← Book details Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 89

Sashe 13

Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hnkli Afeefah ta dago kai tana kallonsa ta ga black coffee dinsa kawae yake sha, ta kuma sunkuyar da kai, bayan kusan minti uku ta kai mug din baki a hnkli ta kurbi coffee din ta ji yyi mata ddi ssae, hada ido suka yi tayi saurin ajiye cup din murya can tace "na koshi" wani kallo yyi mata yace "In xubar knn kike nufi?" Bata ce komae ba ta kuma daukar mug din, fiddo wani foil paper dake cikin basket din gabansa yyi ya bude ya ga cake ne ciki ya ajiye gefe snn ya dauki wani textbuk ya shiga dubawa, rabin mug Afeefah ta sha coffee din snn ta ajiye tace "thanks sir na koshi" ya kalli mug din yace "Its beta ki shanye don baxan xubar ba" kmr xata yi kuka tace "Sir ya isheni" kallon da yyi mata ya sa ta dauki mug din ta kuma kai wa bakinta bata kuma ajiyewa ba sae da ta shanye ta ajiye a kunyace tana goge bakinta, bayan kusan minti biyar ta Mike tsaye ganin hnklinsa na kan textbuk din gabansa murya can kasa tace "ngd sir" sae a snn ya dago Kai yana kallonta yace "Welcm" sunkuyar da kai tayi tace "can I go" yace "yes but dnt ever come to my class absentminded again" a hnkli tace "OK sir" snn ta juya xata fita yace "gashi ki tafi da wnn," juyawa tayi ta ga yana mika mata cake din dake cikin foil paper, xata yi magana ya daure fuska yace "take dis!" karasowa tayi ta dan risina ta karba tayi masa gdya snn ta nufi kofa ta fita daga office din. A bakin lecture hall dinsu ta hadu da Maryam da wasu yan matan class dinsu, Maryam tace "ina kika je ina ta nemanki Afeefah" Afeefah tace "Dr Sharif ne ya kira ni" Kallon juna duka yan matan suka yi amma bbu Wanda yace komae, Maryam tace "wae to tunanin me kike a class ana lecture" Afeefah tace "ni ba tunani nake ba" tana Kai wa nn ta shiga class abunta. Daga masallaci Maryam da Afeefah suka nufi cafeteria, xaunawa suka yi inda suka saba xama Maryam ta gaida matan da taga sun kafa masu ido da alama yan 300lvl ne, bbu yabo bbu fallasa suka amsa ta, Afeefah kam xama tayi abunta Maryam ma ta xauna tace "Me xa a kawo maki?" Girgixa mata kai Afeefah tayi tace "ni a koshe nake" Maryam tace "me kika ci?" Afeefah tace "Dr Sharif ya bani coffee a office dinsa, kuma kin ga cake din nn ma shi ya ban, kawae ki siya drink sae ki sha da cake din." Maryam ta saki baki tana kallon Afeefah tace "da gske?" Afeefah xa tayi magana ta ga yan matan da suka samu a cafeteria tsaye kansu, daya daga cikinsu tace "dama mun xo maku kashedi ne a kan ku fita hanyar Dr Aliyu Sharif, idan kuma ba hka ba duk me ya sameku ku kuka siyan ma kan ku wllh wllh" daga Afeefah har Maryam sake baki suka yi suna kallonsu, Maryam tace "ikon Allah, to a kan wani hujja ko dalilin xa mu fita harkansa yana lecturer dinmu ku ma hka" Daya daga cikin yan matan tace "to idan ku kun cika yan halak ku ci gaba da mu'amala da shi wllh sae kunyi da kun sanin xuwan ku makarantar nn" Maryam ta mike a fusace tace "sae de kuyi da kun sanin xuwan ku bayero ba dae mu ba, har mu ance maku muna da lkcn gantalallu irin ku, mu ba abinda ya kawo mu ba knn, kila ma wnda kuke dan shi bae san Allah yyi ruwan ku a bayero ba yan wahala" da mamaki suka ce "mu kike gaya ma hka?" Maryam tace "yes!" mikewa Afeefah tayi har hawaye ya cika idonta tana kallon yan matan tace "don Allah don Annabi kuyi hkuri...." Turata Maryam tayi tace "kada Allah yasa su yi din mana" xage xage suka soma yi har ana neman dambe, Afeefah tuni ta fashe da kuka tana rokon Maryam su wuce, Xuwa ynxu duk an taru ana kallonsu, masu cafeterian ne suka ce duk su fita su je waje suyi kadda su korar masu customer, Afeefah ta ja Maryam da kyar suka fita da cafeterian suka nufi faculty dinsu Maryam na huci tace "ke daga yau Afeefah ki daina sa baki idan ina abu bbu ruwan ki, idan kuma kina jin kuka to ki dinga fita ko kuma ki matsa daga inda nake ki je kiyi kukan ki," Afeefah dae bata ce komae ba sae share hawayenta take. Karfe uku saura ta ce ma Maryam da ta wani share ta a class tun bayan abinda ya faru a cafeteria xata wuce gida, Maryam ta ajiye littafin hannunta tace "baxa kiyi tutorial din bne?" Afeefah tace "um gida xan wuce" Maryam tace "ba tare ku ke tafiya da su Anty Jidda ba" Afeefah tace "na daina jiran su ynxu" Maryam tace "to shknn Allah kai mu gobe" Afeefah ta Mike ta dauki jakarta snn ta fita daga class din, a hanya ta hadu da Dr Sharif da alamar shi ma gidan xae wuce, ta kasa wuce sa bata gaishesa ba kmr munafuka kanta a kasa tace "ina yini" kallonta ya tsaya yi ta dago jin bae amsa ba kuma bae wuce ba, ya sauke idonsa kasa daga kallonta yace "y are yhu crying?" Wasu sabbin hawayen ne suka xubo mata lkci daya ta fashe da kuka, a dan tsawace yace "ba kya ji na ne?" Ganin student sun fara kallonsu yasa yace "follow me," snn ya bar wajen da sauri, ta shiga binsa tana hawaye har lkcn, motarsa ta ga ya nufa ya jingina jikin motar yana kallonta yace "answer my question" a hnkli tana wasa da fingers dinta muryarta na rawa tace "dama ni da Maryam ne mun je cafeteria sae wasu mata suka xo suka same mu wae daga yau kar mu sake kula ka, idan ba hka ba ni bn san me xa su mana ba, shine sae Maryam ta kula su suka fara fada shine..." Kasa karasawa tayi ta shiga rusa masa kuka kmr an aikota har da shessheka, kallonta kawae ya tsaya yi ta daga kai ita ma tana kallonsa tana ci gaba da kukanta, can ya dauke kai yace "kin san matan?" Girgixa masa kai tayi tana share hawayenta.

Eeshatullah Goni 😘😘
[5/22, 07:56] Umar Dalha: 🌸👩🏻'Ya Mace Kyautar Allah 👩🏻🌸

A true life love story

By *Ashmaad*

19.....

Shiru Dr Sharif ya dan yi kmr me naxari snn daga kai yana kallonta yace "ina xa ki ynxu" A hnkli tace "gida" ya ce "yayyinki fa?" ta make kafada tace "ni baxan jira su ba" yace "OK cry no more, I will fish out those galz, su nawa ne?" Tana kallonsa tace "su biyu ne" yace "gud!" Yana kai wa nn ya xaga ya shiga motarsa ita kuma ta nufi main gate. Da daddare Afeefah na xaune falo da yayyinta da su Sumayya suna kallo Abba ya shigo Aliyu na biye da shi a baya, duk suka yi masa sannu da xuwa ya nufi sama, Aliyu ya dawo kusa da Afeefah bayan ya amsa gaisuwar kannin nasa yana kallon idonta yace "Me aka maki" bata fuska tayi tace "a sch ne mana" yace "hado min coffee ki kawo min" yana kai wa nn ya nufi stairs, ta Mike ta je tayi abinda ya sa ta snn ta haura sama don kai masa coffee din, yana xaune yana waya ta karaso ta ajiye masa ta xauna tana kallonsa, yana gamawa ya ajiye wayar yace "Mami ce ko" girgixa masa kai tayi tace "a sch ne mana, wasu mata...." Shiru tayi da sauri ya daga kai yana kallonta yace "wasu Mata me?" Kmr xata yi kuka tace "su ke son min dariya a sch" harara ya watsa mata yace "shine kike masu kuka wawiya kawae, ke baki da bakin masu dariyar ne" hawaye cike idonta tace "ina masu ni ma ae" tsaki yyi ya dauki coffee dinsa ya soma sha, ta wara manyan idonta da ke kyalli da hawayen ciki tace "yayanmu ashe dama coffee na da ddi?" Ba tare da ya kalleta ba yace "da baki sani ba" tace "wllh ban sani ba sae da na 'dan dana daxu kuma har da madara ya sa min, yyi ddi ssae" cire cup din yyi daga bakinsa lkci daya yana kallonta yace "wa ya bakii?" Xaro ido tayi kmr warce ta tuna abu tana kallonsa a dan tsorace ta fara inda inda, ya ajiye cup din hannunsa ya murtuke fuskarsa yace "nace wa ya baki coffee," kuka ta fara yi tace "yayanmu siya fa muka yi ni da Maryam" tsawa ya daka mata yace "yaushe kika fara karya Afeefah? OK gobe xa ki kai ni inda ku ka siya coffee din" ta xaro ido a tsorace tace "wayyo yayanmu kayi hkuri, wani lecturan mu ne ya bani..." Tsit tayi ganin irin kallon da yake mata, ya mike ya xabga mata mari mai lfya yace "ki ka ce wa ya baki" kuka ta fashe da ya daura hannu lebbansa alamar tayi shiru, lkci daya ta hadiye kukan, fuskarsa a daure yace "wani lecturer ne wnn?" Ta hadiye sauran kukanta tace "A makaranta" ya kai mata wani marin a fusace yace "fita ki ban waje, doluwa kawae, " mikewa tayi da sauri ta toshe bakinta da hannunta ta fice daga dakin da gudu ta afka dakinsu ta xube gabansu Jiddah ta dinga rusa masu kuka, harkan gabansu duk suka ci gaba da yyi bbu Wanda ya kalleta bare ya ji me ya sa ta kuka sanin irin halinta. Ta gaji da kukanta ta Mike ta nufi gado ta kwanta lkci daya bacci ya dauketa.
Chapter 13 · 0% Book details