Sashe 23
Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
kiyi alwala kiyi addu'a kafin ki kwanta" tace "to xan yi" sallama yyi mata ya katse wayar ta ajiye tana kallon su Jiddah dake ta kallonta har lkcn, xata yi magana Jiddah tace "ke da waye" Afeefah na gyara kwanciyarta tace "Dr Sharif" xaro ido duk suka yi Sadiya tace "ko dae son ki yake Afeefah" mikewa Afeefah tayi da sauri ta xauna tana kallonsu, duk suka kwashe da dariya suka ce "tab soyayya ku ke ashe" Afeefah ta hade rae tace "wllh ba soyayya mu ke ba kawae dae...." Sae kuma tayi shiru ta rasa me xata ce masu, Suka kuma saka dariya suka ce "tab, Kinga 'yan matansa a Buk kuwa, duk da dae su suke ta haukansu, to a ina ma kuka hadu da shi" tsaki Afeefah tayi tace "ni dae ba soyayya muke ba" Jiddah tace "kya fada masu dae" Afeefah xata yi magana wayarta ya shiga ring ta duba ta ga ya Aliyu ke kiranta, xaro ido tayi tana kallonsu Jiddah tace "Don Allah Anty jiddah ki dauka ki ce masa ae nayi bacci tun daxu kafata na ciwo, idan yace ya kira ya ji buzy sae ki ce ke ce ke waya" Jiddah ta harareta tace "ehh Sannunki, ki ba Sadiya mana" da kyar ta lallabasu har da dan hawayenta ganin wayar ya kusa katsewa snn Jiddah tayi sallama kmr munafuka, a tsawace yace "who asked yhu to pick my cal ina wasa da ku ne, ina Zainab din" Jiddah tayi tsuru tsuru tana kallon Afeefah, Afeefah ta hade hannayenta a tsorace alamar ta rufa mata asiri, Jiddah tayi saurin cewa "yayanmu tayi bacci tun daxu, kasan likita ya xo ya kuma gyara mata kafarta" a tsawace yace "to wa ke waya daxu?" Jiddah da gabanta ke faduwa tace "ni ce yayanmu bata san na dauka ba ma, ta riga tayi bacci" yace "tasheta ki bata wayar" Jiddah ta juya tana kallon Afeefah ta shiga buga gado tana cewa "Zainab, ki tashi yayanmu ya bugo, Zainab, Zainab" tana shirin mika ma Afeefah wayar yace "kyaleta kawae, sae da safe" yana katse wayar Jiddah ta wurga wayar kan gado ta dinga kyalkyala dariya sadiya na taya ta, Afeefah tayi murmushi ta rungumeta tace "nagode sister" Sadiya tace "da kika ce masa waya kike bae tambayeki da Wanda kike wayar ba" Jiddah tace "ke dae bari ae abun ya bani mamaki" Afeefah a sanyaye tace "da ni ce da yayi min jaraba" Sadiya tace "wnn kuma ke kike shige masa ae" kwanciya Afeefah tayi bata kuma cewa komae ba, Dr Sharif ne ya fado mata, ta Mike da sauri ta nufi bayi tayi alwalan da yace tayi snn ta fito ta kwanta bayan ta gama addu'o'inta. Washegari da asuba Afeefah tayi xaune bakin gado tana Mamakin mafarkin Dr Sharif har sau biyu da tayi daren ranan, mikewa tayi xata je yin alwala taji kafarta yyi mata sauki sosae, ba karamin farin ciki tayi ba tana kallon Jiddah da ta fito daga bayi tace 'kalli anty jiddah na fara iya taka kafar ynxu," Jiddah tace "ashe dae likitan gske ne lecturan" Afeefah ta harareta tace "ba sunansa lecturer ba, its either yhu cal him Dr Sharif, or Dr Aliyu tana kai wa nn ta shige bayi, su Jiddah suka kwashe da dariya, tana xaune kan darduma bayan ta idar da sllh wayarta ya shiga vibrate ta dauka ganin Dr Sharif ne, bayi ta shige ganin su Jiddah sun xuba mata ido, gaishesa tayi ya amsa snn yace " ya kafar Zainab" tace "Sir ya daina min ciwo ssae gashi ina tafiya ynxu" yace "Alhmdllh, Allah kara sauki" tace "Ameen" yace "xa ki xo sch yau?" Ta girgixa masa kai tace "um um sae gobe" yace "ki daure ki xo xan maku revision yau" shiru ta dan yi snn tace "to xan xo" sallama yyi mata ya katse wayar ta bude kofar bayin xata fito ta ga su Jiddah labe bakin kofar bayin, ficewa suka yi daga dakin gaba daya suna dariya, ta tabe baki tayi kwanciyarta.