Sashe 26
Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kawae seta juya a hankali ta fice daga d'akin dan ta bar Ayrahn ta dawo daga shock d'in data shiga, ta san dole abin ya ta6a ta aenun, bata ta6a zata ba ba kuma ta ta6a tsammani ba se gashi rana tsaka taji dalilin rabuwar Abba da Abbun Raj. Ko d'aga ido ta kalli Umman ta kasa yi sanda Umman ta fice daga d'akin, ita bama ta lura ta fita ba dan kuwa har zuwa lokacin ta kasa gasgata duk maganganun nan da Umma take fad'a ba mafarki bane "Abbun Raj fa" shine abinda ta dinga maemaetawa a cikin ran ta tana so ta hasaso fuskar sa amma ta kasa dan shekarun nada yawa, ga kuma yanayin shekarun ta a lokacin, amma tabbas idan har bata manta ba mutumin ya zo wa Abban ta a matsayin mutumin kirki, bata san menene ya had'a su ba se gashi yau Umma ta bankad'a mata komae taji dalilin Abba na cewa ba zata auri Raj ba, tabbas in dae kuwa haka ne dalilin Abban yana da gaskiya, a hankali ta shiga sauke ajiyar zuciya tana jin wani irin zafi a cikin zuciyar ta, sosae zuciyar ta ke zafi wanda har ta numfashin ta seda ya koma fita da zafi, se a lokacin taji wani kuka ya taho mata, bata hana fitowar kukan ba se kawae ta jefar da jikin ta kan gadon ta fashe da wani irin kuka, a hankali take dukan kan ta akan pillown kan gadon tana jin wata iriyar nadama da danasani na lullu6e ta, kunyar abinda ta fad'awa Abba d'azu na sake k'arawa yanayin da take ciki k'aemi, wani irin kuka take wanda ke fitowa daga can k'asan ran ta, kukan nadama, kukan danasani, kukan rashin sanin mafita, a yau d'aya taji tayi danasanin sanin Rk a rayuwar ta, meyasa ma ta san shi? Meyasa tayi silar zuwan sa wajen Abba? Meyasa ta zamo silar da Abba ya janyo mahaefin sa cikin jikin sa? Yanzu kenan itace silar komae? Itace ta janyo komae? Meyasa tayi hakan? Gani take kamar komae ya faru itace me laefi tunda ita ta kawo Rk d'in "Nice silar komae!" ta fad'a sanda take sake sakin wani kukan me cin rae "Tabbas nice sila, dan da ban san Raj ba Abba baze ta6a sanin Abbun sa ba, ni na janyo Abba ya jawo Abbu a jikin sa har me faruwa ta faru, nayi danasanin sanin ka a rayuwa ta Raj!" ta k'arashe maganar tana cigaba da kukan da har muryar ta ta fara dashewa, yau mamaki na neman kashe ta, wae Abbu ne ya cuci Abba, Abbu ne sanadiyyar tarwatsewar farin cikin su, Abbu ne sanadiyyar saka damuwa a zukatan iyayen ta, Abbu ne sanadiyyar abubuwa da dama da suka faru a rayuwar su, shi kam yanzu menene zece musu su yafe masa? A hankali ta sake komawa ta kwanta har lokacin ta kasa tsaeda kukan da take, haka zalika zafin da zuciyar ta yake yak'i raguwa sema k'aruwa da yake yi, ta rasa yadda za tayi, ji take dama zata iya janyo abinda ya faru ada ta goge komae akan alak'ar ta da Rk, da kuma ana iya tariyo baya data hana kan ta had'uwa da Rk, Yah Sadeeq ne ya fad'o mata, se taji wata sabuwar k'walla ta zubo mata, ta sanya hannu ta d'auke ta lokaci d'aya tana lumshe idanun ta, bata da k'arfin da zata iya tashi yanzu haka taje ta duba jikin sa, amma ita kad'ae tasan abinda take ji a cikin jiki rae da kuma zuciyar ta. ... "Don Allah Alhaji kayi hak'uri ka bari ko zuwa gobe ne, kaga ko hutawa ba kayi ba" Muttala ya fad'a yana kallan Alhajin daya fito daga d'akin sa cikin wata bugaggiyar shadda d'inkin babbar riga, juyawa yayi ya kalli Muttala sannan yace har lokacin be tsaya ba "Wallahi bazan iya hak'ura se gobe ba, gwara ma ka k'yale ni kawae" yayi maganar sanda ya isa motar sa, ya bud'e ya shiga sannan ya kalli Muttala yace "Zaka raka ni ne ko kuma in nemi wani?" seya girgiza kae sannan ya k'arasa ya bud'e wajen me zaman banza ya shiga ya kalle shi cike da girmamawa yace "Yalla6ae daka bari dae ko zuwa goben ne kada su fahimci wani abun!" wani kallo Alhajin ya jefa masa se kuma yayi murmushi wanda ya sake k'ank'antar da jajayen idanun sa "Tunda kaga zan yi driving da kae na kasan abu ne me muhimmanci, na kasa jurewa gwara naje ko nan sati 1 ne a d'aura mana aure idan yaso seta cigaba da karatun a cikin gida na" jin maganar da Alhajin ya fad'a ne ya sanya Muttala jinjina kae kawae, bece komae ba har zuwa sanda Alhajin ya tayar da motar sa suka fice daga gidan. A k'ofar gidan yayi parking motar ta sa, sannan ya kashe ta ya kalli Muttala da tunda suka fara tafiya har yanzu be sake cewa komae ba yace "Yi mana sallama da shi pls" seya kalli Alhajin sannan yace bayan ya girgiza kae "A'ah fa Yalla6ae kada ka manta sirikin ka ne, ina ganin gwara ka fito ko kan dakalin can ne seka zauna" Muttala ya fad'a yana nuna wani dakali dake a k'ofar gidan dake kusa da nasu Ayrah, shiru Alhajin yayi kamar ba zece komae ba se kuma can yace "Toh yanzu kae dae je ka" yayi maganar yana sanya hannun sa ya bud'e k'ofar, kusan a tare suka fito, Alhajin ya kalli wajen yana yamutsa fuska sannan ya zauna yayin da Muttala ya tsaya k'ofar gidan ya k'wala sallama, daga can cikin gidan Abba ya amsa yana mik'ewa ya zura takalmin sa ya fito daga d'akin nasa, k'arasowa yayi yana kallan Muttala ganin da yayi be shaida fuskar ba, se dae ya mik'a masa hannu suka gaesa sannan yace da d'an murmushi kan fuskar sa duk da yanayin da yake ciki a yau d'in na damuwa "Se dae ban shaeda fuskar ba" murmushi shima Muttalan yayi sannan yace "Ehh dama baka sanni ba gaskiya, ga can wanda yazo wajen ka akan wata magana me muhimmanci" yayi maganar yana nuna Alhajin dake zaune kan dakalin yana kallan wani wajen, saboda k'arancin hasken dake a wajen ya sanya Abba be iya hangar fuskar sa ba, seya dawo da duban sa ga Muttala yace "Toh ikon Allah" ya fad'a yana yin gaba zuwa wajen da Alhajin ke zaune, dae_dae lokacin da Abban ke dab da k'arasawa wajen Alhajin haske ya kawo a wani k'wan lantarki dake k'ofar gidan dake kallan nasu, hakan ne ya bawa Abba damar ganin fuskar mutumin da akace shi ke son magana dashi, cikin son sake tabbatarwa ya sake bud'e idanun sa dan ganin da gaske fuskar da yake gani ita d'in ce ko kuwa dae? Shi kan sa Alhajin kallan Abba yake with shock all over his face, se yaji gaba d'aya jikin sa ya d'auki wani mahaukacin rawa, ya had'iyi wani yawu da k'yar sannan yace bayan ya mik'a masa hannu "Kae ne mahaefin Ayrah?" Alhajin ya fad'a yana kallan Abba, a ran sa yana tuna cikakken sunan Ayrahn, tabbas da gaske shine mahaefin ta, amma dae gwara ya tabbatar ta hanyar ji daga bakin Abban, da mamaki Abba ke kallan sa jin maganar da yayi, meya kawo zancen Ayrah a tsakanin su kuma? "Meya kawo ka k'ofar gida na?" Abba ya fad'a yana kallan sa fuskar sa a d'inke tsaff, jikin sa ya sake wani sanyi wata zufa na karyo masa yace bayan yayi k'asa da muryar sa "Kayi hak'uri mu zauna sena maka bayani, wallahi ba tashin hankali ne ya kawo ni wajen ka ba" "Alhaji Mato!" Abba ya fad'a cikin er d'aga murya, a ran sa Abba na sak'a lallae duk abinda Alhaji Maton yazo da shi me girma ne "Bani da lokacin 6atawa, idan ba kada abin fad'a na shige gida" Wani yawun Alhaji Mato ya sake had'iyewa shi kan sa yana tunanin ta ina ma ze fara sanarwa da Abban son er sa yake? So na aure, ganin dae da gaske Abban yake idan bece wani abu ba ze iya tafiya ya k'yale shi ya sanya shi fad'in "Wallahi abin alkhaeri ne ya kawo ni, d'iyar ka na gani kuma ina son ta da aure shine kawae abinda ya kawo ni, kuma kada ka damu wancan lokacin akasi aka samu na fad'i magana saboda 6acin rae amma zan dawo maka da kud'in daka biya ni, kuma zan baka sana'ar da zaka dinga yi kana.... " "Dakata Alhaji Mato" Abba ya fad'a bayan ya d'aga masa hannu, zuciyar sa na wani irin zafi da jin kalaman Alhaji Maton na son zuciya "Kada na sake ganin k'afar ka a k'ofar gidan nan, kud'i kuma har abada na riga na biya ka kuma bazan ta6a kar6a ba, saboda haka kada ka sake tunanin zan d'auki 'ya ta in baka ita bayan na san wanene kae, ka cire wannan ma a cikin ran ka" daga haka Abba ya juya yana jin wani jiri jiri na d'ibar sa kamar ze fad'i, da kallo Alhaji Mato ya bishi zuciyar sa na wani irin tafasa, lallae yau ya kuma yadda Abban matsiyaci ne, be san me ake kira da arzik'i ba, har yanzu dae yana zaune cikin duhun kae, har abada ma baya tunanin Abban nada rabon arzik'i a rayuwar sa, tunda gashi yanzu arzik'in ya biyo shi har gida amma ya saka k'afa yayi fatali dashi saboda wani banzan ra'ayin sa na rik'au. Seda Abba ya shiga gida sannan Muttala ya kalli Alhaji Mato cikin mamaki yace "Yalla6ae wae dama ka san shi ne?" "Bar shashasha me k'ashin tsiya, arzik'i na kiran sa yana guduwa, wani k'aramin abu ne ya ta6a shiga tsakanin mu amma da yake zuciya ce dashi irin ta kafirae ya kasa mantawa, toh se yayi tayi ae, ba dae er sa bace na gani ina so kuma sena aure ta, dan kuwa ban ta6a ganin abu inaso ban same shi ba, kuma baza a fara akan ta er talakawa ma da ita ba, ko da amincewar sa ko babu wallahi sena aure ta.. Wuce muje.." ya fad'a yana huci sanda ya k'arasa ya bud'e motar sa ya shige, Muttala ma ya shiga, Alhaji Mato yaja motar da wani irin