← Book details Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 89

Sashe 21

Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

30......
Bayan minti sha biyar Jiddah ta shigo dakin tana kallon Afeefah tace "ke ana neman ki downstairs," Afeefah ta mike xaune tace "ni?" Tsaki Jiddah tayi tace "A'a ni" snn ta fice daga dakin, Afeefah ta mike tana kallon kafarta da ke mata ciwo har lkcn, kasa taka kafar tayi don wani shegen ciwon da taji yana mata, da kyar tana dingisawa ta fita daga dakin ta sauka kasa, xaune ta ga yarinyar a falo Mami ma na xaune falon da Adnaan, Da kyar ta karaso cikin falon tana dingishi Mami tace "wae kafar har ynxu?" Kmr xata yi kuka tace "ciwo yake min sosae Mami" Mami tace "to sae a tafi asibiti gobe" Afeefah ta dan yi Mamakin ganin kanwar Dr Sharif, ta kirkiri murmushi tace "sannu da xuwa' yarinyar ta mayar mata da murmushin tace " ya jikin" Afeefah tace "da sauki" Ledan hannunta ta ajiye tace "Yayana yace in kawo maki" Afeefah ta kalli ledan a dan kunyace tace "ngdd" mikewa yarinyar tayi tace "ni xan koma Mumy ana jirana waje" Afeefah tace "tare ku ka xo?" Kai fateema ta gyada mata, Mami tace "ae da ya shigo," murmushi Fateema tayi ta kuma yi masu sae da safe, Mami ta kalli Afeefah da bata da niyar tashi tace "baxa ki rakata bane Afeefah" mikewa Afeefah tayi ta karbi hijab din jiddah tana dingishi ta bi bayan fateema da har ta kai kofa, har suka fita daga compound din bbu Wanda yace komae cikinsu, sauke glass din motar Dr Sharif yyi Afeefah ta karasa jikin motar kanta a kasa tace "ina yini sir" kallon kafarta kawae yake ta daga kai tana kallonsa jin bae amsa ba yace "har ynxu kafar bae daina ba" gyada masa kai tayi, yace "meyasa baki son a je asibiti a duba maki" tace "kila xa su ce xa su min allura kuma ni bna so" murmushi kawae yyi, a hnkli tace "sir ngdd" yyi noddin kansa yace "welcm, ki gaida mama" tace "xata ji," sae da safe ta kuma yi ma fateema snn ta nufi cikin gida ya bi ta da kallo, dariyar fateema ya sa ya dauke kai da sauri ya juya yana kallonta yace "meye hka" dariya take sosae ta kashe masa ido tace "waow at long last yaya!" Murmushi kawae yyi ya tada motar yyi reverse, tace "yaya amma student din ka kuma?" Harara ya galla mata ya maida hnklinsa kan tukin da yake. Afeefah na shiga gida Mami tace "har sun tafi" gyada mata kai kawae tayi ta kwanta kan kujera, Adnaan yace "kawar ki ce" mikewa xaune tayi da sauri tace "ehh ya aka yi?" ya daga kafada yace "na ga yarinyar na da hnkli da natsuwa ne" dariya Afeefah ta fashe da tace "ahaf ta dai fi karfin ka wllh gwara ma ka daina gnin hnklinta da natsuwa, class din yayanmu ce wnn" da gudu da yar kafarta me ciwo ta nufi sama tana kyalkyala dariya su Jiddah da Mami na taya ta.

Washegari da kyar Afeefah ta yarda aka tafi da ita asibiti a duba mata kafa, ba karamin wahala ta ba likitan da xae gyara mata targaden ba don sae da aka riketa ta dinga rusa masu ihu har sae da Adnaan ya mareta snn suka dan samu lfya, da yamma tana kwance ta fara bacci Dr Sharif ya kira wayarta, da kyar ta iya dagawa don har xaxxabi sae da targaden ya sa mata, murya can kasa ta gaishesa, yace "ya kafar kun je clinic" kuka ta sakar masa tace "bayan mun je an ja min, gashi wani sabon ciwo yake min" yace "wa ya ja maki?" Tace "wani likita ne mugu mana," yace "kiyi hkuri xae daina" da kyar tace "to" snn yyi mata sallama ta ajiye wayar, har kusan magrib Afeefah kasa tashi tayi daga kwancen da take tsabar ciwon da kafar ke mata, Mami ta shigo tace "wae har ynxu kafar ciwon yake maki?" Kmr xata yi kuka tace "Kinga Mami kumbura fa kila xae yi" Mami ta kalli kafar tace "gskya bae gyaru ba knn sae an koma" Afeefah ta fashe da kuka a tsorace tace "don Allah Mami kar mu koma wllh xae kuma mun tsami ne, kila sae xuwa gobe xae daina" Mami ta galla mata harara tace "a hkn kafa ya fara kumbura xa ki ce gobe xae warke? Bari dae Adnaan ya shigo" kuka ssae Afeefah take don bata mance axabar da ta sha daxu ba, Mami bata bi ta kanta ba ta fice, ana idar da magrib Adnaan ya shigo ya kalli kafar yace "ki tashi ki shirya mu koma" kuka ta kuma fashewa da bae bi ta kanta ba ya fice, tana cikin kukan wayarta ya soma ring ta dauka tana kallon Mae kiran, da kmr baxata daga ba da taga Dr Sharif sae kuma ta daga, ta sakar masa kuka tace "Sir kaga wae mai dani asibitin xa ayi a kuma jagwalgwala min kafar koh" shiru yyi bae ce komae ba ya barta ta ci gaba da kukanta, can yace "Zainab, where is d promise yhu made for me?" Hadiye kukan tayi lkci daya tace "ni?" Jin bae amsa ta ba yasa a hnkli tace "Kaga fa sir abun da xafi shi yasa nake kuka, wllh akwae xafi" yace "to ya isa, kina son ni in ja maki kafar?" A hnkli tace "ka iya ne?" Dan murmushi yyi yace "na iya" tace "to xan gaya ma Mami sae kae ka min," yace "OK," snn ya katse wayar, Afeefah ta shiga kwala ma Anty Jiddah kira, Jiddah ta shigo tana hararanta tace "lfya?" Afeefah tace "dan Allah kira min Mami baxan iya tashi ba" tsaki Jiddah tayi ta fice, ba a dau lkci ba sae ga Mami da Adnaan sun shigo dakin Adnaan na rike da makullin mota, Mami tace "ki tashi ki sa hijab" da sauri tace "Mami tsaya ki ji, wnn mutumin da ya kawo ni jiya yace xae gyara min kafar wllh, Dr ne shi ma, sunansa Dr Sharif Mami" Adnaan yace "to kawae Mami ya xo ya gyara mata don ni har tunanin tafiya asibiti nake da ita wllh" Afeefah ta marairaice tace "Ehh Mami, nima har tunanin binsa nake wllh" Mami tace "munafuka, ae sae ki kirasa ya xo ya gyara maki tun da hka kika fi so" dan murmushi tayi tace "to Mami" Mami ta fita Adnaan ya bi bayanta, suna fita wayarta ya soma ring ta jawo da sauri a tunaninta Dr Sharif ne sae ta ga ya Aliyu, a hnkli ta daga ta kara a kunne tare da cewa "yayanmu" "daxu na kira naji buzy, ke da wa kuke waya Afeefah?" Xaro ido tayi a dan tsorace tace "bbu kowa, ntwrk ne" "karya xa ki min knn" yarfe hannu tayi kmr xata yi kuka tace "yayanmu ni da kafata ke min ciwo ma tun safe bn san inda na jefa wayar ba" sauke ajiyar xuciya yyi yace "toh shknn princess, ya kafar ynxu" a hnkli tace "da sauki" yace "Adnaan xae kawo maki ice-cream na kira sa nace ya je ya siyo maki" washe hakora tayi tace "yauwa yayanmu nagode, nayi missin din ka ssae wllh" murmushi yyi yace "OK xan kira ki ltr ki min hira" tace "olryt yayana bye" ko ajiye wayar bata yi ba kiran Dr Sharif ya shigo wayar, kmr munafuka ta daga yace "ke da wa ku ke waya Zainab?" A hnkli tace "yayanmu ne Wanda ke lgs" yace "OK," tace "Sir na gaya ma Mamina tace to ka xo sae ka ja min kafar"

Eeshatullah Goni😘😘
[5/22, 07:56] Umar Dalha: 🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸

A true life love story
Chapter 21 · 0% Book details