← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 90

Sashe 6

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fad'a yana gyara zaman sa a inda yake zaune, har lokacin be d'ago ba ya furta "Suraj.." "Kaee Raj dae.." Ayrah dake baya ta fad'a tana waro idanun ta, dukkan su murmurshi suka yi kafin Abba ya sake cewa "Mahaefin ka fa?" "Kabeeru" jinjina kae Abba yayi sannan yace "Baka zuwa makaranta ne?" se a lokacin ya d'ago kae ya kalli Abban sannan ya maeda kan nasa k'asa yace "Ehh" d'an shiru Abba yayi yana tunanin tambayar da zata fito daga bakin sa haka dae ya cije yace "Suraj meyasa baka zuwa makaranta?" "Abba Raj ne fa" Ayrah ta sake fad'a, girgiza kae Abba yayi da d'an murmurshi akan fuskar sa kafin yace "Toh shikenan Raj" Yah Sadeeq dake gefen ta shima murmurshin yayi yana girgiza kae "Abbu bashi da kud'in saka ni.." "Shikenan kawae, idan nace zan saka ka zaka ji dad'i?" da sauri ya d'ago kae ya sake kallan Abban, ya lumshe idanun sa yana jin dad'i har besan sanda ya jinjina kae ba murmurshi na wanzuwa a kyakykyawar fuskar sa ba, Abba ma yayi murmurshi yace "Ka fad'a wa Abban naka idan yana da lokaci ya same ni a gida akwae maganar da zamu yi.." amsawa yayi da "Toh angode, Allah ya saka da alkhaeri" "Ameen" Abba ya fad'a yana sake yabawa da hankalin yaron, be bar cikin motar ba seda Abban ya bashi number sa yace ya kaewa Abban nasa ya kira shi.. (_A gurguje zanyi wajen nan pls, saboda idan nace zan ja nan d'in da nisa gaskiya zamu dad'e ne bamu matsa gaba ba, so shys nayi deciding kawae nayi briefing wajen amma yadda zaku fahimta_) ... Sanda Raj ya jewa da Iyayen sa maganar Abban sosae suka yi mamaki, dan da farko ma daya fad'awa Ummeen sa cewar mutumin yace ze sanya shi a makaranta bata yarda ba k'aryatawa tayi kuma ta rufe shi da fad'a dan lokacin ma tun safe babu abinda suka ci kuma har zuwa lokacin Abbun nasa be dawo ba, dama shine me fafutuka ya fita yayi er buga buga ya samo musu abinda zasu ci amma takamaemae bashi da tsayayyiyar sana'a, shiyasa idan ya fita ma ya samo wani abun gaba d'aya suna amfani dashi ne wajen samun abinda zasu ci "Toh hayaniyar me nake ji kuma da rana tsakar nan" maganar da taji daga tsakar gidan ne ya sanya ta dakatawa daga fad'an da take wa Raj, Malam Kabeeru ya k'araso hannun sa d'auke da wata leda, seta k'arasa ta kar6a tana fad'in "Sannu da zuwa Abbu" "Yawwah sannun ka dae" ya fad'a yana kallan Raj dake fad'in "Abbu sannu da zuwa" amsa sannu da zuwan yayi kafin yaja kujera er tsuguno ya zauna a tsakar gidan yana sauke numfashi "Meya faru ne kike ta fad'a tun daga soro nake jiyo muryar ki?" "Gashi nan yaron nan yazo min da wani zance wae wani mutumi yace ze sanya shi makaranta wae kuma ya bashi number sa ka ganta ma yace wae kaema kaje yana neman ka" ta fad'a tana mik'a masa wata takadda dake d'auke da number Abban, kallan su su duka Abbu yayi cikin mamaki, se kuma ya tsaeda idanun sa akan Raj yace "A'ina ya san ka?" d'an shiru kad'an yayi sannan yace bayan ya d'auke kae "A makarantar da nake zuwa" jinjina kae Abbu yayi yana mamakin yadda d'an nasa kullum burin sa shine yayi karatu amma shi kam ya rasa yadda zeyi ya cika masa wannan burin nasa, shi kansa sa yana sa kud'i zeyi k'ok'ari wajen cikawa d'an nasa buri ne ta hanyar kae shi wata k'asar ma ba Nigeria ba yayi karatu "Kuma ka tabbatar da gaske kake?" Abbu yayi k'arfin halin fad'in hakan duk da shi shaida ne akan d'an nasa duk da k'arancin shekaru irin nasa amma da wuya yayi k'arya a cikin lamarin sa "Ehh Abba Allah kuwa da gaske nake" "Ikon Allah" Abbu ya fad'a yana jinjina kae, Ummee tace "Toh zaka je d'in?" kallan ta Abbu yayi kana yace "Me ze hana, kika sani ko alkhaeri ke kiran mu?" "Toh Allah yasa, bari na tashi na d'ora mana shinkafar can mu samu mu ci" Ummee ta fad'a tana mik'ewa. Washe gari da wuri Abbu ya shirya tare shi da Raj, ya kira Abba da er k'aramar wayar sa yayi masa kwatancen gidan nasa sannan suka tafi gidan, daga gidan nasu akwae d'an nisa sosae dan haka suka d'an rage tafiyar a k'asa kafin suka tari adaedaeta ta k'arasa dasu da ragowar chanjin daya ragewa Abbu, a k'ofar gidan suka tsaya Abbu yayi wa Abba flashing a wayar sa saboda kud'in wayar sa daya k'are, ganin kiran nasa ya sanya Abba kawae ya fito dan ya fahimci yazo ne, suka gaesa cikin mutuntawa sannan kowannen su ya gabatar da kansa ga d'an uwan sa, tun a lokacin Abba yaji Abbun ya kwanta masa dan kana ganin sa kaga mutumin kirki gashi ko had'a idanu da Abban ya kasa yi, magana ta k'arshe data wakana a tsakanin su shine Abba yace bayan yaji yadda rayuwar su ke kasancewa, se yayi buga buga yake samu suci abinci, wani lokacin idan be samu komae ba haka zasu wuni da yunwa, shi gashi ba karatu yayi ba dududu iya secondary school ya tsaya, sana'a kuma ta k'i shi, shiyasa ma har lokaci be saka Raj a makaranta ba, saboda komae suka samu cikin su ne, kuma gashi Raj d'in ya tashi da k'aunar makaranta a ransa shi kuma be san yadda zeyi ya saka shi ba, dan idan yace ze saka shin zasu matuk'ar takura ne "Allah sarki, kar ka damu In Sha Allah kamar an saka Suraj a makaranta ne an gama, maganar sana'a kuma dama inaso na bud'e wani shago ne a cikin satin nan, toh idan zaka iya seka dinga zuwa muna zama tare ina sallamar ka" daga inda Abbu ke zaune kan wata kujera ya zamo kamar ze tsugunna yace muryar sa na rawa "Nagode sosae Alhaji, Allah ya saka da alkhaeri, ya biya buk'ata, yasa ka gama da duniya lafiya, nagode nagode sosae Alhaji" "Ya isa haka, babu komae Allah ya taemake mu.." Abba ya fad'a yana rik'o Abban, seya mik'e ya koma ya zauna dae_dae lokacin da Abba ke fad'in "In Sha Allah zuwa gobe se kazo mu fara shirye shirye.." "Toh Alhaji babu damuwa" ya fad'a yana cigaba da kwararowa Abban addu'a cikin matuk'ar farin ciki da jin dad'i. Sanda ya koma gida ya fad'awa matar sa zancen tayi matuk'ar farin ciki, haka suka had'u suka dinga yiwa Abba addu'o'i kala kala. Shima Abban daya jewa Umma da maganar taji dad'i sosae ta kuma yi addu'ar Allah ya taemaka. Washe gari kuwa kamar yadda Abban ya fad'awa Abbu se gashi da wurwuri a gidan, daga nan babu 6ata lokaci suka tafi kasuwar zuwa shagon da aka bawa Abba hayar sa, dama ba tun yanzu yake da burin bud'e shago ba amma be bawa abin muhimmaci ba seda wannan abin ya faru dan haka kayan da yake d'an siya yana ajjewa su yayi amfani dasu ya zuba a cikin shagon, sannan yayi amfani da ragowar kud'in da yake dashi ya k'aro wasu kayan ya zuba zuwa lokacin da Allah ze hore ya zuba wasu masu yawa, duk da shagon yafi k'arfin kayan daya zuba a ciki amma haka yake jin sa cikin farin ciki mara misaltuwa, haka suka isa shagon Abba ya bud'e bayan sunyi addu'o'i sosae, tare suka zauna cikin shagon shi da Abbu, Abbu ke kula da harkokin kayan siyarwar yayin da Abba ke kula da harkar kud'i, cikin ikon Allah a ranar kawae sunyi ciniki sosae musamman daya kasance ranar farko ce se Abba yayi discount akan duk wani abu da mutum ze siya, hakan yasa mutane da dama suka dinga zuwa suna siyar kayayyakin, basu suka tashi ba se dab da maghrib sannan suka tashi, Abba ya d'auki kud'i masu d'an dama a cikin cinikin da suka yi ya bawa Abbu, Abbu yayi ta godiya ya tafi gida cikin farin ciki, yau beyi wahala ya nemo kud'in da zasu samu suci abinci ba yana zaune kawae cikin shago babu rana kuma gashi an bashi abinda ko buga bugar yayi baze samu ba, hakan yasa farin cikin nasa ya sake ri6anyuwa. Tun daga wannan ranar ya kasance kullum Abba da Abbu zasu fita kasuwa da safe basa tashi se dab da maghrib, sosae Abba ya sanya idanu akan Abbu da al'amarin sa, cikin k'ank'anin lokaci Abba ya fahimci Abbu mutum ne me rik'on amana da kirki, babu 6ata lokaci ya shiga gwada shi lokacin da harkar ta bud'e dan yana so ne ya d'an dinga sakar masa abubuwa ba tare da wani tunani ba, sau da dama yasha gwada shi seya same shi da rik'on amana lamarin sa babu ha'inci a ciki, cikin ikon Allah da yaddar Allah sana'ar tasa ta samu kar6uwa a wajen mutane, sosae ake zuwa a siyi kayan da yake siyarwa saboda haka a hankali ya d'an fara sakarwa da Abba wasu abubuwa da dama saboda shima ya d'an samu sassauci. A 6angare guda kuwa ya sanya Raj a makarantar su Ayrah, an saka shi a Junior class saboda yanayin shekarun sa, ba laefi sun d'an fara sabo shi da Yah Sadeeq amma ba wani sosae ba, yayin da a tsakanin sa da Ayrah kuwa kullum wata sabuwar shak'uwa ke k'ara ninkuwa a tare dasu kamar wad'anda suka yi shekara da shekaru a tare, kamar kuma wad'anda suka fito ciki d'aya haka suke al'amuran su, kowanne najin d'an uwan sa a cikin ransa, a tsakanin su babu wanda ke son ganin d'aya yana cikin 6acin rae, sau da dama Umma kanyi mamaki na shak'uwar ta su amma idan ta tuna komae daga Allah ne seta dena mamakin, daga k'arshe ma gaba d'aya Raj ya dawo gidan su Ayrah da zama, idan Abba ya d'auko su daga makaranta seya wuce dasu dukkan su har Raj d'in gida, su tafi Islamiyya sannan idan suka dawo suci abinci kana Raj ya tafi gida, wata ran da k'yar yake tafiya d'in idan Ayrah ta saka rigimar seta bishi, da k'yar take hak'ura idan Umman dashi kansa Raj d'in suka rarrashe ta kana take hak'ura amma fa ta dinga nunk'ufurci kenan kamar wata
Chapter 6 · 0% Book details