← Book details Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 90

Sashe 46

Zazzafar Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

numfashin dake alamta kuka take mara sauti, se kawae ya sake saka hannu ya jata cikin jikin sa ya mata wata kyakykyawar runguma, hannu ya saka ya soma zame hijab d'in jikin ta har lokacin kuma be sake ta ba kuma yak'i bata damar tashi, girgiza kae ta shiga yi kamin cikin k'arfin hali tace cikin raunatacciyar muryar ta "Ni ka k'yale ni" ta fad'a kamar zata fashe da kuka, be kula ta ba kawae ya k'arasa zame hijab d'in gaba d'aya ya jefar gefe sannan a hankali ya shiga shafa bayan ta kamar yarinyar goye, shi kad'ae yasan yadda bugun zuciyar sa ya k'aru, kawae k'arfin hali yake yi yana jan numfashi a hankali, ga mamakin ta se taji kukan na neman tafiya inda ya fito, se dae bata ji zata iya d'aga ido ta kalle shi ba saboda kunyar abinda ya mata yanzun, shi ko kunya ma baya ji? Seta sake kae hannun ta bakin ta data ke ji kamar yanzu ne yake kissing d'in nata, dan haka ta d'an zabura kad'an kamar wadda aka daka tana shirin mik'ewa k'irjin ta na cigaba da bugawa cike da tsoro, gyara mata kwanciyar daya dake yi shine ya tabbatar mata da ba yanzu ne yake kissing d'in nata ba, duk jikin ta a matuk'ar sanyaye ta hak'ura da k'ok'arin tashin ta koma kawae tayi shiru se dae har lokacin akwae ragowar k'walla manne cikin manyan idanun ta. A hankali kuma taji wani irin bacci na sakad'ar ta, so take ya cika ta ta mik'e amma yak'i sakin ta dan haka kawae ta hak'ura ta bada kae bori ya hau, babu dad'ewa bacci me dad'i ya d'auke ta, seta shiga sauke ajiyar zuciya a nutse, se a lokacin ya sauke ajiyar zuciya kamin a hankali ya furta "Rigimammiyar mata ta.." k'arar da wayar sa tayi ne ya sanya shi kallan inda take, be san me kiran nasa ba, kamar ze share se kuma ya kalli Ayrahn dake baccin ta hankali kwance kamar bata da damuwa, ya lumshe idanun sa wata matsananciyar k'aunar ta na sake ratsa shi, cikin dabara yanda ba zata farka ba ya shiga zame ta daga jikin sa har zuwa sanda ya k'arasa zame ta gaba d'aya, ya kwantar da ita kan gadon sannan ya lullu6a mata blanket kana ya sake kallan ta, ji yake kamar ya sake kissing nata se dae baya so ya 6allowa kan sa ruwa dan haka kawae ya k'arasa inda wayar tasa take dae_dae lokacin da ta sake yin ringing "Muneerah!" shine dae sunan daya sake bayyana akan screen d'in, tsaki yaja akan la66an sa dan har ga Allah ya manta da wata Muneerah musamman a yanzu da yake tare da Ayrah "Itama matar ka ce, at least yaci ace ka san a wane hali take" shine abinda zuciyar sa ta raya masa, ya sake jan wani gajeran tsakin yana maeda duban sa kan er rigimar tasa, yanzu taya ze fita ya bar ta cikin d'akin nan ita kad'ae? Idan kuma ya fita kafin ta tashi in ta tashi taga baya nan fa meze faru? Mhiz Innocent..... https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* ZAZZAFAR KAUNA *FREE BOOK* Page 039 ___A hankali ya maeda duban sa kan gadon yana kallan ta duk da fuskar ta ce kad'ae ake iya gani gaba d'aya jikin ta na lullu6e ne da blanket, ajiye wayar yayi kan kujerar kafin ya k'arasa a nutse zuwa wajen gadon, hannu ya saka ya janyo side drawer dake gefe ya matso da ita dab da gadon sannan ya zauna akae, murmushi ne ya su6uce a kyakykyawar fuskar sa sanda yaga tayi juyi seya kasance ta koma kallan inda ya zauna d'in, a hankali ya d'an lumshe idanun sa sannan ya kafe kyakykyawar fuskar ta da kallo, sosae kyawun ta ya sake bayyana da tana baccin, dogayen lashes d'in ta sun kwanta luff luff akan idanun ta, ya shafe wajen minti 3 a haka yana kallan nata sannan ya sake lumshe idanun sa kana ya kwantar da kan sa a gefen gadon. A hankali ya k'arasa kan gadon sannan ya d'an rank'wafa kad'an kana ya shiga hura mata sassanyar iska daga cikin bakin sa akan fuskar ta, dan baya so yayi wani abun daze zama takura a gare ta, a nutse ta shiga bud'e manyan idanun ta sanda taji iskar akan fuskar ta, seda ta gama bud'e idanun nata dae_dae lokacin da ta sauke idanun na ta akan sa, da sauri ta tashi zaune ganin yadda fuskar sa take a dab da ta ta, seda ta tashin sannan ya matsa daga kan gadon, ita kuma taja bargon da take ciki ta sake rufe jikin ta gaba d'aya, murmushin gefen baki ya saki lokaci d'aya yana kae hannun sa kan kwantacciyar sumar kan sa ya shafa, ya lumshe idanun sa yana taune gefen lips d'in sa na k'asa "La'asar tayi.." ya fad'a a hankali bayan ya maeda duban sa kan ta "D'an mik'o min hijab d'ina" ta fad'a ba tare data kalle shi ba tana d'an tura baki, bin inda hijab d'in nata yake yayi da kallo, seya saka hannun sa a hankali ya d'auka sannan ya jefa shi kan kujerar daya ajje wayar sa, itama hijab d'in tabi da kallo kafin ta dawo da kallan ta kan sa idanun ta sunyi rau rau "Don Allah ka bani" ta fad'a har lokacin bata sakko daga kan gadon ba kuma bata cika blanket d'in data rik'e ba, seda ya lumshe ido sannan ya sake zuba mata idanun sa kana yace "Ko inzo in sauko dake ne?" yayi maganar calmly, harara ta jefa masa kamar idanun ta zasu fad'o har seda hakan ya sanya shi yin murmushi me k'ayatarwa, kamar zata yi kuka tace "Ni dae Allah ka bani hijab d'ina sallah fa zan yi" seda ya soma takawa kamar ze hau kan gadon sannan yace "Bari kiga abinda za'ayi.." ya fad'a kamar ze d'aga ta, babu shiri ta saki bargon da sauri ta dirga ta d'ayan 6angaren ta fad'a toilet bayan ta sake murgud'a baki, lumshe idanun sa yayi bayan ta shige band'akin, seya samu kan sa da tuna yadda yaga rigar jikin ta tabi jikin ta ta kwanta sosae ta matuk'ar yi mata kyau, bud'e idanun sa yayi kamin ya fesar da iska daga bakin sa kana ya fice daga d'akin. Be dad'e ba ya dawo dan yana idar da sallah ya taho, sanda ya dawo yayi dae_dae da lokacin da take k'ok'arin fitowa daga cikin toilet d'in, akan sa idanun ta ya fara sauka, da sauri tayi maza taja k'ofar ta koma ciki tana ji kamar ta fasa ihu, kallan inda hijab d'in ta ke ajiye yayi da alama bata d'auka ba, yayi wani murmushi kana ya d'auki hijab d'in ya k'arasa bakin toilet d'in, bece komae ba yayi shiru yana jiran jin ko za tace wani abu, kamar kuwa tasan jira yake se yaji tace cikin er k'aramar muryar ta "D'an ban hijab d'in nan don girman Allah" ta fad'a a shagwa6e tana kwa6e fuska "Gashi" ya fad'a bayan ya matsa jikin k'ofar sosae, seda ta d'an yi jimm kad'an kafin a hankali ta saka hannun ta kan hannun k'ofar ta d'an bud'e ta kad'an, shi kuma ya mik'a mata hijab d'in, seda ta sauke ajiyar zuciya sannan ta saka hannu ta kar6a, kafin ta gama kar6ar ya saka hannun sa d'aya ya tura k'ofar se ganin shi tayi cikin toilet d'in, k'ara ta saki lokaci d'aya tana wara manyan idanun ta, ganin sa da tayi cikin toilet d'in, cikin rashin sanin abin yi kawae ta rungume shi gudun kada ya ganta a yadda take d'aure da d'an k'aramin towel tana fashewa da kuka kawae, wata k'atuwar ajiyar zuciya ya sauke sanda ta fad'a jikin sa d'in, seda ya tafi hutun tak'aetaccen lokaci sannan ya fizgo numfashin sa kana ya sake lumshe idanun sa, a hankali ya fesar da iska daga bakin sa yana shak'ar daddadan k'amshin dake tashi daga jikin ta wanda ya had'u da k'amshin sabulu suka had'u suke bada wani sassanyan k'amshi me dad'in shak'a, hannun sa ya d'aga da nufin d'orawa akan farin gadon bayan ta dan bata damar sake kwanciya cikin jikin sa bayan uwar rungumar data masa, seya jiyo muryar ta cikin rauni tana furta "Ka fita don Allah, ka fita don Allah.." abinda take fad'a kenan ilahirin jikin ta na rawa, bugun da zuciyar ta keyi yana iya jiyo shi saboda yadda jikin ta ke manne da na shi, ba k'aramin gudu yake yi ba, wanda ya had'u da nasa bugun zuciyar da ya chanja tun lokacin da ta rungume shi, sheshshek'ar data cigaba dayi har kuma lokacin tak'i sakin sa kamar ma sake shigewa cikin jikin nasa take yi duk dan kada ya gan ta shine ya sanya shi sakin ajiyar zuciya sannan yace cikin wata shak'ak'k'iyar murya kamar ba tasa ba "Zan fita.." ya fad'a yana k'ok'arin kae hannun sa kan ta, se kuma ya dakata saboda yanda yaji jikin sa ya sake yin wani mugun sanyi, se kawae yace cikin d'an k'arfin hali "Toh cika ni Madam" se a lokacin ta d'an rage kaefin rungumar data masa, amma duk da haka bata sake shi ba "Is ohk, na kulle ido na, bazan kalle ki ba shikenan?" "Tsakanin ka dawa?" ta fad'a cike da sakarci, duk da yanda rungumar data masa ta shige shi sosae har ta sanyaya duk wata ga6a ta jikin sa hakan be hana shi yin murmushi ba sannan ya furta "Da Allah" ya fad'a yana kulle idanun nasa da gaske, se a lokacin ta sake shi a hankali sannan ta mik'e tana kallan fuskar sa, da gasken idanun sa a rufe yake hakan ne ya sanya ta saurin saka hijab d'in ta har lokacin jikin ta na wani irin rawa dae_dae lokacin da shi kuma ya fice daga band'akin, bin sa tayi da harara kamin tace kamar zata yi kuka "Wannan ae iskanci ne" ta fad'a tana murgud'a baki gami da sake harara kamar yana gaban ta. Ajiyar zuciya ya sauke sanda ya fito daga toilet d'in ya nemi waje ya zauna idanun sa a kulle har lokacin jikin sa a sanyaye, yana nan zaune ta fito kamar wata munafuka se sussunne kae take, seda ta saci kallan sa sannan ta k'arasa
Chapter 46 · 0% Book details