Sashe 17
Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mik'e jiki na rawa ta fice daga Office d'in, dogon tsaki yaja yana jin wani irin 6acin rae na taso masa, a hankali ya lumshe idanun sa yana sake kwantar da kansa kan kujerar.. Seda ta tsaya ta saeta kan ta sannan ta tura k'ofar d'akin nasu, dukan su suka kalle ta cikin mamakin ganin ta kamar a birkice kuma a firgice "Bahijja lafiya?" Ruks ta fad'a tana kallan ta, se tayi wani yak'e kafin ta nemi waje ta zauna tace "Lafiya mana me kika gani?" "A'ah babu komae" Ruks ta fad'a tana d'an ta6e baki "Dama ke muke jira muna tattaunawa ne akan yadda zamu tunkari Doctor Rk da k'udirin mu, idan yaso seya za6i d'aya duk wadda ya za6a kuma ragowar se suyi hak'uri.." a hankali ta zuro k'afafun ta daga kan gadon da take kae ta kalle su su duka sannan tace "Sam banga amfanin mutum mara kirki ba, wanda be san darajar d'an adam ba, ku kamar ma bakwa ganin abinda yake min" Ayrah ta fad'a dan yau sun gama kae ta bango, kullum cikin zancen sa suke amma sau 2 yana mata d'iban albarka basu ta6a nuna sun gani ba ko sun sani, dukkan su suka kalle ta yadda tayi maganar da alama abin na mata ciwo a rae, Jidda ta dafa cinyar Ayrah tace "K'awa ta mutumin nan fa in dae kabi k'a'idar sa toh zaka zauna lafiya, though dae he is not friendly but he is nice wallahi, baya son hayaniya kamar yadda bashi da hayaniya, daga zarar kin san halin sa fa shikenan babu wata matsala da zata sake faruwa tsakanin ku" ta6e baki Ayrah tayi dan ita dae ba taga inda za'a yabi mutumin ba, kuma ma meye had'in ta dashi da har zata tsaya sanin halin sa? Banda ma dae ita za tayi missing da wallahi ba zata sake zuwa ajin nasa ba in dae tasan shine ze d'auke su, kawae seta mik'e ta shige toilet, Jidda ta dawo da duban ta kan su Ruks tace "Yawwah ya kuke ganin za'ayi?" Bahijja ta ta6e baki "Nifa bana tunanin ze za6i wata a cikin mu wallahi, ina ganin kawae mu hak'ura mu bar abin a ran mu" tayi maganar tana fatan duk su hak'ura d'in su bar ta ita tayi yak'in ta ita kad'ae, shek'ek'e duka suka kalle ta kafin Ruks tayi k'arfin halin fad'in "Kee.. Akwae mummuna ne a cikin mu? Ko kuma dae ke kin sare, idan kin sare ne just tell us kinga yanzu yak'in ya rage tsakani na da Jidda" Bahijja ta ta6e baki kawae ba tare da tace komae ba, Jidda tace "Idan baki janye ba toh zamu ware rana ne muje duk cikin dabara mu isar da sirrin dake zuciyoyin mu" da sauri Bahijja ta kalle su, kallan nan irin na baku da hankali wanda bata san tayi musu shi d'in ba seda taga suna bin ta da kallan tuhuma sannan tayi k'ok'arin saeta kan ta..... Mhiz Innocent..... https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* *TITAN'S OF TALENT* Page 015_016 ___"Bahijja!" Ruks ta fad'a tana sake kallan ta sosae, seta gyara zaman ta sannan tace bayan ta saki wani murmurshin yak'e "Na'am, ehh haka ya kamata muyi kam.." daga haka basu sake cewa komae ba suka yi shiru se dae kowa da abinda yake sak'awa a cikin ransa. A hankali ta k'arasa bakin gadon ta chanja hijab d'in jikin ta da wani sannan ta kalle su su duka tace har lokacin fuskar ta ba yabo ba fallasa "Zan d'an je na dawo" ta fad'a tana shirin ficewa daga d'akin, mik'ewa Jidda tayi tace bayan ta d'auki mayafin ta "Muje na raka ki.." kamar tace ta barshi se kuma taga kamar hakan be dace ba dan haka seta dakata ta jira Jiddan har ta k'araso inda take suka fita tare. Ba laefi yanzu suna tafiyar suna d'an ta6a hira, hirar da se Jidda ta d'auko ta sannan Ayrah kan amsa mata har zuwa sanda Jiddan tace "Ina zamu je wae?" "Mango zan siyo.." harara Jidda ta jefa mata sannan tace "Amma shine baki fad'a min ba, toh ae mun wuce wajen masu siyarwar" "Aou mantawa nayi" ta fad'a tana dariya gami da sanya hannun ta akan bakin ta, daga haka suka juya Jidda ta kae su wajen da masu saeda fruits suke sosae, kae tsaye wajen me mango d'in suka je, Ayrah ta fad'a masa adadin data ke so, shi kuma ya fara zuba mata cikin leda. A hankali wata bak'ar had'ad'd'iyar mota ta gangara ta tsaya kusa da me siyar da mangon, su biyu ne cikin motar Rk zaune a wajen me zaman banza yana danna waya, yayin da Yaseer ke driving, kallan sa yayi sanda yaga yayi parking motar a wani waje daban, da mamaki yace "A'ah meye haka?" Yaseer yace "Fruit zan d'an siya, sun min kyau gaskiya.." "Oh god, ji wani kuma" Rk ya fad'a yana watsa masa harara, Yaseer yace "5 min pls.." ya fad'a sanda yake bud'e motar yana kuma d'aga hannun sa, Rk bece komae ba se d'aga kafad'a da yayi gami da ta6e baki lokaci d'aya yana maeda kansa kan wayar sa, wajen minti 2 da fitar Yaseer d'in, a hankali ya d'aga manyan idanun sa ya kalli wajen, acan ya hango shi tsaye wajen me siyar da mango yana ta zuba shi da me mangoron, seya samu kansa da jan tsaki gami da furta "Yaseer!!" ya fad'a yana shirin d'auke kansa idanun sa suka sauka akan fuskar ta sanda wani sassanya kuma kyakykyawan murmushi yake tashi akan fuskar ta wanda ya matuk'ar k'awata kuma ya sake fito da aenahin kyawun ta, cikin en sekonnin da basu wuce 2 ba yaji yanayin bugun zuciyar sa ya sauya wanda har be san sanda ya rintse idanun sa ba yana sanya hannun sa saetin zuciyar sa, seya maeda kansa jikin kujera yana sake lumshe idanun sa kafin a hankali ya fesar da wata iska daga bakin sa "What happen to me?" he asked him self still dae idanun sa suna a lumshe haka zalika hannun sa dafe da k'irjin sa, yafi minti 2 a haka kafin bugun numfashin sa ya fara komawa dae_dae, dae_dae lokacin kuma da Yaseer ya bud'e murfin motar ya shigo, da mamaki ya kalli Rk da har lokacin be bud'e idanun sa ba yace "Rk.. Lafiya?" se a lokacin ya shiga bud'e idanun sa dake d'auke da dogayen bak'in gashin idanu masu matuk'ar kyau sannan ya sauke su kan Yaseer yace muryar sa a d'an ciki "Babu komae.." "Sure?" seya jinjina masa kae kawae yana sake lumshe ido, shi kansa ba zece ga dalilin da yasa yaji bugun zuciyar sa ya chanja tafarar d'aya ba "Ohk.." Yaseer ya fad'a yana kunna motar ya fara driving, seda suka yi nisa da fara tafiyar sannan Yaseer ya kalli Rk kana ya maeda duban sa kan titi yace "Ina tunanin gobe zan koma Kano fa.." "Saboda?" Rk ya fad'a bayan ya d'an kalle shi "Madam ta matsa wallahi, ni kuma bansan 6acin ran ta, so dole na koma a goben gaskiya" murmushi Rk yayi wanda ya sake fito da aenahin kyansa kana yace bayan yaja k'aramin tsaki "Idan ba kayi haka ba ae bazan gane kae ne ba" "Me kuma nayi?" Yaseer ya fad'a yana dariya, shiru Rk ya masa dan yasan dama da biyu yayi maganar "Mutumi na kae ma ka daure kayi auren nan wallahi.." kafin ya kae ga k'arasawa Rk yace "Bismilllahi.., pls wae kae baka gajiya da zancen nan ne? Ka dae san bazan k'ara shekarun da nayi a baya ba tare da nayi aure ba koh?" "Yawwah mutumi na yanzu kace dae na fara shiri kenan?" Yaseer ya fad'a duk da yayi mamakin jin zancen Rk d'in "Kamar haka kake so na fad'a koh? Toh ae gashi nan na fad'a maka" Rk yayi maganar cikin basarwa, tsaki Yaseer ya ja yana fad'in k'asa_k'asa "Ae seka yi ta zama" duk da ya ji shi amma bece masa komae ba ya cigaba da danna wayar sa.. .... Da sallama ya shiga cikin parlourn, Mummy dake zaune kan kujera ta taso tana fad'in "Sannu da zuwa likita, ka dawo lafiya?" murmushi yayi kana yace "Lafiya k'alau Mummy, Daddy fa?" "Be shigo ba tukunnah" seya jinjina kae kawae, can ya jiyo Mummyn na fad'in "Ka dad'e da shigowa ne?" d'an ta6e baki yayi kana yace bayan ya girgiza kae "Nop, ban wuce 1 hour ba.." "Ohk bari Muneerat ta kawo maka abinci yanzun nan" seya d'an yi shiru kad'an, baya son Mummyn ta dinga had'a harkar sa da yarinyar ballantana har suyi tunanin wani abun, se dae 'ya 'ya ce, ko yaya ya nuna baya son hakan yasan ba zata ji dad'i ba, so ko dan kulawar Mummyn a gare shi ya sanya ya dinga d'auke kae akan wasu abubuwan, dan haka bece komae ba ya wuce dinning area, ya ja kujera ya zauna bayan ya ciro wayar sa daga cikin aljihu ya fara dannawa. Wajen mintuna 10 da zaman nasa, wata madaedaeciyar budurwa er kimanin shekaru 22 ta fito daga cikin kitchen sanye cikin riga da skirt na atamfa wanda suka yi cif cif a jikin ta, se dae kasancewar haka take a tsaye yasa kayan basu wani mata kyau ba sun dae yi mata cas cas kamar a jikin ta aka d'inka, daga fuska babu laefi tana da nata kyan dae_dae misali, bak'a ce se dae ba can ba, amma saboda man da take shafawa yasa fuskar ta ta ta fito tayi haske sosae kuma take wani irin shek'i, sannan kuma doguwa ce babu laefi, kan ta babu d'an kwali se wata hula data saka ta zame ta har wajen rabin kan ta, wanda ya fito da kusan rabin kitson attach d'in dake kan ta, a hankali ta k'arasa ta ajje cooler data d'auko sannan ta koma ta kwaso ragowar kana ta dawo taja kujera ta zauna tana kallan sa cike da matsananciyar k'aunar sa tace "Sannu da zuwa Yaya na" se a lokacin ma shi yasan da wanzuwar ta a wajen, ya d'an d'aga kan sa ya kalle ta da kyawawan manyan idanun sa sannan ya d'auke, seta lumshe idanun ta tana jin idanun nasa kamar wani abu ne a cikin su wanda ya sanya