Sashe 38
Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yak'i barin sa, cike da mamaki Yaseer yace "A'ah na kasa gane duk wannan abin, meyasa iyayen ta zasu ce baza ka aure ta ba? Idan ma akwae wani dalilin ina ganin kamar Abbu ne zece baza ka aure ta ba saboda wannan dalilin koh?" ya k'are maganar da sigar tambaya, ta6e baki Rk yayi, shi kan sa a wannan wajen be san abinda zece ba, be san dalilin hakan ba, da farko kamar Ayrahn na bayan sa duk da yadda iyayen su kace baze aure ta ba, se kuma daga k'arshe gaba d'aya ta juya masa baya "Amma meyasa ba zaka tambaye ta dalilin ta na juya maka baya ba?" Yaseer ya katse masa tunanin da yake yi kamar yasan abinda yake sak'awa a ransa, ajiye numfashi yayi kafin yace "Tak'i bani wannan damar Yaseer, tun farko abinda naso inji kenan a lokacin ne kuma ta birkice min, yanzu kuma bani da k'warin gwuiwar tambayar ta dalilin hakan tunda ga abinda ya faru" jinjina kae Yaseer ya shiga yi cike da gamsuwa da maganar Rk d'in amma duk da haka yace "Amma yaushe zaka sanar dasu Abbun?" seda ya d'aga ido ya kalli Yaseer d'in sannan yace bayan ya girgiza kae "Ba yanzu ba Yaseer, maganar da nake maka aure na da Muneerah rana ita yau ne, me kake tunanin ze faru idan na fad'awa Abbu maganar nan?" ya k'are maganar yana d'an ajje numfashi, shima Yaseer sauke ajiyar zuciya yayi sannan yace "Hakane kuma" ya fad'a yana jinjina kae cike da tunani a zuciyar sa ko ze samowa Abokin nasa mafita. ... Tana zaune cikin d'akin a ranta tana k'iyasta adadin lokacin da take jira ya cika ta tashi ta fita daga d'akin, wani irin bacci me dad'i ke ta sakad'ar ta tun d'azun, se yakice shi take yi ta k'arfi da yaji amma se dad'a lumshe idanu take yi kamar wadda tasha kayan maye, ko cikakken minti 1 bata k'ara ba ta 6ingire kan gadon se bacci. Sosae Rk yaji dad'i lokacin da Hameedah ke sanar dashi Ayrahn bacci take yi, dan haka ya d'an samu relief, hatta maganin ta ma bebi takan a tashe ta tasha a daren ba, a cewar sa goben seta sha tunda dae yanzu ta samu bacci, ko ba komae ze d'an samu nutsuwar zuciya kafin goben daya san me raba shi da ita se Allah. A hankali ta shiga bud'e narkakkun idanun ta da suka mata nauyi, har ta gama bud'e su tarr cikin d'akin, da sauri ta mik'e zaune tana cigaba da kallan d'akin, kallan agogon dake manne a jikin bangon d'akin wanda ya harba k'arfe 6:00 tayi, seta sake kallan agogon kamar me k'aryata abinda ta gani, se dae ga mamakin ta hakan dae ya sake nuna mata, wannan wane irin bacci ne? Bata san sanda hawaye ya soma sintiri akan kuncin ta ba, ta mik'e da wani irin sauri ta dirga daga kan gadon, sabon brush d'in data gani akan gadon ta d'auka ta fad'a toilet d'in tayi alwala tayi brush sannan ta fito tayi sallah tana istigfari cikin ran ta, bata san wane irin nannauyan bacci ne haka ya d'auke ta cikin k'ank'anin lokaci irin wannan ba, seda ta idar da Sallahr sannan ta sake fad'awa toilet d'in tayi wanka kana ta shirya yanzu ma cikin abayar data gani akan gadon ta maeda hijab d'in jikin ta ba tare data shafa komae akan fuskar ta ba ko ta shafa wani abu me kama da mae ba ta k'arasa ta ta6a k'ofar d'akin, cikin sa'a kuwa se taji ta a bud'e, sauke ajiyar zuciya tayi sannan ta k'arasa fitowa daga cikin d'akin, ba tare data kalli ko'ina ba kawae tayi hanyar fita daga cikin d'akin, daga inda yake zaune kan dinning shi da Yaseer ya mik'e da sauri dan tunda ta fito yake ankare da ita, bece da ita komae ba kawae ya k'arasa a nutse zuwa gaban ta, dakatawa tayi da sauri ganin yanda ya tsaya d'in dab da ita, Yaseer dake zaune shima ya mik'e ya bar parlourn gaba d'aya, se a lokacin ya d'aga hannayen sa ya sak'ale su a k'irjin sa sannan ya zuba mata idanun sa gaba d'aya, k'ok'arin komawa gefe ta soma yi ba tare data kalle shi ba har lokacin fuskar ta a had'e "Ina zaki je?" ya fad'a a nutse har lokacin idanun sa na kan ta, bata dae kalle shin ba se d'aga kae da tayi kawae ta kalli gefen sa sannan ta sake had'e fuska tace k'irjin ta na d'an bugawa saboda yadda ya tsare ta da idanun sa "Gidan mu zan tafi!" ta fad'a lokacin da wasu ruwan hawaye suka taru a cikin idanun ta, cike da fatan kada ya kawo wata maganar dake nuni da k'in zuwan ta "Gidan ku kuma?" ya tambaya yana d'an d'age girar sa guda d'aya yana cigaba da bin ta da wani irin kallo saboda yadda yaga ta masa wani shahararren kyau kamar ba cikin tashin hankali take ba, ba tace komae ba tunda tasan ae yaji abinda ta fad'a d'in dan haka ta sake k'ok'arin tafiya "Toh ya zakiyi da aure na kuma da yake kan ki?" "Zan fad'awa Abba na abinda ya faru, nasan zasu warware auren gaba d'aya.." ta fad'a har lokacin fuskar ta a had'e, murmushi ya saki daga inda yake tsaye sannan ya d'an lumshe idanun sa kad'an kana yace "Ohk je ki.." bata sake cewa komae ba ta sauke ajiyar zuciya sannan tabi gefen sa ta fice daga d'akin, bin ta yayi da kallo yana mamakin ta, sosae yake mamakin ta musamman idan ya tuna yanda suka fara soyayyar su hankali kwance amma rana d'aya ta sauya kamar ba ita ba, be ta6a tunanin zata ta6a juya masa baya ba, ya d'auka zata taya shi fafutuka ne da kuma nemo hanyar da zesa iyayen su su amince da auren su, se yanzu yaji inama kafin ta fita ya tambaye ta dalilin sauyawar ta? Koda yake yana da 80% sure cewar maganar iyayen ta kawae tabi yasa ta chanja masa, yasan tana k'aunar sa fiye da zaton sa, amma kuma soyayyar iyayen ta ta danne tashi, amma meyasa tun farko bata chanja ba se daga baya? Meyasa haka? Shi kad'ae yake tunanin sa kuma yasan babu me amsa masa dan haka kawae ya sauke hannayen sa sannan ya fita daga cikin d'akin, yana hango ta sanda ta fita zuwa k'ofar gidan, seda ta fita d'in sannan ya k'arasa ya hau motar sa ya jata shima ya fice daga gidan, a nutse kuma cike da takatsantsan yake bin ta a baya, baya so ta fahimci bin ta yake dan haka yake bin ta a hankali, itama a hankali take tafiya kamar wadda k'wae ya fashewa a ciki, se dae hakan na da nasaba ne da jikin ta da har lokacin take ji be koma mata dae_dae ba, a haka har ta fita titi ta tsaya tana kallan motocin da suke wucewa, se a lokacin ta tuna babu ko sisi a tare da ita, amma koma menene gwara taje gidan idan yaso seta kar6a ta bawa me Napep d'in, dan haka babu 6ata lokaci ta shiga tsare adaedaeta, daga cikin layin ya dakata da motar tasa yana ganin ta har zuwa sanda wata k'atuwar mota me kyau ta dawo da baya tayi parking a gaban Ayrah, d'an runtse idanun sa yayi yana jiran ganin abinda ze faru next, dae_dae lokacin da mutumin cikin motar ke k'ok'arin fitowa ita kuma ta gama fad'awa me Napep d'in data tara inda zata je, babu 6ata lokaci ta fad'a ciki dae_dae lokacin da mutumin ya gama fitowa daga cikin motar, wani banzan kallo Rk yabi shi da shi yana jin yanda zuciyar sa ta fara tafasa lokaci d'aya, tana shiga kuma me Napep d'in yaja, mutumin na shirin yin magana yaga yaja adaedaetar sa "Kashhh!" ya furta yana bin adaedaetar da kallo sanda suka wuce shi, se a lokacin Rk yaja motar sa ya fito daga cikin layin har lokacin yana d'an kallan mutumin yaga ko zeyi wani abun bayan nan, se dae yaga beyi ko k'ok'arin bin su ba, se a lokacin ya d'an ji sanyi sannan ya cigaba da bin ta, yana cikin driving d'in wayar sa ta soma ringing, kamar baze kalli me kiran ba se kuma ya kalla "Muneerah" shine abinda ya bayyana akan screen d'in wayar, runtse idanun sa yayi zuciyar sa na cigaba da wani irin zafi, kawae seya kae hannun sa ya kashe wayar gaba d'aya sannan ya jefa ta kan kujerar me zaman banza ya cigaba da driving d'in sa yana jin yadda ran sa ke kuma 6aci. Har cikin layin su ya shigar da ita seda suka kusa kaewa k'ofar gidan su sannan tace "Ya isa" babu 6ata lokaci ya tsaya ta sauka, se kuma ta d'an yi shiru tana tunanin yadda zata shaeda masa seta shiga gida ta kar6o kud'i, a ranta tana fatan Allah yasa me mutunci ne, ganin dae babu wata mafita ya sanya ta fad'in "Bari na kar6o kud'in don Allah.." kallan ta yayi sannan yace "Toh shikenan amma kiyi sauri don Allah" sauke ajiyar zuciya tayi kana a hankali ta juya, a hankali ta sauke idanun ta akan gidan nasu, se ta shiga kallan sa kamar yau ta fara ganin sa, a hankali ta lumshe idanun ta sannan ta taka k'afar ta cikin soron gidan nasu tana jin yadda bugun zuciyar ta ya k'aru lokaci guda.. Mhiz Innocent..... https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* Page 035 ___A hankali ta cigaba da takawa zuwa cikin gidan har zuwa sanda ta k'arasa cikin tsakar gidan, Abba da Yah Sadeeq suna zaune a tsakar gidan, yayin da Umma ke fitowa daga cikin kitchen hannun ta d'auke da tea flask ta k'araso ta ajje a gaban su Abba "Sannu da k'ok'ari" Abba ya fad'a, seta d'an yi murmurshi sannan ta fara k'ok'arin mik'ewa, dae_dae lokacin data d'ago d'in yayi dae_dae da lokacin da Ayrah ta shigo cikin gidan kuma idanun ta suka fara sauka akan Umma, da gudu ta k'arasa bata yi wata wata ba ta rungume ta tana fashewa da wani kuka me tsuma zuciyar me sauraro, lumshe idanu Umma tayi sanda Ayrahn ta rungume ta, lokaci d'aya taji zuciyar