Sashe 85
Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da idanun sa sannan yace "Toh ko dae..?" Kallan sa tayi sosae tana jiran taji abin da zece, se dae kuma taji yayi shiru hakan ne ya sanya ta fad'in "Me..?" Murmushin ya sake yi a ran sa yana sak'a yadda ze rabu da ita be fad'a mata ba, dan wannan sakarcin nata birge shi yake yi, dan haka yace "Ehh toh kawae ki dena cin abincin koh?" ya fad'a a ran sa yana dariyar mugunta, dan a yadda take cin abinci yanzun ya san ba zata ta6a zama ba tare da abincin ba, se ji yayi tace "Ehh" tana murmushi. ... Washe_gari wajen k'arfe 7 suna kwance kan gadon, tana cikin jikin sa saboda yau d'in ba inda zeje, waya yake dannawa yana sane yak'i tashi so yake yaga iya gudun ruwan ta. A hankali ta shiga zame jikin ta daga na sa, se ya sake rik'o ta yana maeda duban sa kan ta yace "Ina zaki je?" Se da ta yamutse fuska sannan ta tura bakin ta gaba, kamar baza tace komae ba se kuma tace "Yunwa" tayi maganar tana shafa cikin ta. Dariya yayi kana yace "Naji kuma kin ce kin dena cin abinci?" "Toh ae dae ciki na ne!" Tayi maganar tana d'auke kae gami da sake tura baki. "Iyeee!!" ya fad'a yana bin red lips d'in ta da kallo, lura da hakan da tayi ne ya sanya ta saurin zamewa daga jikin nasa ta mik'e ta sauka daga kan gadon, da sauri sauri ta fice daga d'akin, bin ta yayi da kallo har ta fice yana murmushi gami da taune lips d'in sa na k'asa. Ajiye wayar yayi ya mik'e ya fita daga d'akin zuwa kitchen d'in da yake da tabbacin nan ta nufa. Aekuwa anan ya same ta d'in zaune ta yanka wasu sabbin fruits d'in tana sha. K'arasawa yayi ya sark'afe hannayen sa duka biyun a k'irjin sa yana kallan ta, lumshe idanun sa yayi a ran sa yana jin tausayin ta na kama shi, yadda ya san da d'in sam bata da ci amma yanzun saboda wani dalili, dalilin kusan zamowar ta uwa yasa gashi tana cin abinci sosae babu fashi, se ma dad'i da aka samu. A nutse ya k'arasa ya zauna kusa da ita, ta kalle shi ta sakar masa murmushi, shi ma murmushin ya sakar mata. Be sake cewa komae ba har ta gama cinyewa tass ta mik'e, hannu ya saka ya janyo k'ugun ta zuwa kusa da shi, ya zamana sun samu kusanci sosae, dan kuwa tazarar dake tsakanin su bata da yawa, karan hancin sa ya soma matsarwa zuwa kan na ta bayan ya d'an rage tsayi, hakan ne yasa suka soma musayar numfashi, saboda yadda ya rik'o ta sosae kamar zata shige cikin jikin sa yasa hatta k'afar ta se da ta taka tasa, jin tana neman fad'uwa ya sanya ta saurin rik'o shi da hannayen ta duka biyun, hakan se ya k'arawa tsayuwar ta su armashi. A nutse ya soma fad'in "Kin san wani abu?" yayi maganar kamar me rad'a duk da ba'a cikin kunnen ta yake fad'a ba, girgiza kae tayi dan a yadda bakin sa ke dab da nata bata san yadda zata bud'e shi tayi magana ba. Hannun sa d'aya ya d'auko daga zagaye tan da yayi ya d'ora shi a saman marar ta yace "Babe ba laefin ki ba ne cin abincin da kike yawan yi ba, laefin Babyn mu ne!" Da sauri ta bud'e idanun ta sosae tana kallan sa duk da ba wani sosae take iya kallan na sa ba saboda kusancin da suka samu. Jinjina mata kae yayi cike da tabbatarwa wani murmushi na su6uce masa kafin a hankali yace "K'warae kuwa Babe, kin kwana biyu kina d'auke da juna biyu, ina nufin Babyn mu ne a cikin ki." Kamar wata doluwa haka ta cigaba da kallan sa tana rarrabe abin da ya fad'a d'in. Se kuma ta ciro hannun ta d'aya itama ta d'ora shi akan nasa tana jin abin da yake fad'a d'in kamar a mafarki, wae ita ke d'auke da ciki? Kuma a cikin cikin ta yake? A cikin wannan shamulallen cikin na ta yake?. Ganin yadda gaba d'aya ta rikice ta ma kasa furta komae ne ya sanya shi sake jan ta, kawae se ya had'e bakin su waje d'aya yana sake rungume ta sosae. Kusan a tare suka lumshe idanun su, kowanne na saurarar yanda zuciyar d'an uwan sa ke bugawa, duk da yanda jikin Ayrahn ke a sanyaye hakan be hana ta maeda masa da martani ba, se kuma a lokacin taji wani irin farin ciki mara misaltuwa na ratsa ta, kawae se taji wata k'walla a cikin idanun ta ta taru se dae har lokacin so take a tabbatar mata da gasken ita Ayrah ita ke d'auke da ciki. Jin da yayi har lokacin jikin ta be bar rawa ba ya sanya shi cigaba da kissing na ta a nutse, k'amshin fruits d'in da ta gama sha yanzun na k'arawa sumbatar armashi.. Daga haka se nace mu had'u a last page Mhiz Innocent... https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* Page 060 ___A hankali ya sake ta se dae har lokacin hannun sa na rik'e da jikin ta, kawae se ya d'auke ta gaba d'aya ya fito da ita zuwa cikin parlour, ya mata masauki akan kujerar d'akin kana ya zauna a k'asan kujerar yana kallan narkakkun idanun ta hadda sanya hannu akan fuskar sa kamar me tunani. Murmushi ne ya su6uce mata ta sanya hannu ta kulle fuskar ta idanun ta a rufe. Shi ma murmushin yayi kana ya saka tattausan hannun sa ya kamo na ta hannun ya sauke, be cika su ba ya cigaba da rik'e su a hannun sa kafin ya d'an dage girar sa d'aya yace "Kunyar ta menene kuma Babe?" Shiru tayi kawae tana kallan sa har lokacin tana tuna sanda yace mata tana d'auke da ciki. Bata k'arasa tunanin ba ta sake jiyo muryar sa yana fad'in "Na yanko miki wasu fruits d'in?" Ture hannun sa tayi tana tura baki tace a shagwa6e "Allah ni dae bana so." ta fad'a dan ta san tsokanar ta yake yi. Rik'o ta yayi cikin jikin sa sannan yace a saetin kunnen ta "Toh kuma me nayi?" "Ba kae ne ba!" "Ni ne nayi me?" yayi maganar cikin basarwa yana had'iye dariyar sa. "Kake tsokana ta mana." Waro idanun sa yayi kamar gaske yace "Wane ni na tsokane ki Babe, Ummun triplets." Tashi tayi da sauri tana kallan sa jin abin da yace, se kuwa tayi rau rau da idanun ta kamar zata yi kuka tace, "Wae ba d'aya bane dama?" yadda tayi maganar cike da sakarcin nan na ta ya sanya dole se da ya dara, da yaga dae dariyar ta sa sake tunzura ta take yi ya sanya shi cewa "Shikenan.. shikenan.. Na bari kin ji?" yayi maganar yana kafe ta da idanun sa, a hankali ta jinjina kae tana cigaba da hasaso 'ya'ya 3 a cikin ta. Se ta kae hannun ta ta sake d'orawa akan cikin ta kamar me son ganin da gasken 'ya'ya 3 ne, lura da hakan da tayi ne ya sanya shi yin murmushi kana shi ma ya d'ora na sa hannun akan nata yace "D'umin Babyn mu kike ji?" Se ta jinjina masa kae tana murmushi. Kan sa ya d'ora akan hannun na ta bayan ya zame nasa hannun kana yace "Nima ina so na ji." Murmushi tayi se ta ciro hannun ta ta maeda shi kan kwantacciyar sumar kan sa tana wasa da ita. "Babe yanzu kin fahimci motsin me kike ji ko har yanzu na abincin ne?" Yanzu kam dariya tayi me isar ta, aekuwa se yanzun ta gane ba abinci ne yak'i fad'awa ba, ashe shiyasa ko ta ci ko bata ci ba bata dena jin motsin, ashe mutum ke rayuwa a cikin nata. Shi ma taya ta dariyar yayi yana sake tuna yadda suke yi da ita idan ta ji motsin a cikin ta. __Bayan wasu watanni_ A cikin watannin abubuwa da dama sun faru, ciki kuwa har da soma kasuwancin da Yah Sadeeq yayi, kuma se Allah ya ba shi sa'a cikin yaddar sa komae yake tafiya dae_dae. Cikin k'ank'anin lokaci se gashi Abbu ya sakar masa komae dan da farko shi ke taemaka masa da wasu abubuwan da suka shige masa duhu ko kuma ya had'a shi da wani. ... A 6angaren Muneerah ma zuwa lokacin ta gama idda se dae abin da yaso birkita ta bayan kwanaki kad'an da gama iddar ta ta, ranar nan suna zaune ita da Mummyn ta Daddy ya shigo cikin d'akin da sallama. Duka suka amsa masa sallamar ya k'araso yana kallan Muneerah yace "Ki je parlourn bak'i, kin yi bak'o" "Bak'o?" Mummy da Muneerah suka had'a baki wajen fad'ar hakan. Jinjina kae Daddy yayi kana yace "K'warae kuwa" A fusace Mummy tace "Wae don Allah Daddyn Muneerah meyasa kake haka ne yanzu? Bayan takunkumin da ka saka mana na ko ina tare muke zuwa, ka hana azo wajen mu duk be ishe ka ba, yanzu kuma kana nufin miji ka samowa Muneerahn ne ko kuwa?" Shiru Daddy yayi na en wasu sakanni kafin yace bayan ya rungume hannayen sa a k'irjin sa. "Ki kiyaye ni wallahi, ki kiyaye ni. Muneerah 'ya ta ce, ina da damar za6a mata mijin da naga ya dace. Duk da kasancewar ta ta6a aure har yanzu bata da hankalin da zata iya za6arwa kan ta mijin da ya dace da ita ba, shiyasa na yanke shawarar za6a mata da kae na, duk da bani na kawo shi ba shi ne ya kawo kan sa kuma yayi mim. Se dae bance zan miki dole ba ki je ki gan shi idan yayi miki fine, idan be yi miki ba ki dawo ki cigaba da zama cikin gidan amma fa aure tsakanin ki da Raj ya k'are!!" Daga haka be jira sun ce komae ba ya fice daga d'akin. Bin sa suka yi da kallo dukan su kowacce cike da mamakin furucin sa, lallae Daddyn da gaske yake. K'walla fall idanun Muneerah tace "Mummy wae anya kuwa Daddy shi ne baba na?" Ture hannun ta Mummy tayi kafin ta shiga rafka salati, kana ta