← Book details Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 89

Sashe 33

Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

ba karamin kunyar tambayar da dad ke mata Afeefah tayi ba, taki dago kanta don ji tayi da ma ta nutse wajen kawae, Ammi tayi dariya tace "ka bar ni da ita kawae Alhaji, xata gaya min gskya" dad yyi dariya yana kallon Afeefah yace "to tashi ki tafi" mikewa tayi kanta a kasa ta bar falon, dad yyi murmushi yace "Allah ya ji kan Umar ya gafarta masa," Ammi tace "Ameen ya Allah" snn ta mike ta bi bayan Afeefah, bedroom dinta ta kai ta ta xaunar da ita gefen gado tace "kar ki ji kunya ta dota, ki gaya min gskya kina son Aliyu wan matar yayan ki?" Afeefah ta sunkuyar da kai bata ce komae ba, sae da Ammi tayi da gske snn a hnkli ta gyada mata kai a kunyace, Ammi tayi murmushi tace "toh shknn tashi ki yi tafiyar ki" mikewa tayi da sauri ta bar dakin ta shige na su Ilham. A hanya xa su koma gida Afeefah ke ce ma Ma'aruf "yaya amma don Allah kar a gaya ma su Mami, kasan Abbanmu karatu yake son muyi, ni sae na gama karatuna" kmr xata yi kuka ta kare mgnr Ma'aruf ya dan tabe baki yace "na ji" duk da kawae amsa mata yyi don shi ya ma fi son a aurar da ita da karatun hofin. Hka Afeefah ta karashi hutun ta a Kaduna duk ta kagu ta koma kano ta rasa dalili, ana gobe xata koma Abba ya sa ya saleem ya yankar mata ticket, tsaraba ssae Ammi tayi mata, hka ma Anty Amina, ya Ma'aruf kuma laptop ya siya mata, Saleem kuwa da ya tambayeta me take so kawae Ca tayi yar karamar Nokia xae siya mata, da yamma Ya Ma'aruf da Anty Amina suka rakata airport, suna nn har jirgin yyi take off snn suka koma gida. Adnaan ne ya tare ta a airport din kd, Afeefah tayi mmkin da ya Aliyu bae xo tarar ta ba as usual. Bayan sun kama hanya tace "ya Adnaan yayanmu fa?" Adnaan yace "yana gida" shiru tayi bata kuma cewa komae ba har suka isa gida, bata damu da murnar dawowanta da yan uwanta ke tayi ba ta nufi sama da sauri ta shige dakin ya Aliyu, yana tsaye waya na kare kunnansa alamar waya yake, da gudu ta rungumesa tsam cike da farin ciki tace "yayanmu" da farko dakewa yyi, tana dago dara daran idonsa ta daura kan nasa kawae ya kasa, lkci daya ya sakar mata murmushinsa Mae kyau ya ja kumatunta yace "Welcm" bata fuska tayi tace "shine baka xo daukana a airport ba ko yayanmu" ajiye wayar hannunsa yyi yace "kin gaya min xa ki taso yau?" Ta wara ido tace "yaya ka manta bnda waya" yace "na tuna," tace "amma ya saleem ya siya min yar karama bn fara amfani da shi ba" gyada mata kai kawae yyi, ta juya ta nufi kofa tace "bari in je in gaida Mami" bin ta yyi da kallo har ta fita. Tana fita dakinsu ta nufa da sauri ta bude jakarta ta ciro wayar da Dr Sharif ya siya Mata ta shige bayi da sauri ta shiga kiran layinsa, yana dagawa tace "Sir na dawo" yace "haba, yaushe kika dawo" tace "ynxun nn" yace "welcm dear, result din ku ya fito" xaro ido tayi tace "da gske sir? Ka duba min nawa?" Yace "yep na duba, Allah ya taimake ki a course dina kadae kike da carry over" dafe kirji tayi sae kuma ta saka masa kuka, yyi dariya ya katse wayar. Ta ci kukanta ta koshi ta fito daga bayin. Cikin jaka ta boye wayar da sauri. Da daddare Afeefah na fiddo da tsarabar su jiddah wayarta dake cikin jaka ya soma ring, xaro ido su Jiddah suka yi jin Ringtone din, da gudu Afeefah ta nufi jakar don mancewa tayi bata sa a cylnt ba, kashe wa tayi gaba daya ta mayar jakar, Jiddah tace "iPhone Afeefah? Wa ya siya maki" bata fuska tayi tace " ya Ma'aruf" bata jira cewarsu ba taje ta ci gaba da abinda take, Sadiya ta sauke ajiyar xuciya har da su Sumayya. Hka Afeefah ta dinga kaffa kaffa da wayar kar yayanmu ya gani, laptop kuwa da ma ta kai ma Mami tace Ma'aruf ne ya bata, wayar kuwa bata nuna mata ba sae wnda saleem ya siya mata, ana gobe xa su koma sch da daddare Afeefah na xaune ita kadae daki ta shige cikin bargo ta gama waya da Dr Sharif knn tana danne dannenta, ya Aliyu ya turo kofar dakin ganin tun yamma bata sakko falo ba, tsayawa yyi yana kallon bargon, ko kadan Afeefah bata san an shigo dakin ba, ya karasa kan gadon ya yaye bargon a hnkli yana kallonta, a kidime ta mike xaune tana kallonsa, lkci daya ta shiga kkrin boye wayar hannunta, fixgewa yyi yana kallon wayar da mmki, kuka ta saki ta mike da gudu ta fice daga dakin ta shige dakin Mami, Mami da fitowarta daga bayi knn ta bi ta da kallon mamaki, kuka ta fashe mata da tace "wayyo Mami ki ce ma yayanmu dady ne fa ya siya min wayar" korarta Mami tayi daga dakinta a fusace, Afeefah tayi dakin Adnaan shi ma ta fashe masa da kuka tace "kaga ya Adnaan, dady ne ya siya min wayar fa" Adnaan yana kallonta da mmki yace "wani waya?" Cikin kuka tace "yana hannun yayanmu je ka gani kar yace ba shi ya siya min ba ya min duka" dariya Adnaan yyi ya mike ya fita ya samu Ya Aliyu dakin sa a kwance, kallon iPhone 7 din kan gadon Adnaan yyi ya karasa ya dauka yana dariya yace "Wae kaji dady ya siya mata tace" wani mugun kallo Aliyu yyi masa can yace "naji, ae ni bn ce mata komae ba kai mata wayarta" Adnaan ya fita da wayar ya kai Mata dakinsa, mikewa ya Aliyu yyi ya fice daga dakin ya nufi dakinsu jiddah, jakar kayan Afeefah ya nufa ya xuge ya shiga fiddo kayan ciki can kasan jakar ya ga kwalin wayar ya bude bae ga receipt ciki ba, kan farin envelope idonsa ya sauka ya dauki envelope din ya bude ya ga hotuna ne ciki, yana cikin fiddo hotunan aka bude kofar dakin ya daga kai suka yi ido hutu da ita ta shigo, mutuwar tsaye tayi bakin kofar cikin rawan murya tace "yayanmu" bae kuma kallonta ba ya ciro hotunan gaba daya yana kallo, mikewa Aliyu yyi da sauri ya dafa bango tsabar wani mugun jirin da ke neman kada sa daga durkushen da yake kansa na juya masa.

Eeshatullah Goni😘😘
?
?[5/23, 08:34] Umar Dalha: 🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸

A true life love story

By Ashmaad
Chapter 33 · 0% Book details