← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 90

Sashe 10

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

se tarin damuwa da tunanun nuka tana ganin Abban zaune babu alamar zeyi bacci, se daga k'arshe dae ta kasa shiru tace "Kayi hak'uri Abban su don Allah kayi bacci, kada damuwa ta maka yawa.." Abba ya lumshe idanun sa, baya tunanin ko awa nawa zeyi zae iya yin wani bacci, amma dan ya kwantar mata da hankali ya sanya shi fad'in yana gyara zaman sa "Toh shikenan, yanzu zan kwanta kiyi baccin ki.." ... Wasa wasa wajen kwana 3 kenan Abban baya samun yin bacci, shi kansa besan dalili ba dan ko yayi niyyar yin baccin baya samu yazo masa, se dae kawae ya kwanta yayi ta tunani, zuwa lokacin tunani ya zama kamar wani mahad'in rayuwar sa ne dan kuwa in dae ze zauna toh fa zeyi tunanin nan ne, har kuma zuwa lokacin mamaki yak'i sakar shi, ga Kabeerun da kullum da shi yake kwana yake tashi, duk da guduwa da kud'in da Abbu yayi ya masa zafi amma be kae zafin yadda ya d'auki duk wata yadda tasa ya dank'awa Abbun ba amma daga k'arshe yaci amanar sa, ya yaudare shi, gefe guda kuma tunanin halin da zasu shiga a yanzun yake, yana ganin kamar rayuwa na gab da juya musu baya, babu sana'a, babu takaddar da ze iya zuwa ya nemi aeki, ga kud'in da Alhaji mato yake bin sa, duka tunanin sa yafi karkata nan 6arin ne "Allah ka bani ikon cinye wad'annan jarabobin" Abban ya fad'a akan la66an sa, yana jin wani irin rauni a tattare dashi.... https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* *TITAN'S OF TALENT* Page 007_008 ___Washe gari wajen k'arfe 8 na safe Abba na zaune cikin parlourn yana yin iya bakin k'ok'arin sa dan kada iyalan nasa su fahimci damuwar da yake ciki se ga kiran Alhaji Mato a wayar sa, ya kalli wayar na tsawon sakanni sannan ya d'aga ya kara ta a kunnen sa, daga can 6angaren Alhaji Mato yace "Haji Ibraheem na jika shiru kwana 2 yasa nace bari na ta6o ka" d'an numfashi kad'an Abba ya sauke sannan yace "Wallahi kuwa, nima ina ta k'ok'arin kiran ka se kuma na sha'afa, dama zuwa anjima nake so nazo wajen naka, ina so ka sake min kwantance" "Toh toh Madallah.." Alhaji Maton ya fad'a yana d'orawa da yiwa Abban kwatance, Umma ta kalle shi sanda ya gama wayar tace a nutse "Yanzu ya za'ayi da shi kenan?" seda Abba ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "Zan fad'a masa gaskiya ne, idan ya yadda da k'addara shikenan idan kuma be amince ba yace sena biya shi kud'in sa se nasan yadda za'ayi.." "Toh Allah Ubangiji yasa ma shima ya kar6i wannan k'addarar" "Ameen" Abba ya fad'a ba dan yana da tabbacin hakan ba, dan shi sheda ne akan son kud'i irin na Alhaji Maton. .. Shiru Alhaji Maton yayi har Abba ya gama masa bayanin abinda ya faru, se yayi murmushi yana girgiza kae kana ya d'aga kae ya kalli Abba yace "Haji Khaleel ni fa gani nake ko menene ya faru kae ka jawa kanka, ba sau d'aya ba ba sau biyu ba na fad'a maka na kuma baka shawara ka rabu da matar ka, farar k'afa gare ta, an kore ka daga banki, kazo ka fara teaching an dakatar da kae ka fara kasuwanci wani ya gudu da kud'in wannan kad'ae be ishe ka ka gane.." "Malam ya ishe ni haka!" Abba ya fad'a yana d'aga masa hannu idanun sa akan sa cike da zallahr 6acin rae "Aou aou toh hakane abin, wato har yanzu kae ka kasa gane Annabi ya faku koh?, toh cigaba da zama da ita, ina ga ba zaka fahimci abinda nake fad'a maka ba se ranar da kayan sakawa ma ya gagare ka sakawa.." Abba ya runtse idanun sa zafin zuciyar da yanzun ya zame masa jiki se k'aruwa yake yi, a nutse ya mik'e tsaye sannan cikin kaurin murya ya furta "Kana buk'atar kud'in ka ne ko kuwa?" "A'ah se kuma in k'i buk'ata, ina jiran kud'i na a cikin satin nan kawae" Alhaji Mato ya fad'a shima yana mik'ewa ya bar wajen, da kallo Abba ya bishi yana mamakin wannan banzan hali irin na Alhaji Maton, shikenan kuma a matsayin ka na bawa musulmi Allah baze jarabce ka ba? Da wannan tunanin ya koma gida yana sak'a da warwarar yadda ze biya Alhaji Maton kud'in sa. Sanda ya koma gidan bayan yaci abinci Umma ta tambaye shi yadda suka yi da Alhaji Maton, duk se yaji tausayin ta ya kama shi yadda wani ke ik'rarin duk dalilin tane abubuwa ke faruwa dashi, abinda shi kuma baze ta6a yadda ba kenan, dan kuwa shi musulmi ne daya yadda da k'addara me kyau da kuma mara kyau, gyara zama yayi yana kallan ta "Kada ki damu, zan san yadda zanyi in biya shi kud'in sa.." cike da mamaki Umma tace "Aou yace se an biya shi?" "K'warae kuwa" Abba ya fad'a "Ikon Allah.." Umma ta fad'a tana girgiza kae... Abba beyi k'asa a gwuiwa ba wajen d'akko motar sa ya siyar da ita ba, saboda matsalolin da take dasu yasa ba tayi wani daraja ba gata kuma dama ba babbar mota bace, seya d'auki kud'in Alhaji Mato ya bashi sannan ya rik'e ragowar a hannun sa dan amfanin yau da gobe, abinda ya tsaya masa a rae yanzun kawae shine yadda zeyi ya samu sana'a ko dan ya sanya 'ya'yan nasa a makaranta, abinda ya k'ara masa k'aemi ma akan saka su a makarantar shine.. Rannan suna zaune a cikin parlourn dukan su suna kallan Al jazeera inda Abba ke kallan labarae, Ayrah na zaune gefen Abban itama tana kallan T.Vn kamar me fuskantar abinda ake nunawa a ciki, daga k'arshe a cikin labaran aka nuno wasu d'alibae da Uniform d'in su, se kuwa tayi zumbur ta tashi zaune tana kallan Abba tace "Abba mun dena zuwa makaranta?" kallan ta Abba yayi cikin mamakin jin furucin ta, se yayi murmushi sannan yace yana shafa doguwar sumar kanta dake a bud'e "A'ah za'a sanya ku mana" "Abba yaushe?" ta sake tambayar sa, seya d'an yi shiru kana yace "Nan bada dad'ewa ba Uhmm?" "Hadda Raj koh?" ta fad'a tana murmurshi, zancen kenan dan kullum idan ba tayi maganar Raj ba toh ba Ayrahn bace "Ehh" Abba ya fad'a yana maeda duban sa kan T.V. .... Sosae Umma ta takurawa Abba akan zuwa asibiti saboda rashin baccin da yake samu, shima kansa rashin baccin na damun sa dan haka a wannan karon da tazo masa da k'orafi be musa mata ba ya shirya ya tafi asibitin, gwajin hawan jini aka fara masa, kuma tashin farko su kaga yanda jinin sa ya hau, sosae suka bashi shawarwari akan hakan da kuma magunguna, hakan ba k'aramin kuma tayar masa da hankali yayi ba, amma gudun kada hankalin Umma ya tashi yasa be sanar da ita ba, kawae yace mata an gwada shi amma basu fad'a masa aenahin abinda ke damun sa ba se result d'in ya fito, haka ta yadda da abinda ya fad'a mata d'in, yayin da shi kuma ya cigaba da shan magungunan sa ba tare daya bari Umman ta sani ba. A lokacin ne ya cigaba da fama da rashin bacci da kuma tunanin daya zame masa jiki, se kuma bugun zuciya da shima baya rabo dashi, haka wataran ze kwana a zaune, se dae da yake baya bari lokacin ya tafi masa a banza se hakan yake sakawa baya wani damuwa sosae, dan kuwa k'arin lokacin karatun Qur'an ya samu, idan dae ya fahimci bacci baze zo masa ba seya fito tsakar gidan nasu ya shimfid'a dadduma yayi ta karatu har zuwa asuba, ranar da kuma ya samu baccin se yayi baccin sosae, sau da dama Umma kan farka ta same shi yana karatu, dalilin kenan daya sanya bata damu da rashin baccin nasa ba, saboda ta riga data saba da ganin sa cikin dare yana tashi karatu, se dae tasan ya k'ara lokacin karatun, amma duk da haka bata kawo rashin samun bacci ne ya sanya shi k'ara lokacin karatun ba, tafi ta'allak'a hakan da yanayin rayuwa kawae.. Sanda Umman ta gano ciwon dake tattare da Abban ba k'aramin tashin hankali ta shiga ba, dan har kuka seda tayi, Abba ya fesar da iska daga bakin sa yana kallan ta yace "Kiyi hak'uri kiyi shiru, kada kisa nima nawa hankalin ya tashi mana" "Amma Abban su meyasa ka 6oye min?" "Toh yanzu ba gashi kin sani ba?" ya fad'a yana kallan ta, seta share hawayen fuskar ta sannan tace "Duk da kullum cikin yi maka addu'a nake, amma ko ba komae zan dage da maka addu'a akan ciwon koh?" "Toh shikenan nayi laefi amin afuwa" ya fad'a yana kallan ta da tattausan murmushi akan fuskar sa, itama murmurshin tayi duk da yadda can k'asan zuciyar ta ke cunkushe da tausayin Abban. .. Sosae Abba ya dage wajen neman sana'ar da zata rufa musu asiri, se dae har zuwa lokacin be samu ba, gaba d'aya yanzu burin sa be wuce na yadda ze samu ya sanya Yah Sadeeq da Ayrah a makaranta ba dan haka idan ya tashi tun safe ya fita baya dawowa se dare amma har zuwa lokacin be samu ba. .. "Abba wae ana sallama da kae" Yah Sadeeq ya fad'a yana Kallan Abba dake zaune "Inji wa?" Abban ya fad'a yana kallan sa, girgiza kae Yah Sadeeq yayi sannan yace "Abba bansan shi ba.." "Toh Ikon Allah" Abba ya fad'a yana mik'ewa, ya kalli Umma da itama kallan sa take yace "Bari naje.." "A dawo lafiya" ta fad'a sanda yake barin tsakar gidan zuwa waje.. Murmushi yayi sanda yaga mak'ocin sane wanda suke yawan had'uwa a masallaci, seya mik'a masa hannu suka gaesa sannan mutumin yace "Wato dama magana ce akan wani aeki, yasa nace bari na maka magana idan zaka iya toh seka fara ko ranar litinin ne.." sosae annurin fuskar Abba ya k'aru yace "Ina jin ka wane irin aeki ne?" "Aekin Company ne haka amma ba wani aekin wahala bane sosae, idan ka amince zaka iya se muje ka gani" sosae Abba yaji dad'in wannan abu dan haka cikin farin ciki yace "Toh nagode nagode sosae, Allah ya saka da alkhaeri.." "Ameen Ameen" mutumin
Chapter 10 · 0% Book details