Sashe 82
Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
takaddar ta, bayan shi ne ya had'a su. Da sauri Abbu ya d'auki wayar yace "Abbakar meye haka ne? Meye na shiga tsakanin ma'aurata? Ka rasa a'ina zuciyar taka zata yi amfani se akan d'iyar ka?" Abbu ya fad'a duk da shi d'in ma ya girgiza da al'amarin Muneerah ya kuma tsorata da ita aenun. (Idan sunan Daddy da na saka a farko ya bambamta da wannan toh amin afuwa, walle na manta wane suna na saka a farkon "Don Allah ka bari, ina so ne nayi aeki kamar yadda ya kamata ace kowanne mutum me adalci yayi, idan er mu ce hakan ya faru da ita kana ganin zamu k'yale ne? Idan ita Muneerahn wata ta yiwa haka zamu bari ne wadda ta aekata mata taci banza? Abin da ya sa kenan nake so nayi k'ok'ari na kuma danne son zuciya ta nayi abin da ya dace kafin en uwar yarinyar suyi abin da ya dace su ma." "Shi ne kuma kake so ka raba auren?" Abbu ya fad'a dan so yake shi ma a kowanne 6angare yayi adalci, tabbas ba dan er d'an uwan sa bace Muneerah shi kan sa hukuncin da ze umarci Rk d'in yayi kenan, dan cigaba da zama da me halin Muneerah hatsari ne, se dae baya so zumuncin su ya 6aci, baya so akan wannan dalili zumuncin su ya lalace. "Ba dan wani abun nake so yaron nan ya sake ta ba se dan ta koyi hankali, kuma ni bance yayi mata sakin da ya wuce 1 ba, se dae kuma idan shi ne yayi ra'ayi yayi hakan dan kuwa ta cancance shi. Ina so ya mata saki 1 dan ta dawo hayyacin ta, ta san menene rayuwa, ta kuma san halin ta bana zama a gidan miji ba ne, idan da wani ne ma ba d'an uwan ta ba tana tunanin zuwa yanzu tana cikin gida ne? Kae kan ka ka sani Yaya se dae ta tsinci kan ta wajen en sanda. Ni uba ne, har abada babu uban da ze so ganin er sa na zawarci, se dae wannan d'in za'a yi shi ne da niyya me kyau, ya bar Muneerah ko da ze maeda ta toh se zuwa lokacin da zata gane menene aure, menene kuma kishi, sannan kuma se ta koma Islamiyya!" Shiru Abbu yayi yana nazarin maganar Daddyn, duk se yaji tausayin Daddyn ya kama shi, se dae shi kan sa yayi na'am da abin da ya fad'a d'in ko dan Muneerahn ta sake hankali da sanin ya kamata, shi kan sa be san rashin imanin ta ze iya bata tayi kisa ba, se a yanzun da ta aekata hakan, duk se yaji danasanin abin da yasa tun farko suka yi maganar had'a su aure, kuma hankalin su be kwanta ba se da suka ga anyi auren, se gashi Muneerahn ta watsa musu k'asa a ido. Mik'awa Rk wayar Abbu yayi ba tare da yace komae ba, dae_dae lokacin da Daddy yace "Ka turo ko d'an aeke ne ya kawo mata takaddar se tafi fahimta, ta kuma fi shiga hankalin ta" Daga haka ya katse wayar. Duk jikin sa se yayi sanyi, lallae wannan d'in babban abu ne, tunda har Daddy da kan sa ya bud'i baki yace a saki Muneerah, ko da yake komae son da mutum ke yiwa Muneerah yaji abin da ta aekata se ta sire masa. Maganar Abbu ta katse masa tunani sanda yake fad'in "Ka rubuta mata saki 1, sannan ka tabbatar zaka maeda ta idan har tayi hankali, ta kuma shiryu musamman akan abin da ta aekata na k'ok'arin hallaka wata halitta.." Kallan Abbu dake maganar yayi fuskar sa a raunane, daga nan be sake cewa komae ba ya fice daga Office d'in, Ummee ta rufa masa baya. Bin su da kallo Rk yayi tabbas Muneerahn ta basu kunya, ta wulak'an ta su, ta kuma nunawa duniya ilimin addinin ta ragagge ne. Ya sauke ajiyar zuciya yana janyo takadda da biron dake ajje kan kujera. Shiru yayi na en wasu sakanni, tabbas ba dan abin da Muneerahn ta aekata ya wuce misali ba, ya wuce abin da be ta6a tunani ba har abada baze ta6a sakin ta ba, musamman a yanzun da zuciyar sa ta soma kar6ar ta, se dae bisa abin da ta aekata cikin lokaci k'ank'ani ta fice masa fitt, ta sire masa gaba d'aya, ta kuma bashi tsoro da mamaki. Kawae se ya d'auki biron cikin hannun sa ya soma rubutu da had'ad'd'en rubutun sa kamar na mace me kyau da tsari. Cikin lokaci kad'an ya ida rubuta takaddar ya ninke ta lokaci d'aya yana d'an runtse idanun sa cike da tausayin Daddy, wanda yau d'in ya nuna masa shi d'in uba ne na gari. Mik'ewa yayi yana jefa takaddar cikin aljihun gaban rigar sa kana ya soma takawa dan ficewa daga cikin office d'in.. Ayi haquri da abin da aka gani, ina bin yadda Alqalamin ya tafi da ni ne kawae.