo ya juya mata dashi dan ta gani, bin hannun tayi da kallo dan fahimtar abinda yake nufi da hakan "Duba lokaci" ya fad'a har lokacin be d'auke hannun nasa ba, se ta sake bin hannun nasa da kallo sannan ta d'an runtse idanun ta dan har lokacin ganin ta be koma dae_dae ba, k'uri ta yiwa agogon kamar me k'irga sakannin da suke wucewa, ganin da yayi ta janye idanun ta daga kallan agogon ya tabbatar masa data gani, be sake cewa komae ba ya fice daga Office d'in, seda ya kulle k'ofar sannan ya tafi, bin sa tayi da kallo sanda ya fice d'in sannan ta dawo da kan ta kan gadon da sake kwantawa, ta k'agu ta koma gida, bata san nan d'in ina ne ba da babu shakka da kan ta zata koma gida. Wajen mintuna 20 se gashi ya turo k'ofar Office d'in ya shigo hannun sa d'auke da leda, se tayi sauri ta tashi dan tasan yanzu kam may be ya shigo mata da takaddar tane ta wuce gidan su, ganin yadda take shirin sakkowa daga kan gadon ne ya sanya shi fad'in "Kici abinci ki sha magani, sannan ki koma gidan" ya fad'a yana ajje ledar akan gadon ba tare daya kalle ta ba haka zalika fuskar sa a had'e, ji tayi kamar ta fasa ihu, ita gaba d'aya bata ta wani abinci bare akae ga magani, dan haka ta d'auke kae kamar ba taji ba, d'an d'aga kae yayi ya saci kallan ta yadda take ta wani cic cin magani ita a lallae dole bata ji shi ba ya sanya wani murmushin gefen baki ya su6uce masa se kuma ya sake had'e fuskar sa sannan yace "Well, se kiyi ta zama anan d'in, ni kinga tafiya ta" ya fad'a yana ta6e baki gami da soma tafiya kamar ze bar Office d'in, se kuwa ta fashe da kukan tana sakkowa daga kan gadon gaba d'aya cikin kukan ta furta "Don girman Allah kayi hak'uri, bazan iya cin abinci ba, ka maeda ni gidan mu ko ka bani kud'in mota na tafi.." tayi maganar tana saka hannun ta kan fuskar ta tana goge hawayen dake ta sintiri akan kuncin ta, dakatawa yayi daga inda yake ba tare daya juyo ba har wajen second 20, seda kukan nata ya fara raguwa sannan ya juyo a nutse ta fara takawa zuwa cikin d'akin, har ga Allah ya gaji da jin kukan nan nata, d'aga masa hankali yake yi, kuma babu damar rarrashi kada yaje ta koma zargin sa ko ta hasaso wani abun nan gaba, dan haka yanzu ma be kalle ta ba yaja wata kujera sannan ya janyo abincin ya d'ora akan kujerar kana yace "Ba zaki koma gida a haka ba, dan haka ki tsaya kici abincin kawae" yayi maganar lokacin daya ida bud'e abincin, ya ajje cokali a gefe sannan yaja gefe ya tsaya yana fiddo da wayar sa daga aljihu ya shiga dannawa, seda ta gama sheshshek'ar ta ran ta na cigaba da suya, tasan taemakon ta yayi amma kuma ita bata buk'atar wani abinci dan gaba d'aya hankalin ta da nutsuwar ta sun tafi gida ne, amma kuma daga yadda yayi maganar tasan idan ba taci abincin ba ba mayar da ita zeyi ba dan haka ta k'arasa ta zauna kan gadon kana taja kujerar, ruwa ta fara d'auka ta 6alle murfin robar ta kae bakin ta, se yanzu ta tuna rabon ta da shan ruwa har ta man ta, wata irin k'ishirwa ta taso mata dan haka bata sauke robar ba seda ta shanye shi tass, sannan ta ajje tana sauke ajiyar zuciya lokaci d'aya kuma jikin ta na d'aukar rawa, lumshe idanu tayi dan gaba d'aya bakin ta babu taste amma yaza tayi? Janyo abincin tayi a hankali ta fara kaewa bakin ta tana 6ata rae, spoon na farko data fara kaewa sega hawaye sharr akan fuskar ta, haka dae ta cigaba da ci lokaci d'aya tana kae d'ayan hannun ta tana d'auke hawayen, daga inda yake yake d'an satar kallan ta gaba d'aya wani tausayin ta yazo ya lullu6e shi, seya maeda wayar cikin aljihu sannan ya k'arasa cikin Office d'in ya fara wani abun, ita sam bata lura dashi ba seda yazo dab da ita hannun sa d'auke da allura, beyi tunanin ta lura da ita ba seda yaga tayi sauri ta koma kan gadon manyan idanun ta da suka yi ja sun sake cika taff da hawaye "Idan kana k'aunar Allah kada kamin allura, naci abincin fa, ka k'yale ni don Allah" ta k'arasa fad'a tana sakin kukan gaba d'aya, lumshe idanu yayi na tsawon sakanni kafin ya bud'e su still dae a kan ta, a hankali ya shiga takawa zuwa bakin gadon, ita kuma tana cigaba da komawa baya tana girgiza kae gami dayin kukan ta kamar wadda aka riga aka yiwa allurar "Oh god" ya furta sanda ya dakata yana d'an murza goshin sa "Wannan wace irin yarinya ce?" ya furta a k'asan ran sa kafin ya sake maeda duban sa kan ta har lokacin dae ba tayi shirun ba "Ina yi miki allurar zan maeda ki gida bayan na baki takaddar ki" yayi maganar a nutse kuma cikin lallashi, ita sam ba fahimtar sa take ba wannan allurar kad'ae data gani ta gama rikita ta dan kuwa zata iya cewa tunda take da girman ta ba'a ta6a mata allura ba, ganin da yayi zata cigaba da 6ata masa lokaci ne ya sanya shi tamke fuskar sa sannan ya hau kan gadon ya zauna kana ya sanya tattausan hannun sa yana k'ok'arin rik'o ta, wani sabon kukan ta sake fashewa dashi tana cigaba da komawa baya, hannu biyu ya saka ya janyo ta gaba d'ayan ta cikin jikin sa, duk da yanda take cigaba da k'ok'arin k'wacewa tana kukan ta hakan be hana shi zagaye ta da d'ayan hannun sa ba sannan ya fara k'ok'arin zame hijab d'in jikin ta, lokaci d'aya bugun zuciyar sa ya k'aru, wani irin kasala na saukar masa, d'an lumshe idanun sa yayi kafin ya bud'e har lokacin yana jin yanda take cigaba da kici kicin k'wace kan ta, be bi ta kan ta ba kawae ya saka hannun nasa ya zame hijab d'in zuwa kan kafad'ar ta, sannan babu 6ata lokaci yayi mata allurar, k'ara ta saka sanda taji tsinin allurar ya shige ta bata san sanda ta ruk'unk'ume shi ba lokaci d'aya gaba d'aya jikin
Chapter 35 · 0% Book details