Sashe 75
Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wanka da kuma na tsuguno, ki fara amfani da su tun yanzun" Kasa d'aga ido Ayrah tayi ta kalli Umman, kunya kamar wajen ya tsage ta shige. Lura da hakan da umma tayi ne ya sanya ta yin murmushi kan tace "Ya fad'a miki sanda zasu dawo?" Se ta girgiza kae da sauri ba tace komae ba, Umma tace "Toh tashi dae yanzu kiga abin da za'ayi" Umma ta fad'a tana mik'ewa, da sauri Ayrah tace "Umma..!" ta fad'a tana tura baki. Ba tare da Umma ta kalle ta ba tace "Tashi kawae" mik'ewar tayi umma ta tasa ta a gaba zuwa toilet. A ranar Umma bata k'yale Ayrah ba se da ta gyare ta tass da abubuwan k'amshi, ita kuwa se nok'ewa take yi amma Umman tayi kamar bata san ma tana yi ba. Cikin k'ank'anin lokaci kuwa ta soma zuba k'amshi me d'an karen dad'i da sanyin k'amshi, ita kan ta seda taji sauyi a cikin jikin ta. .. Tun daga wannan rana ya kasance Umman ta ware kwanaki 3 ta gyare d'iyar ta ta ciki da waje, tun Ayrahn na nok'ewa har tazo ta hak'ura dan taga alamar Umman ba fasawa zata yi ba. .. Basu dad'e a Zarian ba suka d'auko hanyar dawowa bayan komae ya dae-dae ta, kae tsaye Abbu gida ya wuce yayin da Rk ya wuce gidan su Ayrah dan d'auko ta duk da tare yake da Muneerah. A k'ofar gidan yayi parking na motar sa yana jin zuciyar sa wasae, duk wata damuwar sa tana neman kauwa tun be yi arba da ita ba. A nutse ya juya ya kalli Muneerah dake zaune a wajen me zaman banza yace "Zaki shiga ne?" Ga mamakin sa se yaji tace "Idan dae har kace naje ae se naje" ta fad'a a hankali. Sam se yaga ma yanayin beyi mata kyau ba amma be bi takan hakan ba yace "Bar shi kawae, sauri nake yi yanzun kada mu dad'e" yayi maganar yana bud'e k'ofar, se da tayi murmushi sannan tace "Toh a fito lafiy a, a gaeda mutanen gidan" be tanka ba se bin ta da yayi da kallo kawae yana mamakin abin da ya chanja ta haka, amma ya san hakan na da nasaba da zuwa gidan da tayi ne. Ta6e baki yayi yana d'aga kafad'a dae-dae lokacin da ya isa kofar gidan. .. Da sallama suka shiga cikin gidan shi da Yah Sadeeq, Umma dake zaune a tsakar gidan ta amsa sallamar, murmushi ne ya wanzu akan fuskar Umman sanda suka ida shigowa cikin gidan "Sannu da zuwa" ta fad'a tana tashi daga kan tabarmar ta koma kan kujera. "Yawwah Umma" ya fad'a yana neman waje ya zauna akan tabarmar da aka masa masauki. Se da ya zauna sannan yace "Barka da wannan lokacin" "Barkan ka dae , kun dawo lafiya?" Umma ta fad'a har lokacin da murmushi akan fuskar ta "Alhamdulillah" daga nan suka d'an sake gaesawa kafin yace "Abba baya nan?" "Ehh ya d'an fita ne" Umma ta fad'a tana mik'ewa sannan ta d'ora da "Bari na taso ta ina ga bacci take" Umma ta fad'a ba dan tana buk'atar jin amsa daga bakin wani ba. Aekuwa akan gadon ta same ta idanun ta a lumshe, Umma ta k'arasa tana fad'in "Ayrah" bud'e idanun ta tayi da sauri saboda yadda ta ji kiran dan bacci ya fara d'aukar ta "Tashi ki fito ku tafi" se da ta 6ata fuska sannan tace "Kae Umma wae har ya zo?" girgiza kae Umma tayi sannan tace "Ehh, tashi kada ki 6ata lokaci" mik'ewa tayi ta k'arasa ta d'auki mayafin doguwar rigar dake jikin ta ta saka sannan ta juyo kawae se ta rungume Umman, itama Umman rungume ta tayi dan ba shakka zata yi missing d'iyar ta ta. "Zan yi kewar ki Umma ta" "Nima haka Auta" Umma ta fad'a a hankali sannan ta d'ora da "Bana so naji wani tashin hankali ya had'a ki da abokiyar zaman ki, bana so naji mijin ki na k'arar ki akan zaman ki da kishiyar ki kin ji koh?" "Tohm Umma" Ayrah ta fad'a tana tashi daga jikin Umman. Tare suka fito zuwa tsakar gidan, cikin sa'a idanun ta suka soma sauka a kan sa, bata san sanda ta lumshe idanun ta ba tana jin wani irin sanyi da kuma kewa na ratsa ta, se ta kasa d'auke idanun ta a kan sa dan gani tayi kamar ma an k'ara masa kyau ne. Shi kuwa tun d'azu yake son kallan ta amma gudun kada Umma ko Yah Sadeeq a cikin su wani ya gan shi ya sanya be yi hakan ba har seda yaji Yah Sadeeq yace "Bari na raka ku" se a lokacin ya mik'e shima kafin ya d'an risina yace "Toh Umma mun tafi, a gaeda Abba" "Toh ku gaeda gida, Allah ya kad'e fitina" "Ameen" suka amsa kusan a tare ban da Ayrah da ta bi bayan su. Har bakin motar Yah Sadeeq ya raka su sannan yace yana kallan Ayrah "Toh Auta a gaeda gida Uhmm?" seda tayi murmushi itama kana tace "Tohm Yah Sadeeq" daga haka yayi musu sallama ya koma cikin gida. A karo na barkatae ya sake d'aga idanun sa ya kalle ta, duk da yanda idanun ta suka d'an fad'a hakan be hana bayyanar kyawun ta ba da ze iya rantsuwa ya k'aru shi fiye da da, se ya saka hannu ya bud'e mata k'ofar gidan baya, ta shiga ta zauna sannan ya rufe yana aeka mata da wani sassanyan murmushi, kana ya koma driver seat ya zauna. Tun kafin ta ida gyara zaman ta ta jiyo muryar Muneerah na fad'in "Tun da baki gaeshe ni ba ni bari na gaeshe ki, Ina wuni?" da mamaki ta kalle ta se dae hakan be hana ta furta "Aou, ina wuni?" ta fad'a tana d'an murmushi tun da ta san Muneerahn ta girme mata. "Alhamdulillah" Muneerah ta fad'a tana gyara zaman ta. Ya tashi motar suka bar k'ofar gidan. .. Dukan su da mamaki suke kallan gidan da ya kawo su d'in, dan kuwa ba gidan da suka baro bane wannan d'in, shima be tanka musu ba har zuwa sanda suka k'arasa cikin gidan, yayi parking a k'aton parking space d'in da ka iya lamushe motoci da dama, se a lokacin ya juya ya kalli Muneerah da kuma ita kan ta Ayrah yace bayan murmushi ya wanzu akan kyakykyawar fuskar sa. "Wannan ne sabon gidan ku, kowacce ta d'auki part 1, zan je asibiti zuwa anjima zan dawo In Sha Allah" yayi maganar yana bud'e k'ofar ya fita, cike da zumud'i da kuma farin ciki Muneerah ta bud'e side d'in da take zaune ta fita tana kallan gidan da ya gaji da had'uwa kamar ba'a k'asar nan ba, se a lokacin Ayrah ma ta bud'e k'ofa ta fito itama. Kusan a tare suka jera zuwa aenahin inda parts 2n suke, kafin kowa ya ankara se ganin Muneerah yayi a bakin part d'in da ke na farko tana k'ok'arin bud'ewa da mukullin da ke a jiki, ya juya ya kalli Ayrah da itama gidan ya matuk'ar burge ta yace bayan yayi murmushi, "Ki k'arasa na ki, yanzun ina sauri ne Uhmm?" jinjina kae tayi kana ta bud'e bakin ta a hankali tace "Toh Allah ya tsare" da "Ameen" ya amsa, tayi gaba yayin da shi kuma ya koma wajen motar sa, ya hau ya ja ta ya bar gidan yana Allah Allah ya gama abin da yake ya dawo cikin gidan. A nutse ta cigaba da takawa zuwa cikin gidan, har lokacin da ta k'arasa zuwa cikin d'akin da ya gaji da had'uwa, kyau iya kyau, aji iya aji, se ta shagala da kallan d'akin dan babu k'arya ya had'u, a nutse ta cigaba da takawa tana kallan ko ina na cikin d'akin gwanin birgewa. Kamar daga sama ta jiyo sallamar Muneerah a cikin d'akin na ta, se ta juya cike da mamaki tana kallan ta kamin ta amsa sallamar, se dae ta dakata a inda take tsaye. Murmushi Muneerah tayi tana k'arasowa cikin d'akin tace "Ae ina ga bamu ga ta zama ba, wannan gida haka, ya kamata ace mun d'an zagaya mun ga ko'ina koh?" Murmushin yak'e Ayrahn tayi a ran ta tana raya yadda Muneerahn ke k'ok'arin gwada mata duniyanci, a fili tace "A'ah, ki je kawae idan na shirya zan fito" "Ahh idan kuwa kika yi haka baki kyauta min ba Uwar gida, tun ina Zaria nake ta rawar jikin mu dawo Kano na nuna miki na chanja bayan fad'an da Mummy na ta min, amma da haka zaki saka min?" Muneerah ta fad'a fuskar ta a dame kamar gaske, yayin da a zahiri tana bin hud'ubar Mummyn ta ne da ta gama jik'uwa da ita. Cikin er basarwa Ayrah tace "Ba kamar haka ba ne, kawae dae ina ganin ki je d'in na gode" tayi maganar tana soma takawa dan shigewa wani d'aki da ke cikin parlourn. Da sauri Muneerah ta sake fad'in "Shikenan, amma ki sani ko da ze yi k'orafi akan rashin zaman lafiya ba laefi na bane, tunda gashi na zo har cikin d'akin ki kin wulak'anta ni, ba dan na rok'i wani abun a wajen ki ba dan kawae nace mu zagaya gidan mu gani ba cewa nayi mu fita waje ba, meye laefi na anan?" dakatawa Ayrah tayi daga inda take tsaye, se ta ji kamar idan ta biyewa son ran ta bata kyauta ba, tun da dae cikin gidan ne ba wani wajen ba, se kuma idan ta ga dama ne sannan zata yi mata magana hakanne ya sanya ta juyowa tace "Shikenan" Ajiyar zuciya Muneerah ta sauke tana fad'in "Yawwah toh ko ke fa, ae kin ga ma soma sabawa ma" tayi maganar tana yin gaba yayin da Ayrah ta rufa mata baya ba tare da tace komae ba. A hankali suke takawa zuwa cikin k'atuwar harabar gidan da aka k'awata ta ta kuma k'awatu matuk'a, shiru duk suka yi babu wadda ke cewa komae, ita Muneerah so take ta tuno wani abun da zata fad'a kada tafiyar ta zama babu wani armashi har su koma, hakan ne ya sanya ta fad'in "Ni dae gidan nan ya min gaskiya, ke fa?" ta fad'a tana kallan Ayrah, murmushi kad'an Ayrah tayi