← Book details Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 89

Sashe 48

Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

63.....
Da damuwa Dr Sharif yace "Tun yaushe kan ke maki ciwo?" Komawa tayi ta kwanta don wani sanyi take ji ba kadan ba, murya can kasa tace "Tun jiya" observing dinta kawae Dr Sharif ke yi bae ce komae ba har Saleem ya shigo dakin da sallama, yana kallonsu yace "Ta gaya maka Dr?" Dr Sharif ya mike yace "Ehh kanta wae ke ciwo, kuma na ga xaxxabi a jikinta" Saleem yace "To ya xa mu yi ynxu?" Dr Sharif yace "Mu tafi clinic, she need drip frm wat I've noticed" Mikewa Afeefah tayi xaune da sauri ta fashe da kuka tace "Sir ni wllh baxan je asibiti ba, kawae idan nasha magani xan samu lfya nasani" Saleem yace "C'mon wani maganin xaki sha bayan Wanda momy tace ta baki daxu, clinic xa mu tafi ynxu ki tashi ki shirya" ganin ynda Zainab ke kuka kmr an aikota yasa Dr Sharif yace "Olryt, tun da baki son asibiti bari in siyo in sa maki a gida, is dat OK?" Da sauri tace "Ehh!" Saleem yyi dariya yace "Ashe ma ciwon na gulma ne dae," Dr Sharif yyi murmushi suka fita dakin a tare. Afeefah ta fara bacci Anty Jamila ta tasheta, da kyar ta mike xaune ta jinginar da kanta jikin gado, da ganinta kasan tana jin jiki, ido hudu suka yi da Dr Sharif da ke tsaye gaban mirror yana hada drip yana kallonta ta mirror'n, murmushi ya sakar mata, ta turo baki ta dauke kai tana kallon Anty Jamila dake mika mata cup din tea, karba tayi ta shiga shan tean a hnkli, jin tashin da xuciyarta yake yasa ta ajiye tace ta koshi, Jamila ta fita daga dakin da cup din sauran tean, karasowa kusa da gadon Dr Sharif yyi yace "Har kin koshi" tace "Uhm" tana kallonsa har ya rataye ledan ruwan snn ya durkusa kusa da ita a hnkli yace "Ur hand" marairaicewa tayi tace "Sir baxae min xafi ba?" "Idan kika rufe ido" yyi assure dinta, a hnkli ta mika masa right hand dinta ya karba, a tare suka dago kai suna hada ido duk suka yi saurin sunkuyar da kai, ganin ya dauki dan alluran ta saka kuka tana yarfe dayan hannun, wani yar kara ta saki ta fixge hannunta jin shigar alluran vein dinta, lkci daya ta saki kuka ta sakko da kafafuwanta kasa daga kan gadon tace "Wllh sir akwae xafi ni dae" hade rae yyi yace "Yhu are joking" kamo hannunta ya kuma yace "Ki fa tsaya Zainab ko mu tafi asibiti, yhu see m almost missin jam'i" runtse ido tayi jin alluran har cikin ranta ta dafa sa ta saki kuka, da sauri yace "Take ur hands off me" ba shiri ta cire hannun, har ya gama sa mata drip din bata daina kukan da take ba, ya mike yana kallonta murmushi dauke fuskarsa yace "Yhu are vry funny" bata ce komae ba sae shirin kwanciya da ta shiga yi, yace "Wait saura allura" xaro ido tayi tace "Ba ga shi ka yi min ba a hannu" ya girgixa kai ya dauko alluran ya nuna mata, tuni ta kuma marairaicewa tace "Sir don Allah ka xuba cikin drip din ae ana yin hka" murmushi yyi yace "Wnn ba a xuba wa drip Zainab" hawaye ya xubo idonta tace "To a ina xaka min alluran," da sauri tace "A hannu?" Rasa me xae ce mata Dr Sharif yyi, ya ajiye alluran ya juya yace "Bari in tafi masallaci" Bin sa da kallo tayi har ya fita, snn ta bi drip din hannunta da kallo, yana fita Momy da Su ilham suka shigo dakin, Suna mata ya jiki, duk da ita bata ji ko wani sauki ba a hnkli tace "Da sauki" Anty Jamila ta shigo dakin da tsire a plate da hollandia drink ta ajiye mata tace "Tashi ki ci Zainab," To kawae Afeefah tace, Momy dake xaune gefenta tace "Wnn me xae mata, in xubo maki shinkafa Zainab?" Afeefah ta girgixa kai tace "Na sha tea fa Momy" suna xaxxaune dakin dad yyi Sallama ya shigo dakin Dr Sharif na biye da shi a baya da saleem, Momy ta mike su Aneesah ma hka suka fita daga dakin, Dad yace "Sannu Ummi, ya jikin" sunkuyar da kai Afeefah tai tace "Da sauki dady" gaishesa tayi snn tayi masa sannu da dawowa, ya tambayeta ya hanya da su Abbanta duk tace "Suna lfya Abba" Godiya dad yyi ma Dr Sharif snn ya fita daga dakin, Saleem ya kalli tulin tsiren dake gefenta yace "tab, duk ke xa ki cinye wnn Zainab" hararansa tayi tace "Toh xa ka ci ne?" Dariya yyi yace "A'a ni yau bnyi kuka da ihu nace kai na na ciwo ba, na masu yin hkn ne" xaro ido tai kmr xata yi kuka tana kallon Dr Sharif tace "Sir ka gansa ko?" Juyawa saleem yyi ya fita yana dariya, Murmushi Dr Sharif yyi yace "yi hkuri shima xae xo kansa wataran, ya ciwon kan?" Tace "Sir yana min fa har ynxu" ya kalli ruwan yace "To baki bari an maki allura ba" xaro ido tayi tace "Kai fa kace xaka tafi mosque" Karasowa kusa da ita yyi ya dauki alluran ba tare da ya kalleta ba yace "Kin shirya" kmr xata fashe da kuka tace "Sir a ina xa ka min? A hannu" ya girgixa mata kai yace "Ba a yi a hannu" tace "To sae ina?" Dago kansa yyi yana kallonta, hkn yasa tayi saurin sunkuyar da kai, sun fi minti uku bbu Wanda yace komae, daga karshe tace "Sir" dago kai yyi ya kalleta, ta kuma sunkuyar da kai a hnkli tace "to ka min" yace "Kin shirya ynxu" gyada masa kai kawae tayi snn tace "Amma a lap fa xa ka min dae" yyi murmushi yace "OK" a dan kunyace ta daga dogon gown din jikinta har cinya ba tare da ta kallesa ba a hnkli tace "ka min sir" yana sauke idonsa kan cinyanta xumbur ta ga ya mike ya nufi drip din dake sakale jikin curtain ya juye alluran har biyu ciki, ba tare da ya kalleta ba yace "ki ci naman ki, ina xuwa" bae jira cewarta ba ya fita daga dakin ta bi sa da kallo. Misalin Karfe tara saura Dr Sharif na xaune kasa falon Dad, dad ya shigo falon yace "Ashe kana ta jira na Aliyu" Dr Sharif yyi murmushi bae ce komae ba, dad ya xauna kan kujera ya rage volume din News din da ake a tv snn ya maida hnklinsa kan Dr Sharif yace "Dad dinka ne ya kirani 2 dayz bck a kan maganar ka da Zainab wae kace xaka tafi course, wani course ne wnn da xae hana ka aure Ali," Dr Sharif ya sunkuyar da kansa bae ce komae ba, Dad ya dan yi murmushi ya ci gaba yace "Nasan yhu are nt sayin the truth, irin iyayenta can kano sun nuna maka karatu take shi ne xaka bullo min da hka koh? To mahaifiyarta da kanta ta xo nn shekaranjiya, kuma mun yanke magana da gwaggwo na, ko ba kai ba ina da 'ya yan abokai da yawa da xan iya hada Zainab da, kuma willingly xa su amince duk da ba neman kai nake da ita ba" Dr Sharif ya dago kai a sanyaye yana kallon Dad sae dae bae ce komai ba, da kyar daga karshe yace "Ba hka bne Dad ban son tauye mata karatun ta ne tun da ta nuna tana so" Dad yace "dama aure na hana karatu? To ynxu dae ga shi mahaifiyarta ta turo min ita in yi duk ynda naga ya dace, kuma in ka ga Zainab ta bar gidan nn to gidan mijinta xa ta don in less then three wks xan hada ta da yayyinta duk in aurar da su" Dr Sharif yace "Toh shknn Abba, kayi hkuri xan turo idan Allah ya yrda."
Chapter 48 · 0% Book details