← Book details Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 89

Sashe 19

Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

a kullum xa a kirata sau hudu sau biyar kuma bata kin dagawa sbda abinda Jiddah ta gaya mata sae dae har lkcn ya ki gaya mata waye shi, kiri kiri ta daina hawa wtspp sbda shi don da ta hau xae ce ta sauka barin da nyt, gashi bata iya masa musu. Ran Monday da yamma ya Aliyu ya kare hutunsa ya kama hanyar lagos, Washegari Tuesday kusan a tare suka shigo sch da Dr Sharif, Afeefah ta sunkuyar da kai bayan su Jiddah sun nufi department dinsu, har sae da ya karaso inda take snn ta gaishesa, ya amsa va tare da ya kalleta ba ya nufi office dinsa. Har ya dan yi nisa ya juya yana kallonta yace "come, xo ki gyara min office" kmr munafuka ta bi bayansa ya bude office din suka shiga, yace "Just 10 mins ki gama gyara min office kafin in dawo" yana kai wa nn ya fita ta fara abinda ya sa, har ta gama bae dawo ba, ta gyara masa kan table dinsa ta jera masa duka buks dinsa gu daya, snn ta nemi guri ta xauna, har kusan takwas da rabi bata gan shi ba gashi suna sa lecture, taji kmr tayi kuka, sae kusan Karfe tara da rabi ya shigo yana kallonta yace "srry na je clinic ne, you've missed ur lecture koh?" Hade rae tayi bata ce komae ba ya karaso ya xauna yace "Wani lecture ku ke da shi" kanta a kasa ta gaya masa yace "to fiddo littafin kiyi karatu" mikewa tayi yace "ina xa ki?" Tace "xan fita in je inyi" yace "sit, kiyi a nn wajen" komawa tayi ta xauna kmr xata yi kuka snn ta fiddo littafin, shi dae sae kallonta yake ta farin glass din idonsa, can bayan minti kusan bakwae ta saci kallonsa taga idonsa na kan wani littafi, ta sunkuyar da kanta, bude kofar aka yi aka shigo da sallama Afeefah ta kafa ma yarinyar ido, yarinyar ta karasa kan table din tana cewa "yaya don Allah ka xo kayi ma baba sanusi magana, ka ji wae baxae kai ni ba yawo nake son xuwa" kallonta kawae yake ta ajiye basket din hannunta ta marairaice, Ya ajiye pen din hannunsa yace "Ummi ta sa ni ne" tace "ta sani mana, kawae shi sae ya dinga min abinda ya ga dama," mikewa Dr Shariff yyi yace "mu je" yarinyar tayi gaba yana biye da ita a baya, Afeefah ta bi su da kallo snn ta fiddo wayarta da sauri ta duba Dp din mutumi me kiranta taga hoton yarinyar ce a kai, duk sae tayi confuse tana tunanin to ko Dr Sharif ne ke kiranta, amma ae bae da nmbr ta, dubara ce ta xo mata tayi dailin nmbr dake kiranta, cikin second biyar wayar Dr Sharif da ke kan table ya soma ring, still tayi tana kallon table din, jiki ba kwari xata karasa table din ya shigo office din, juyowa tayi da sauri, yana kallonta yace "kina neman abu ne" girgixa masa kai tayi a daburce tayi saurin katse kiran da take masa, ya karasa table din yana kallon wayarsa murmusi dauke fuskarsa yace "lfya kike kirana" sunkuyar da kai tayi a hnkli tace "Sirr," Karasowa gabanta yyi yana kallon fuskarta yace "ya aka yi" kin bari su hada ido tayi murya can kasa tace "kayi hkuri ban san kai bne ba" murmushi yyi yace "to ynxu kin sani koh?" Juya masa baya tayi da sauri ta rufe fuskarta, ya nufi kujera ya xauna ya jawo basket din da Kanwarsa ta kawo masa ya shiga hada coffee, Ita dae har lkcn bata juyo ba, can ta nufi kofa tace "Na tafi Sir" a nutse yace "Zainab!" Juyowa tayi tana kallonsa snn ta karasa table din tace "gani sir" kujera ya nuna mata ta xauna snn ya mika mata mug din coffee. Girgixa masa kai tayi kanta a kasa tace "Ngd sir" jin bae ce komae ba yasa ta dago kanta a hnkli ta ga kallonta yake, sauke idonsa yyi daga kallon nata ya ajiye mata gabanta yace "je ki xubar a waje to" murmushi tayi ta dauki mug din a hnkli ta kai bakinta, rabi ta sha ta ajiye ba tare da ta kallesa ba tace "na koshi Sir" bae ce mata komae ba ta mike kanta a kasa tace "Sir I want to go nd read for test" yace "OK" snn ta fice daga office din. Ana gama sllhn Azahar Afeefah ta nufi lecture hall dinsu da Maryam, Maryam ta xauna kujerar gaba Afeefah tace "ke test fa xa muyi, mu koma baya" Maryam ta xaro ido tace "wani test?" Afeefah tace "na Dr Sharif mana" harara Maryam tayi Mata tace "ke wa ya gaya maki" Afeefah tayi shiru da dan mmki tana kallonta, sae a snn ta tuna ashe fa ita kadae ya gaya ma, "wllh nayi xaton kin sani, kuma bamu hadu yau bne da na gaya maki" Maryam tace "kin kyauta ae, da ni ce da na kira ki" bata jira cewar Afeefah ba ta nufi seat a baya, Afeefah ta bi bayanta sanin bata kyauta mata ba, gefenta ta xauna ta marairaice tana bata hkuri, Dr Sharif ya shigo hall din, tsit kke jin hall din bayan minti daya kowa yyi settle down, Dr Sharif yace "I will b conducting my last test today, hope yhu all are ready" kallonsa students suke da mamaki, bae damu da hka ba ya bukaci duk su fito da jakansu da any material da suka san is nt proper to b with dem while writtin his test, mikewa Afeefah tayi ta karbi jakar maryam da nata bayan sun dauki pen da takardar sa za suyi test din ta nufi front din hall din ta ajiye, hada ido suka yi ta dauke kai da sauri ta bar wajen ya bi ta da kallo, dictating questions din yyi masu snn ya basu time yace "this my last test, any one dat misbehaves I will cancel all the test he has done so far, I strictly warn yhu once more to respect ur selves" tsayuwarsa yyi bakin kofa yana danna wayarsa, bayan minti goma Afeefah ta juya tana kallon Maryam ta ga guda biyu kadae tayi ta ajiye pen, kallon Dr Sharif Afeefah tayi taga wayarsa yake danna wa, murya can kasa tace "kawo in rubuta maki 2 nd 4 a bayan paper da pencil sae ki goge da eraser" Ganin maryam bata tanka ta ba yasa ta mika mata papern nata gaba daya tace to gashi ki kwafa, nn ma bata ce komae ba, hkn yasa ta daga kai tana kallonsa ta ga kallonta yake, ajiye takardarta tayi da sauri, Dr Sharif yace "stand up" a hnkli kmr me shirin kuka tace "am srry sir" wani kallo ya watsa mata ba shiri ta mike ya nuna mata kofa alamar ta xo ta fita, kmr xata yi kuka ta nufi gaban class din tace "sir plss am srry i...." Tsawa ya daka mata yace "out!" Jakarta ta dauka ta fice daga class din ta nufi main gate, ta rasa dalilin da yasa bata yi kuka ba, cukuikuye takardar test din nata tayi ta jefar snn ta tsaida adai daita sahu ta hau ta tafi gida abunta.
Chapter 19 · 0% Book details