← Book details Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 89

Sashe 28

Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

38......
Afeefah ta dauki hijab dinta a sanyaye ta sa don bata iya masa musu, ta bi sa suka sauka downstairs, yana gaba tana biye da shi a baya har suka iso kitchen din, Amina da ke kkrin jona blender Fadil na bayanta ta juya tana kallonsu yace "Honey ga ta xata taya ki aiki" bbu yabo bbu fallasa Amina tace "A'a taje tayi xamanta ngd" Ma'aruf yace "Haba ki bari ta taya ki mana" bnxa Amina tayi masa hkn yasa ya nuna ma Afeefah sauran tomatoes din da take wankewa tace "je ki karasa wanke mata" kai Afeefah ta gyada masa a sanyaye ta shiga kitchen din ta ci gaba da wanke mata kayan miyan, juyawa yyi ya bar kofar kitchen din ya koma sama. Afeefah na gamawa ta juya tana kallonta a hnkli tace "Anty na gama" ba tare da Amina ta kalleta ba tace "sannu" shiru Afeefah tayi tana tunanin abun yi kuma, kayan salad da cabbage da su carrots da ta gani ta nufa ta daukosu ta nufi sink don wanke su, Amina dae bata ce mata komae ba har ta gama ta yanka salad din da cabbage carrot kuma tayi grating dinsa, hka ta dinga kame kame a kitchen din Amina bata tanka ta ba har dae ta ga ba sauran aiki tayi jigum, can tace "kawo sa in rike maki shi Anty," ba musu Amina ta sauke Fadil dake bayanta ta mika mata ta karbesa ta fita daga kitchen din. Misalin sha daya Amina ta gama duk girke girken da xata yi ta bar kitchen din. Afeefah na kwance tana rungume da Fadil dake ta wasa a jikinta Amina ta bude dakin da sallama ta tsaya daga bakin kofa tace "bani shi xae ci abinci" mikewa Afeefah tayi ta kai Mata yaron ta karbe sa ta juya ta fice. Amina na fita Afeefah ta jawo wayar Ma'aruf dake gunta har lkcn, taga alamar private sim dinsa ne shiyasa bata ga an kira ba, nmbr Dr Sharif tayi dialing, yana dagawa ta gaishesa a hnkli, ya amsa yace "Kin tashi lfya Zainab?" Tace "um" yace "ina hanya fa" ta wara ido tace "da gske sir" yace "yea ko in koma" da sauri tace "A'a," yyi murmushi yace "to sae na xo" ita ma tayi murmushin tace "Allah tsare hanya" tana ajiye wayar jikinta yyi sanyi, to ya ma xata gaya ma ya Ma'aruf xata yi bako, ga matarsan nn da bata da kirki.

Mikewa Afeefah tayi daga kwancen da take jin har an tada sllhn Azahar ta nufi bayi tayi alwala ta fito, ko da ta idar da sllhn kayanta ta ciro don ita tsoron kwalliya ma take a gidan tun kayan baccin jiya ne jikinta duk da tayi wanka, ta dan yi shafe shafenta snn tasa wani gown dinta na material ta maka dogon hijab a kai ta koma ta kwanta, Amina ce ta bude kofar dakin tace "ki je ki dauki abincin ki kitchen fa" to kawae Afeefah tace mata, Amina ta rufe kofar, bayan minti talatin Amina ta kuma bude kofar dakin tace "baki sauka kin dauki abincin ba kuma" mikewa Afeefah tayi da sauri ta nufi kitchen a sanyaye, Aminan na biye da ita a baya ta nuna mata abincin nata da ta ajiye Mata kan faranti da drink da ruwa snn ta juya ta fita kitchen din. Plate Afeefah ta dauka ta bude shinkafar don ba iya cinye duka xata yi ba, ta dibi kadan ta bude miyar ta diba, kaji ta gani a daya kulan dake kan farantin ta dauki daya, coslow din ma bata diba ba ta dauki ruwa maimakon drink snn ta fita daga kitchen din ta haura sama. Kasa cin abincin tayi ta dan cakalkala ta mayar kitchen tana neman bolan xubarwa, bell din gidan aka danna sae da ta dan tsorata ta fito daga kitchen din da sauri rike da abincin don kar Amina ta gani, kallo daya Amina tayi mata ta nufi kofa tana rike da Fadil murmushi dauke fuskarta, Afeefah ta koma kitchen din kmr xata yi kuka, ita dae ta kawo kanta, da ta sani da bata fara bin ya Ma'aruf ba, Amina na bude kofar ta rungume yayanta cike da farin cikin gninsa, rankwashi Dr Sharif ya kai mata yace "kina ma da hnkli kuwa, kada ni xa kiyi" dariya ta kyalkyale da tace "kai yaya, kaga ynda ka canxa kuwa yayana, welcm big bro nah," murmushi yyi ya karbi yaron hannunta ta basa hanya ya shigo falon, Afeefah kam kasa kwakkwaran motsi tayi a kitchen din jin kmr muryar Dr Sharif take ji a falon, ga kamshin turare irin nasa da ya gauraye gidan, Amina kuwa baki har kunne ta ga yayanta da take bala'in so, Dr Sharif ya xauna yana rike da Fadil yace "ina Captain din?" Tace "wllh ya fita tun daxu yaya, amma nasan yana hanya ynxu," kitchen ta nufa da sauri sae ta ga Afeefah a tsaye, dauke kanta tayi ta dauki faranti da glass cup ta bude fridge ta fiddo drinks da ruwa ta daura kai ta fice daga kitchen din tana cewa "yaya ina momyna da fateema, meyasa ba ka xo min da teema ba" yace "suna gida, idan kina son ganinsu ae sae ki je kanon" tace "Ayya yaya dama wllh kila next wk xan tafi kanon sae ga shi kace min xaka xo" hiran yaushe gamo suka dinga yi da yayan nata don sun kusa shekara ba su hadu ba, mikewa tayi tace "bari in hado maka coffee yayana, nasan kuna tare har ynxu" murmushi yyi ta nufi kitchen, wnn karan da mmki take kallon Afeefah dake tsaye har lkcn a kitchen, a dan fusace tace "wae ke me kike yi a kitchen a tsaye ne" bata jira cewarta ba ta shiga yin abinda ya shigo da ita kitchen din, hawaye ya cika idon Afeefah, Amina na fita daga kitchen din ita ma ta fita a sanyaye tana rike da plate din abinci har lkcn, assuring kanta ta shiga yi cewar ae da Dr Sharif ne ya xo Kaduna da ya kirata tasan Mae irin muryarsa ne kawae, tana fitowa daga kitchen din suka yi ido hudu da shi, sake plate din shinkafar hannunta tayi a kidime ta juya da sauri xata koma kitchen din sae kuma ta nufi stairs da gudu kmr munafuka, ya bi ta da kallon mamaki, Amina ta mike da mugun mmki ita ma ta bi ta da kallo snn ta maido da dubanta kan shinkafar kan tiles tace "anya yarinyar nn na da lfya ma kuwa, ba da ni ba wllh" wayarta ta shiga nema don kiran Ma'aruf, murmushi kawae Dr Sharif yyi yana shafa kansa yace "wa xa ki kira?" A fusace tace "Baban Fadil xan kira mana, do ni bnsan ko tana da iskokai ba yarinyar bbu ruwana, Dubi fa abinda tayi ynxun nn" Dr Sharif da har lkcn yana murmushi yace "Uncle dinta ne mijin naki" tace "ni bn san ynda suke ba, jiya ya kawota" Dr Sharif yace "kira min ita" bata fuska Amina tayi tace "tayi maka me yaya, ka rabu da ita ina jin ba ita kadae take ba" hararanta yyi yace "nace ki tafi ki kira min ita" sama ta nufa ba don ranta ya so ba ta shiga dakin da Afeefah take, ta sameta xaune tana rusa kuka bakin ranta, mamaki ne ya cika Amina, sae abun ma ya kusa bata dariya, ta dake tace "me aka maki kike kuka?" Afeefah ta girgixa mata kai da sauri muryarta na rawa tace "gida xan wuce Anty" Amina tace "to sakko a mayar da ke" mikewa Afeefah tayi da sauri ta dauki jakar kayanta, Amina tace "A'a bar jakar xa a biyo ki dashi daga baya sakko kawae" ba musu ta bi bayanta kmr munafuka ita dae har lkcn bata yarda Dr Sharif ta gani xaune falon ba, suna shigowa falon Afeefah ta shiga rufe fuskarta da Hijab dinta ta nufi kofa da sauri, har ta kusa ba Amina dariya, Dr Sharif yace "Zainab!" Juyowa Afeefah tayi da sauri tana kallonsa har lkcn fuskarta a rufe, kuka ta saki ganin shi din ne, Amina ta shiga kallon yayanta da mmki jin ya kira sunan Afeefah, mikewa yyi ya karasa inda Afeefah take yana murmushi yace "sauke hijab din" saukewa tayi ta sunkuyar da kanta da sauri, ya tsura mata ido snn a hnkli yace "baki son ganina ne kuma" muryarta na rawa tace "ina so" Amina ta kwalalo ido da mugun mmki tana kallonsu, yace "toh share hawayen ki" a hnkli ta shiga share fuskarta yace "follow me," ba musu ta bi bayansa suka koma falon ya xauna kan kujera ita kuma ta xauna kasa gefensa har lkcn taki dago kanta, da mmki Amina tace "yaya kasanta ne dama wae?" Yace "ehh nasanta, student dita ce" Amina ta xaro ido tana kallon Afeefah, murya can kasa Dr Sharif yace "kuma budurwata! koh Zainab?" Afeefah ta rufe fuskarta da hijab da sauri ta daura kanta bisa gwiwanta, Amina ta fashe da dariya tace "kai yayana, wae da gske kke don Allah" murmushi yyi yana kallon Afeefah da ke jin kmr ta nutse wajen, yace "karya nayi Zainab?" Kin cewa komae Afeefah tayi ya sakko nn kasa gefenta ya xauna yana kallonta a hnkli yace "Zainab" murya can kasa tace "um" yace "wae ke ba budurwata bace?" Kin dago kanta tayi, yace "shknn bari in tashi in tafi since yhu re denying me" dago kanta tayi da sauri a kunyace tace "Sirr"

Eeshatullah Goni😘😘

[5/22, 07:56] Umar Dalha: 🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸

A true life love story

By Ashmaad
Chapter 28 · 0% Book details