← Book details Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 89

Sashe 79

Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸

By Ashmaad

97____98
Kallonta Aunties din nata suka shiga yi, lkci days duk suka sa dariya Anty Baby ta ajiye ledojin hannunta ta xauna gefenta tace "Je tambayi yayanmu" shiru tayi tana kallonsu kafin ta sunkuyar da kai, Anty sadiya da Jiddah suka dinga dariya, Kmr munafuka ta mike xata bar dakin Anty baby ta kamo hannunta ta xaunar da ita tana murmushi tace "biki xa ayi," xaro ido tayi tana kallon su Jiddah tace "Bikin wa kuma?" Anty baby tace "Bikin ki da yayanki" shiru tayi kmr warce aka dasa a gun tana kallon yayar tata ko kifta ido bata yi, lkci daya tayi apprending abinda Anty baby tace ta fada jikinta ta boye fuska, banda dariya bbu abinda yayyin nata ke yi. Tun daga wnn rana Afeefah ta fara wasar 'Yar buya da yayanmu, duk inda xa su hadu bata bi da taji motsin sa xata shige bayi ta kulle, ya lura da hkn ya daina xuwa inda take ma gaba daya, shi kansa kunyar nata yake ynxu, gyara ssae wata kawar Mami 'Yar nijar ta shiga yi mata sanin auren ta na biyu knn, gyaran da ba a cika son ayi ma budurwa ba ma, kuma ita a tunaninta ae ba budurwar bace ita din, bbu wanda bae yi Mamakin Afeefah a gidan ba ganin ko kadan bata daga hankalinta ba, barin Mami, sae dae kusan duk kunyan 'yan gidan take ynxu, gashi tayi sanyi ko magana bata so, abinci ma sae Mami tayi da gske da ita take ci, ana sauran kwana uku biki Anty Safiya ta dawo shake da lafiyayyun kayan lefen da taje Dubai ta yo na akwatuna saiti uku da kits, kuma a ranan 'yan kaduna suka iso gidan da wasu daga 'yan uwan Mami, dangin Abba dama tuni suka iso, gidan ya cika ssae da mutane, ko ta ina Shirye Shirye ake, occasions uku su Anty Safiya suka shirya, mothers eve, kamu, sae dinner, shima da kyar yayan nasu ya yrda don ya ce baya so, ran da xa a sa Afeefah a lalle tana dakin Mami kwance sun dawo daga saloon da su Anty Jiddah, Fadila ta shigo dakin rike da envelope ta karasa kusa da Afeefah, Mami ta bi ta da kallo tace "Meye wnn" k'asa cewa komae fadila tayi, sae da Mami ta maimaita tambayar snn ta isa gun Mami ta duka k'asa tace "Dr Aliyu ne yace in ba Anty Zainab" mikewa xaune Afeefah tayi da sauri tana kallonsu, Mami tayi shiru tana kallon fadila kafin tace "Ina kika ga Aliyun?" Fadila ta sunkuyar da kai tace "A waya ya kira ni" Mami ta sauke ajiyar xuciya tace "Kai mata" mikewa tayi ta karasa gun Afeefah ta mika mata, a sanyaye ta karba ta bude envelope din ta fito da abun ciki, kudi a rafe ta gani da wata farar takarda, hawaye ya kawo idonta da kyar ta warware takardan ta shiga duba content dinsa, rubutunsa me kyau taga kmr hka a takardan "Ina taya ki murnar bikin ki Zainab, Allah sanya Alkhairi, ya bada xaman lfya da xuri'a dayyaba, ya bada hkurin xama da juna, congratulations Afeefah, Happy married life in advance." Hawaye ne ke sakko mata ssae, ta ajiye takardan tayi kwanciyarta duk jikinta yyi sanyi. Yayyinta na shigowa aka nuna masu kudin suka yi murna ssae da yi masa fatan alkhairi, Anty Sadiya ce ta kirga ta ga dubu hamsin ne, Mami tace "Allah ya saka da Alkhairi" Da yammacin ranan aka yi kamu, tayi kkrin ganin ta saki ranta, tayi kyau ba kadan ba cikin tsadadden less maroon da ratsin silvern da ke jikinta, light make up wata kwararriyan make up artist tayi mata, aka yi komae lfya cikin burgewa, Karfe bakwae saura ta shiga gida ita da su ilham da Aneesah, ko wannensu da sabon ciki jikinsa, wayarta ta dauka bayan ta shiga daki ta kwanta ta nemi nmbr Dr Shariff ta tura masa text kmr hka, "Nagode Dr Aliyu, Allah saka da alkhairi ya baka mace ta gari, ina kuma rokon gafarar ka, ka yafe min plss, nasan na xalunce ka amma ka yafe min ba don halina ba, nasan kai din me hkuri ne," tana kuka ta tura masa text din, daga hka ta rufe ido kmr me bacci. Karfe tara da kusan rabi tana kwance dakin Adnaan ita kadae don bata son hayaniyan gidan, Rahmah ta shigo ta xauna gefenta tace "Anty Zainab yayanmu na kiran ki wae" shiru tayi bata ce komae ba, don rabonta da shi kwana biyar Yau, Rahmah ta mike ta nufi kofa xata fita cikin sanyin murya tace "Yana ina?" Rahmah ta juyo tana kallonta tace "Yana cikin motarsa a waje" Hijab dinta ta jawo a hnkli ta sa ta fita dakin, sae da ta fara sanar da Mami snn ta fita gidan ta kama hanyar gate. Nesa da motar ta tsaya, ya jima yana kallonta kafin ya bude motar ya fito ya karaso inda take ya rungume hannunsa yana kallonta, kin dago kanta tayi har sae da ya kira sunanta cikin sanyin murya, da kyar ta iya cewa "Um" ba tare da ta dago ba still don wani kunyarsa take ji ba kadan ba, murmushi yyi yace "Shknn tunda baxa ki kalleni ba" a hnkli ta dago kai ta kallesa, suna hada ido ta rufe fuskarta da tafin hannunta da sauri, dariya yyi yace "ynxu kuma kunyan yayan naki kike princess" kin cewa komae tayi sae juya masa baya da tayi, yace "uhm xaki gaya min ma'anar kunyan nn jibi" juyawa ta yi da gudu ta shige gida, yyi murmushi ya koma gun motarsa ya shiga ya bar anguwar. Washegari thursday aka yi mothers day, gidan ya cika makil da kawayen Mami da abokan arxiki, Mami tayi Mamakin ganin Mahaifiyar Dr Shariff, ta tarbe ta da kyau sae dae da kunya kuma, a ranan ta bada nata gudunmawan bikin na bedsheet me tsada da turarrukan wuta da na ruwa, Mami ta dinga mata gdya tana cewa Allah bar xumunci, tambayar Afeefah Hajiya Hajaran ta dinga yi, hkn yasa Mami ta lallaba Afeefah da kyar ta yrda ta fito don gaidata cike da kunya da nauyinta, da yamma misalin bakwae aka tafi dinner, Afeefah tayi kyau har ta gaji don wani ubansun lace ne jikinta sea green da head pepper red, an mata make up da ya kara fito da ainahin kyanta, shi ko yayanmu sanye yake da tsadadden shadda fara kal da ya amshi farar fatansa, yasa babban riga, waow ina ma fanz xa su gan sa a wnn rana nasan sae sun yi fall din masa, yayyin Afeefah da kanninta duk lace ja da ratsin ash da silver suka sa, guri ya cika da 'yan uwa da abokan arxiki da suka xo taya murna, can na hango 'yan Khaleesat Haiydar Novels da suka xo taya su farin ciki a gefe daya sae ciye ciye ake baki har kunne suna yaba kyan amarya da ango, ko wannensu ya cakare cikin nasu ankon na net lace sky blue da milk colour da ratsin silver a can filin rawa na hango su Hajiya Jamila, Fati Jaji, Rukayya M inuwa, Maryam Liman, Zainab sani daura, Maryam N Abubakar sae tikar rawa suke bakin rae cikin dangin Amarya, na rike Haba ina kallon ikon Allah, to ko wa ya gaya masu venue din dinnern??? can rumfar da Amarya Zainab da angonta yayanmu ke xaune na hango su Ummee Ibrahim, Shafa'atu Ibrahim Usman, Zaynab lawal da Ummi Salma sae likin 'yan dubu dai dai suke ma amarya da ango baki har kunne, a can wani gefe na hall din na hango 'yan partyn Dr Shariff sae wani tabe baki ake kar dae wae ace basu xo ba duk da nasan ganin kwakwaf suka xo yi ba wae taya murna ba, da alama bbu abinda ya burgesu wajen don ko abinci naga sun ki ta6awa, su Halima Muhammad ne, Ibrahim Sadiya, Humairah ibrahim yusuf, Beaulin Bilmoh, Nafeesat A Muhd, da sauransu duk sun tsuke baki cikin ankon wata atamfar leda 'yan duba daya daya da suka yi, su Zahra baba alkali da Asiya Usman da Maryam Adam muhd kam dama ko shigowa hall din naga basu yi ba, daga waje suka tsaya ana yatsine fuska ana taunar cingam wae nn jiran ganin ko Afeefah xata yi fuck up a taron suke, sae addu'a Allah sa hkn ya faru su ke don a cewarsu ba kai gare ta ba, sae ta iya saka kuka a gun, hka dae aka watse taro lfya bbu mishkila. Lol
Washegari ana sakkowa juma'ah aka daura auren Barrister Aliyu Mahmoud, da Zainab Mahmoud Umar a kan sadaki dubu dari biyu, daurin auren da ya samu halartar jama'a da dama daga garurruwa daban daban, kayataccen walima aka yi ranan a gidansu ango da amarya, Karfe biyar aka fara shirin tafiya da amarya gidan mijinta, bata wani daga hankalinta ba sae dae tayi kuka ssae yayin da iyayenta maxa ke mata nasiha, su Momy ma suka daura da nasu da yayyinta mata, nn yayyinta da kawayen Mami da 'yan uwan Abba suka rakata gidan m[truncated by WhatsApp]

🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸

By Ashmaad
Chapter 79 · 0% Book details