← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 90

Sashe 51

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

magana ba saboda abinda ya aekata "Lallae baka da kunya, kana so in shigar da kae k'ara akan abinda ka aekata?" ya d'an dakata sannan ya d'ora da "Stay away from our life, otherwise wlh i will sue you, kasan kuma me ze biyo baya.." ya k'arasa maganar cikin zafi, se kuma ya d'an yi shiru kana yace "Maganar kud'i kuma, bama buk'atar kud'in kowa wanda Ayrah zata yi amfani da shi, kae ma tayi amfani da naka ne bisa rashin sani, saboda haka kada nan gaba ka cigaba da tunanin ka ta6a taemaka mata a rayuwar ta wanda hakan zesa ka ta6a goran ta mata, dan haka ka bani Account number ka zan tura maka kud'i, ka d'auki adadin kud'in da kasan ka kashe mata tun daga farko har k'arshe, ragowar kuma kayi amfani dasu wajen yin nesa da wannan iyalan, hope u get it.." tunda ya fara maganar har ya gama Alhaji Mato bece komae ba, yayi shiru yana saurarar sa, takaeci gami da borin kunya suka had'u suka kama shi, be ta6a tunanin akwae wanda ze iya biyawa Abban kud'in nan ba, shiyasa yayi amfani da wannan damar dan ya tozarta kuma ya wulak'anta Abban se gashi hakan be yiwu ba, saboda haka abinda ya kamata ya fita daga rayuwar tasu kada allura ta tono garma. Ba shi ya bar k'ofar gidan ba seda ya bawa Rk account number sa sannan yaja tsummar k'afafun sa ya bar layin cike da takaecin rashin samun damar tozarta Abba. Kallan sa Abba yayi sanda Alhaji Mato yaja motar sa ya bar layin "Allah ya saka maka da alkhaeri" wata irin kunya ce ta kama Rk, dan tunda ya gano abinda Abbun sa yayi duk wani kud'i da zeyi amfani dasu gani yake kamar na Abban ne, yanzu ma se yake gani kamar Abban da kan sa ya biya kud'in dan haka abinda ya furta kawae shine "Abba Umma na ciki?" "Eyyah ta d'an fita ne, amma ba tayi nisa ba" "Toh a gaeda min da ita" "Zata ji In Sha Allah" Abba ya fad'a yana cigaba da kallan Rk, seda ya d'an sake yin shiru kamin yace "Bari na koma Abba.." "Toh shikenan, ka gaeshe ta" "In Sha Allah" Rk ya fad'a yana yin gaba, Abba ya bishi da kallo yana jin k'aunar yaron har cikin ran sa, halin su sam ya banbanta dana mahaefin sa, Allah kenan me halitta, bashi ya koma cikin gidan ba seda Rk ya tashi motar sa ya bar wajen sannan ya sauke ajiyar zuciya ya shige cikin gidan. ... A nutse ya tura k'ofar d'akin idanun sa akan gadon cike da fatan har lokacin bata tashi ba, addu'ar tasa taso ta kar6u dan kuwa bata dad'e da tashi daga baccin ba, fitowar ta kenan daga toilet sanye cikin doguwar riga da Baby hijab daya zarce k'irjin ta da kad'an, hannun ta na kan fuskar ta tana goge ruwan dake kan fuskar ta ta, dae_dae lokacin daya shigo ta sauke hannayen ta wanda hakan ya bayyana kyakykyawar fuskar ta da tayi wani fayau, se dae hakan ba k'aramin sake fiddo da aenahin kyawun ta yayi ba, manyan idanun ta suma sunyi zuru_zuru sun sake haske da girma, ganin irin kallan da yake bin ta da shi ne ya sanya ta saurin d'auke kae tana neman waje ta zauna, ta rasa gane dalilin da yasa har yanzu ta kasa sakin jiki da shi kamar da, ta kasa komawa asalin Ayrahn ta me k'aunar Rk, haka kawae seta dinga masa kallo kamar bak'o wanda take jin kunyar sa. A hankali ya shiga takowa zuwa cikin d'akin, ya nemi waje ya ajje ledar hannun sa sannan cike da sassarfa ya k'arasa inda take, dan yadda ta masa kyau d'in nan zuciyar sa ba zata huta ba idan be ji ta a jikin sa ba, hakan ne yasa yana k'arasawa babu 6ata lokaci ya saka hannayen sa duka biyu ya kamo kafad'ar ta ya mik'ar da ita tsaye, sannan ya zuba mata k'wayoyin idon sa, kasa d'aga nata tayi ta kalle shi se shirun da tayi kawae ta kasa furta komae, shima bece komae ba se jan ta da yayi cikin jikin sa yayi mata kyakykyawar runguma lokaci d'aya yana lumshe idanun sa sannan ya zagaye ta da duka hannayen sa, shiru tayi lokacin da zuciyoyin su ke harbawa kamar zasu fito, seta samu kan ta da lumshe nata manyan kyakykyawan idanun tana jin wata nutsuwa na saukar mata lokaci d'aya kuma wani rauni na tarar mata, sun kae wajen minti 1 a haka yana sake jin yanda d'umin jikin ta ke ratsa shi sannan ya sake ta a nutse kana ya bud'e idanun sa da suka d'an sauya, ajiyar zuciya ya ajje kana ya ja hannun ta ya k'arasa da ita k'asan carpet d'in d'akin ya ajje ta sannan ya koma shima ya zauna gami da tank'washe nasa k'afafun yana cigaba da kallan ta, ita kuma tak'i d'ago nata idanun ta kalle shi, murmushi yayi kana ya janyo ledar ya ajje ta a gaban ta sannan ya fara fito da kayan ciki, tunda ya fara fito dasu k'amshin mango ya cika hancin ta, bata san sanda tayi murmushin daya k'awata kyakykyawar fuskar ta ba lokaci d'aya kuma tana d'aga kae ta kalli hannun sa da yake fito da abubuwan cikin ledar, se daga k'arshe ya fito da ledar mangon dake cigaba da tashin k'amshi da naso a jikin ledar da alama sassanya ne, hannu ta mik'a da niyyar kar6a se yayi sauri ya janye hannun sa yace yana jefa mata wani kallo me cike da ma'anoni da dama gami da d'age girar sa d'aya "Nak'i wayon, se kin fara cin abincin" "Allah ni dae, ni dae bana ci.." ta fad'a tana d'an jijjiga jikin ta gami da tura k'aramin bakin ta, bin ta yake yi da kallo wata irin k'aunar ta na sake ratsa shi, wannan shagwa6ar ta ta na neman yi masa illa wanda ita sam bama tasan a yanda tayi maganar ba, seda ya lumshe idanun sa sannan yace cikin k'arfin hali "Shikenan bari na maeda mangon, tunda ba zaki ci ba.." ya fad'a yana shirin mik'ewa, da sauri ta rik'o hannun sa kafin ta kalle shi da narkakkun idanun ta tace kamar zata fashe da kuka "Don Allah.." "Naji.. Ki ci abincin.." ya k'are maganar yana tura mata abincin gaban ta, yanzu kam ba tayi musu ba se d'aukar spoon da tayi ta fara cin abincin a hankali lokaci guda kuma tana bin sa da kallo yadda taga yana shan mangoron kamar na shi, bin sa ta cigaba dayi da kallo, da taga dae bashi da alamar dena sha se tace "Ni dae Allah kar ka shanye min ae ba naka bane, kuma naga dae kae ma ba kaci abincin ba" ta fad'a a narke, dakatawa yayi da abinda yake ya zuba mata idanun sa sannan yayi murmushi, tunda dae yau tana biye masa tayi magana, bari ya cigaba da sanya ta maganar dan hakan ba k'aramin dad'i yake masa ba "Waye ya siyo?" "Kae ne, amma ae nawa ne" ta fad'a tun kafin ya aje maganar da yayi "K'arfin hali" ya fad'a yana jinjina kae, seda ta sake tura bakin ta kad'an sannan tace "Toh ka bani ae dae na ci" kamar ya sake jan wata maganar, se kuma ya fasa ya kalli abincin da taci dududu befi a k'irga lomomin da tayi ba, amma kuma yasan halin ta dama na k'in son cin abinci hakan ne ya sanya shi mik'a mata mangon, ta kuwa kar6a tana murmushi cike da jin dad'i, dan ba k'arya tayi missing nasa, dan kuwa rabon da ta sha shi har ta man ta, hakan ne ya sanya ta zagewa ta dinga sha a hankali cike da santi, tana sha tana lumshe ido, se ya shagala da kallan ta yana murmushi. Wajen k'arfe 4 suka fito daga Hotel d'in bayan ya saka ta ta saka k'aton hijab har k'asa, ya shigar da kayan ta backseat sannan ya koma ya bud'e mata frontseat kana ya kalle ta "Bismilllah Madam" ya fad'a cikin wani irin salo, a nutse ta k'arasa ta shiga motar ya rufe sannan ya koma driver seat ya shiga ya zauna kana ya tashi motar suka fice daga wajen. .... A karo na 3 kenan taja wani tsakin wani irin takaeci da tuk'uk'i take ji cikin zuciyar ta, ita wannan tsirfar da ishe ta, ae ba se ta girmama uwar mijin ta sannan za ta yi zaman aure ba, a bar ta taji da matsalar ta ta cikin gida mana, fizgo wayar ta ta ta sake yi sannan ta lalubo number Ummee ta danna kira kana ta kara ta a kunne, ringing 1_2 Ummeen ta d'aga "Ina kwana?" ta fad'a ba dan ta so ba, dan ita gaesuwa bata daga cikin tsarin ta kawae dae tayi ne kada ace ba tayi ba "Kina lafiya Muneerah ya gidan?" "Lafiya lau, ya mutanen gida?" Muneerah ta tambaya "Kowa Alhamdulillah, ina Raj d'in yake?" da mamaki Muneerahn ta tsaya tana jin tambayar ta ta kamar banbarakwae, kada ta nuna kamar bada sanin ta Rk d'in ya koma aeki ba mana, seda ta d'an 6ata rae sannan tace "Yana asibiti.." "Asibiti kuma? Waye ba lafiya?" Ummee ta fad'a cike mamaki itama, zuwa lokacin Muneerah ta gama fusata ji take kamar ta janyo Ummeen daga cikin waya tayi ta dukan ta, da k'yar tayi k'arfin halin fad'in "Ae ya koma aeki.." ta fad'a muryar ta a cushe "Shi Raj d'in ne yace miki ya koma bakin aekin sa?" Ummee ta fad'a cike da mamakin maganar Muneerahn.. Mhiz Innocent.... https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* Page 042 ___"Ehh tun d'azu ma ya fita" Muneerahn ta fad'a cike da k'osawa da tambayoyin Ummeen "Ina zuwa" Ummee ta fad'a tana katse wayar, tsaki Muneerah taja tana jefar da wayar ta kan gadon, ita kad'ae ta san takaecin da take ji a cikin zuciyar ta musamman idan ta tuna yau d'in ba'a gidan ze kwana ba, ba zata sake ganin da ba se gobe, amma babu komae goben idan ya dawo ba zata ta6a barin sa ba ko menene kuwa zece ko kuma zeyi a d'akin sa zata kwana, dan kuwa ta gaji, dan ita sam
Chapter 51 · 0% Book details