Sashe 43
Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
tana kallonsa tace "Yayanmu me xan dafa da daddare yau" cikin dubara ya xamo kasa ya xauna snn yace "Kar ki damu xan fita ynxu, idan ina dawowa xan siyo mana take away" tace "toh baxa ka tafi da ni ba?" Girgixa mata kai yyi yana kurban tean hannunsa yace "muna aiki ne kan wani case da colleagues dina" mikewa tayi tace "to shknn bari in kawo maka maganin da Dr Sharif ya kawo maka" bin ta kawae yyi da kallo har ta fita snn ya sauke ajiyar xuciya tare da lumshe idonsa. Har bakin mota ta rakasa yace "idan kin koma ki rufe kofar da key ina da spare key, in kuma aka dauke wuta ki kunna inverter" tace "To Allah kiyaye yayanmu sae ka dawo" murmushi kawae yyi mata ya tada motar ya fita daga compound din ta rufe gate snn ta dawo cikin gida tayi kwanciyarta bayan ta rufe kofa da key, Karfe Takwas da wani abu Aliyu ya shigo gidan, kwance ya sameta kan dogon kujera alamar sllh ta idar ta kwanta, karasawa yyi ya duka yana kallonta, lkci daya ta bude ido ya sakar mata murmushi yace "Bacci kike?" Girgixa masa kai tayi ta mike xaune, abincin hannunsa ya ajiye ya nufi kitchen ya dauko plate, yace "sakko ki ci abinci" ba musu ta sakko ya shiga xuba mata abincin a plate. Afeefah na gama cin abincin ta mike ta nufi dakin da take ta bar sa xaune yana kallo. Karfe goma saura ya shigo dakinta ya sameta kwance tayi rub da ciki idonta lumshe tana waya, ko ba a gaya masa ba yasan da Wanda take wayar ya juya da sauri ya fice daga dakin xuciyarsa kmr xae fashe. Mikewa xaune tayi bayan ta katse wayar sae kuma ta mike ta bi bayansa, kwance ta samesa yyi rub da ciki ta karasa kusa da shi tace "yayanmu!" Banxa yyi mata, hkn yasa ta kuma kiransa nn ma ya share ta, mikewa tayi a sanyaye ta fice daga dakin don idonsa biyu, shi kam wasu hawaye ne suka xubo masa ya Mike xaune da sauri ya rike kansa dake Sara masa. Afeefah na shiga daki kuka ta dinga yi ta kasa daga kiran da Dr Sharif ke mata, da kyar daga karshe ta mike ta shiga bayi don yin wanka bayan ta gama cin kukan nata. Ta fito daga wankan tana tsaye gaban madubi daure da xaninta Aliyu ya shigo dakin, karasawa yyi kusa da ita ganin yanda ta dauke kai ya sa ya tsaya yana kallonta murya can kasa yace "Zainab!" Jin bata tanka sa ba yasa ya jawo ta jikinsa don fara lallashi kmr ynda ya saba a ko da yaushe, wani yarr ya ji tun daga tsakiyar kansa har yatsansa kafarsa kmr Wanda wuta ya ja yyi saurin saketa ya koma baya, ta fashe da kuka ta juya tana kallonsa muryarta na rawa tace "ni bn san me na maka ba yayanmu," kasa jure kukanta yyi ya runtse ido ya kuma jawota jikinsa gabansa na faduwa, jin Afeefah a jikinsa ba karamin rikita sa yyi ba sabanin da da bae taba jin komae ba, kasa daukansa kafafuwansa suka yi ya nufi kan gado da ita, ya xauna ya wani kankameta jikinsa ya runtse ido muryarsa na rawa ya shiga cewa "No! no Plss Zainab kar ki guje ni, plss plss plss, ki tausaya min i i i just can'ttt do with... without yhuuu, I love yhu" kmr wani xautattce hka ya koma don har wani rawa jikinsa yake, Afeefah tuni ta daga kai da mamaki tana kallonsa lkci daya ta shiga tura sa tana cewa "yayanmu" bude idonsa da ya kada yyi yana kallonta lkci daya hawaye ya shiga xuba a idonsa, tsorata tayi ba kadan ba, ta shiga kkrin kwace kanta daga jikinsa, bata ankara ba sae jin bakinsa tayi a wuyarta a rikice yake cewa "I just love yhu Zainab, son ki a jini na yake ki tausaya min ki xama matata pls, Marry me Zainab kar ki guje ni" wani matsanancin kuka ta fashe da a tsorace jikinta na wani mugun rawa tace "Meye hka yayanmu, na shiga uku, innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ihu ta fasa a gigice ganin yana kkrin saka bakinsa cikin nata, wani karfi ya xo mata ta hankadesa ta mike da gudu ta fada bathroom ta sa key, sae a snn hnklin Aliyu ya dawo, ya mike da sauri yana kiran Allah a xuciyarsa, bayin ya nufa ya shiga bubbugawa yana kiran sunanta jin irin ynda take kuka amma kmr da da tunxurata yake, dakinsa ya koma don dauko spare key amma tsabar rudewa yasa ya rasa inda ma ya ajiye ya dawo ya ci gaba da yi mata magiyan ta bude kofa amma taki sae kuka take tana kiran Mami a tsorace, a takaice dae a bayi ranan Afeefah ta kwana kuma ynda ta ga rana hka ta ga daren gashi ta ci kuka har ta gode Allah, shima Aliyu a xaune dakin ya kwana duk ya fice hayyacinsa, kiran sllh yasa ya koma dakinsa a sanyaye yyi alwala ya wuce masallaci, Afeefah na jin fitarsa ta fito jikinta na rawa ta saka abayanta da hijab, ta bude hand bag dinta ta dauki dubu uku da wayarta kan kace me har ta fice daga gidan da gudu, har ta bar layin bata daina gudu ba duk da bata san takamaiman inda xata ba ga ko ina duhu, tana isa main road ta tsayar da adai daita sahun da ta gani bata basa amsar tambayar da yake mata ba ta shige da sauri sae a snn tana mayar da numfashi tace "Tasha xa ka kai ni" Xa ku ji ni shiru kwana biyu ta dalilin jarabawar da nake da shi sisters, srry for the inconvenience dat will cause. [5/22, 07:57] Umar Dalha: 🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸