← Book details Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 89

Sashe 87

Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tsaye tayi bakin stairs sanye da rigar baccinta da bae wuce gwiwa ba tana kallonsa, mopping yake bae ma lura da ita ba, mika tayi ta karasa saukowa, sae a snn ya a ganta, ya langwabar da kai yana kallonta, ta turo baki tace "Me sa baka tashe ni in taya ka ba" karasawa yyi kusa da ita ya jawo ta jikinsa a hnkli yace "Yau fa xa mu je gida baby" xaro ido tayi ta bata fuska tace "Me xa mu yi a can" yace "Xamu je gaida su Mami" shiru tayi bata ce komae ba sae kuma a hnkli tace "Yayanmu ni tsoro nake ji" ya hade rae yace "nace ni ba yayanki bne ynxu ki canxa min suna" dariya tayi tace "Toh xan dinga ce maka Brother!" Matse ta yyi jikinsa, tayi 'yar kara tace "Wayyo babyna" sae kuma ta boye fuska jikinsa da sauri, yyi dariya ya shiga kissing wuyanta tana shigewa jikinsa romantically. Karfe sha daya saura ta fito daga wanka daure da towel yana xaune yana danna laptop, ta nufi gaban mirrorn sa ta xauna cikin shagwaba tana kallonsa ta madubi tace "yayanmu" kallonta yyi kafin ya dauke kai ya ci gaba da abinda yake, ta kuma kiransa bae tanka ba, bata fuska tayi tace "Toh babyna" sae a snn ya kalleta yana murmushi yace "Ya aka yi" tace "Kaga lotion dina da spray suna can dakin fah," mikewa yyi ya nufi kofa yace "Toh bari in dauko maki" ba a dau lkci ba ya dawo rike da lotions har biyu da sprays kala kala, ya dire mata su gaban mirror ga su ki xaba, ta shagwabe tace "Yayan..." Da sauri ta rufe baki sae kuma tace "Babynah saura kaya" ya langwabar da kai yace "Toh ae ban san wanda xaki sa ba" tace "Kaje ka kakkawo min sae in xaba" yace "Toh!" Ya juya ya fita sae ga shi ya dawo da kaya saiti hudu, biyu atamfa daya lace, daya shadda, kmr xata yi kuka ta karbi kayan tana duba su kafin tace "kasan me? xa ka ga wani lace gold colour da milk ka kawo min," juyawa yyi ya fita ya kuma dawowa da lace din ta karba yace "Takalmi da mayafi fa?" Tace "Toh kawo min har da kayan make up" tana shafe shafenta ya dawo ya ajiye mata su, kafin yace "Toh kawo in shafa maki man" ta hararesa tace "Uhm nasan wayo xaka min bana so xan yi da kaina" ya marairaice mata yace "Allah shafa maki kawae xan yi, Kinga wanka nima fa nake son inyi" daukota yyi ya xaunar gefen gado ya dauki lotion din ya shiga shafa mata a hnkli jikinta yana kallonta, ae shafa lotion sae da ya daukesu fiye da awa daya, don wata duniyar daban ya lula da ita, daga karshe daukar abarsa yyi suka nufi bayi ganin ynda take masa kukan shagwaba ita wllh bata son irin hka, wanketa ya kuma yi tass, ya bar ta tayi daya wankan kafin ta bar masa bayin da gudu yana kkrin kamota don bata yrda yyi wanka gabanta, ko kafin ya fito har ta shirya tana durkushe tana busar da gashinta da hand dryer, yyi dariya yace "Ae da ki jira in kuma shafa maki lotion din" turo baki tayi ta kashe socket din don ta gama ta mike, ita ta fito masa da shadda sky blue da hularsa tace "Wnn xae ma kyau yayanmu" ta fito masa da takalmi da agogo ma ta ajiye masa gefen gado, yace "Toh baxa ki shirya ni ba baby" ta wara ido ta ce "ba gashi na fito maka da kayan ba" yace "Amma ae kin aike ni na je maki daxu, shine ni baxa ki min abinda nake so ba koh" marairaice masa tayi kafin ta tabe baki tace "Toh naji" ta dauki lotion da stool din gaban mirror ta xauna gabansa ta karbi towel din da yake goge gashin kansa da shi ta shiga goge masa sauran ruwan kafarsa da ma jikinsa gaba daya, nan ta shiga shafa masa lotion din tana kallon kwantattcen gashin jikinsa, kallonta kawae yake yana murmushi, ta turo baki ta ci gaba da abinda take har ta gama ta dauki farar singlet dinsa ta mika masa, ya bata fuska yace "Toh baxa ki sa min ba" ita ma ta hade rae xata yi magana ya fixgota jikinsa, ae da kyar ta kwace kanta ta fice da gudu daga dakin. Ba su suka bar gidan ba sae bayan Azahar, sae a snn mood din Afeefah ya canxa wae ita tsoron Mami take, ya dinga kwantar mata da hnkli har suka iso gida, yana rike da hannunta kmr xata yi kuka suka shiga falon, Adnaan kadae ne xaune falon, yyi murmushi ganinsu ya mike ya gaida yayan nasa, Aliyu ya amsa masa yana murmushi shi ma yace "Kwana biyu aiki ya boye ka," yace "Wllh kuwa, ynxu ma anjima xan koma tun jiya nake nn, har da nake shirin xuwa gaida ka can gida ashe kuna hanya" Aliyu yace "Sae mu koma tare, ya baka gaida Zainab ba" kallon Afeefah yyi ya tabe baki yace "Lallai yaya ni xan gaisheta, tana wani kallo na da ido kmr owl" ya karashe maganar yana hararanta, ta bata fuska tace "Toh ba jira nake in gaisheka ba" Aliyu yyi dariya yace "Sae ma nace ka dinga ce mata Anty Zainab xaka gane" dariya ssae Adnaan yyi, Afeefah ta turo baki tace "Ina kwana ya Adnaan" yace "Ban kwana ba" Aliyu yyi dariya yace "Kada Allah yasa ka kwanan mana" daga hka ya ja hannunta suka nufi sama ta juya tana masa gwalo. Dakin Mami suka nufa, sae dae gabanta faduwa yake ssae, shi kuma kunya ta shiga dawainiya da shi don bae ma san da idon da xae kalli Mamin ba, tana xaune daki Fadila durkushe gefenta alamar magana take mata, kmr munafuka Afeefah ta rabe jikin Aliyu, duk suka xauna k'asa, Fadila ta kalli yayanta da jajayen idonta ta gaishesa ya amsa kafin ta mike ta fita daga dakin, yana son tambayar kukan me take sae dae bae ce komae ba, ya gaida Mami kansa kasa, ta amsa masa a sake tana tambayarsa gida, Afeefah ma ta gaisheta a sanyaye ta amsa mata ita ma hka, rasa abun cewa suka yi gaba daya, shi kam har lkcn bae dago ba, Afeefah ta mike a hnkli ta isa gaban uwar tata ta durkushe gabanta cikin rawan murya tace "Don Allah Mami kiyi hkuri ki yafe min...." kuka ta saki a hankali, Mami na kallonta tayi shiru na kusan minti biyar, ganin ynda take kuka yasa tace "ya wuce Zainab, Allah yafe mana baki daya, sae dae ki nemi gafarar wanda kika cutan" kai ta gyada ma uwar tata hawaye na sakko mata, Mami ta kalli Aliyu da bae d'ago ba har lkcn tace "Kai kuma sinne kan me kke hka kmr munafuki" murmushi yyi sae dae bae iya ya dago ba, Mami ma tayi murmushin ta tabe baki tace "Allah kyauta" mikewa yyi yace "Abba na daki Mami" tace "yana ciki," yace "Bari in je gaida shi" daga hka ya juya ya nufi kofa, Mami ta kalli Afeefah dake durkushe har lkcn gabanta tace "Ki tashi ku je" mikewa tayi ta bi bayansa kanta a kasa. Sun dde xaune falon Abba bayan sun gaisa, sae dae shi din ma Aliyu bae iya daga kai ya kallesa ba, duk kunyan iyayen nasa yake, Abba na lura da hkn ya shashantar ya dinga jan Zainab da hira. Uku da 'yan mintuna suka fito daga bangaren Abba, Aliyu ya shiga dakin 'yan matan gidan don ganin Fadila ya ji kukan me take, kwance ya sameta idonta biyu kuma kuka take har lkcn, sae dae duk ynda ya so jin damuwarta kin gaya masa tayi tace ba komae, hka ma Afeefah tayi tayi da ita ta ki magana, juyawa yyi ya nufi dakin Mami ya sameta tana waya ya jira ta gama wayar kafin yace "Mami wae me ya samu Fadila?" Mami tace "Me ka ga?" Yace "Naga tana ta kuka," Mami ta dan yi murmushi tace "xata daina"
Chapter 87 · 0% Book details