← Book details Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 89

Sashe 20

Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Eeshatullah Goni😘😘

[5/22, 07:56] Umar Dalha: Ya mace kyautar Allah
A true life love story
By Ashmaad
29.....
Mami na kitchen Afeefah ta shigo gida, Mami
tace "Har kun tashi?" Afeefah tace "ehh," snn ta
gaisheta ta nufi sama, kwanciyarta tayi bayan ta
jefa jakarta kan gado, nan da nan bacci ya
dauketa, vibration din wayarta da ke jakarta ne
ya farkar da ita ta mike xaune tana mitsika ido ta
jawo jakarta ta bude ta ciro wayar, tana kallon
me kiran nata, Nmbr Dr Sharif ne, ta yi tsaki ta
ajiye wayar ta koma ta kwanta. Da daddare tana
gugan Hijabbanta wayar ta ya fara vibrate ta
dauka tana kallon me kiran taga Nmbr Dr Sharif
ne still, sae da ya kusa katsewa snn ta daga, ta
kara a kunne tayi shiru, "kin ga dama knn" nn ma
shiru tayi masa, yace "Zainab!" Kin amsawa tayi
se da ya kuma kiranta tace "Na'am" hade da
murguda baki, "me yasa na kira ki daxu ba ki
daga ba" a takaice tace "bacci nake" yace "koh"
shiru tayi masa, ya dan yi murmushi yace "yhu
will explain dat tomorrow," katse kiran yyi, ta ja
dogon tsaki ta ajiye wayarta ta ci gaba da abinda
take. Tun daga ranan Afeefah ta soma wasan
yar buya da Dr Sharif da ta gansa xata gudu ta
canxa hanya idan ya kira ta ki dagawa, duk inda
tasan xae ganta daina xama tayi a gun, in suna
da lecture dinsa to ranan da wuri xata wuce gida,
masallaci ma Dena xuwa Wanda xa su hadu tayi,
sbda shi ta goge wtspp a wayarta, sae dae fa
ynxu kukan ta ya ragu ssae har aka dinga
Mamakin hka a gida, sau da yawa Maryam kan
tambayeta wae me ya hadata da Dr Sharif take
gudu idan ta gansa, sae dae tace bbu komae,
ana hka suka fara Shirye shiryen exams, ana
saura sati daya exams dinsu Afeefah na xaune
gaban department dinsu da su Maryam an gama
tsula ruwa knn, duk ta sakankance ranan dr
Sharif bae xo ba don bata ga motarsa a parkin
space ba kawae ta hangosa yana tahowa da
wani student da alamar lecture ya fito, mikewa
tayi da sauri ba tare da ta lura da wani katon
dutse dake gefenta ba xata falla a guje ta buge
kafa da dutsen sae ga ta kasa cikin ruwa, lkci
daya ta fasa ihu uwa wata jaririya tana cewa
wayyo kafarta, su maryam tuni suka mike a rude,
Maryam ta fara kkrin dagota amma ta kasa don
kin tashi tayi, Dr Sharif ya karaso gun da sauri
shi ya dagota ta fashe da wani matsanancin
kuka tana cewa wayyo kafarta, office dinsa ya
nufa da ita ya sa ta xauna kan kujera har lkcn
tana kuka, yana mata mugun kallo yace "ni
dodonki ne da xaki dinga gudu idan kin gan ni
Zainab? An ce maki ina da lkcn ki, listen daga
yau kika kuma gudu idan ki ka gan ni, I will make
yhu spell doom" kuka kawae take tana yarfe
hannunta, a dan tsawace yace "pull off dat hijab
my frnd" tana kuka ta fara kkrin cire hijab din
don duk ruwa ne da datti, yyi tsaki ya mike ya
nufi first aid box dinsa ya dauko ya dawo
gabanta ya durkusa yana kallon kafarta da ke jini
amma ya kasa taba kafan, yace "ina ke maki
ciwo?" Ankle dinta da toes ta nuna masa da
kneel, ya rasa ynda xae ce ta daga skirt din ma,
kawae ya Mike ya nufi table ya dauki wayarsa,
wata nurse ya kira tana dagawa yace "kina duty
ne pls farida" ta amsa masa da tana gida, yace
"OK plss ki xo Buk ynxu, over to my office wata
student dina ce taji ciwo xa kiyi mata dressing"
tace ga ta nn xuwa, yace "olryt tnxx" snn ya
katse wayar, kanwarsa teemah ya kira yace
"Fatima plss ki taho sch ynxu da spare hijab din
ki" bae amsa tambayoyin da take jefa masa va
yace "just come over" snn ya katse kiran ya
dawo kusa da Afeefah dake hawaye har lkcn, ya
daure fuska yace "srry" kae kawae ta gyada
masa a hnkli ba tare da ta kallesa ba, yana tsaye
kanta har Nurse Farida ta shigo office dinsa da
sallama yyi welcoming dinta, Nurse Farida ta
duka tana kallon kafar Afeefah yace "garin ya
hka" Dr Shariff yace "she's runnin ne" yar dariya
Farida tayi snn ta shiga fiddo kayan da xata
gyara mata kafar a first aid box, yace "ki duba
mata ankle dinta ma its hurting her" kuka
Afeefah ta fara ganin matar ta tsoma cotton
wool tace "na shiga uku sir kace ta min a hnkli
xae min xafi" harara ya balla mata yace "Naki"
da kyar ta bari nurse Farida ta wanke mata kafar
tana kuka, ya fita don bata waje ta duba mata
knee dinta, nurse Farida ta ga gurjewa kawae
tayi shima ta wanke mata snn tace "to sannu an
gama yan mata" Afeefah ta share hawayenta ta
mike xata sa hijab dinta ta ji ta kasa tsayuwa da
toes dinta ta koma ta xauna da sauri tace "xafi"
matar ta kuma duba kafar tace "kin yi targade
knn" kuka ssae Afeefah ta dinga yi tana yarfe
hannu, nurse din ta fita ta kira Dr Sharif tace
"Doctor tayi targade ne fa" kallon kafar kawae
yake snn ya karasa ya duka kusa da ita yace
"Sae an kai ki asibiti knn" Afeefah ta fashe da
kuka tace "Sir ni ba sosae fa yake min ciwo ba"
nurse Farida tace "Haba Dr ka gyara mata mana
ba sae anje asibiti ba" girgixa kai yyi yace "su
tafi asibiti dai" Dubu daya ya ba ma nurse din
tayi transport bayan yyi mata godiya ta wuce,
tana fita Fateema ta shigo, ledan hannunta ya
karba ya ciro hijab din ciki ya mika ma Afeefah,
ta karba kanta a kasa, Fatima tace "Yaya me ya
sameta" yace "gudu take ta fada cikin ruwa"
Fatima tace "eyya sannu" kasa dago kai Afeefah
tayi, Dr Sharif yace "yhu can go, ko ba tare da
driver kike ba," sallama tayi masa ta fita daga
office din, ya kalli Afeefah yace "tashi in yi
dropping din ki a gida, sae ki fadi kinyi targade a
kai ki clinic" mikewa tayi ta dauki hijab dinta ta
linke snn ya fita daga office din bayan ya dauki
car key dinsa ta bi bayansa tana dingishi, har
kofar gidansu ya ajiyeta, kanta a kasa tace "ngd
sir" snn ta bude motar ta fita ta nufi gate da kyar
sae kuma ta tsaya tana yarfe hannu, Dr Sharif ya
fito yana kallonta yace "ya aka yi?" Durkushewa
wajen tayi Cikin kuka tace "ni baxan iya tafiya ba
kuma ciwo kafata ke min" xae yi magana aka
bude gate dinsu, Mami ta fito da Rahamah,
Afeefah ta mike da sauri, Mami da bata ma kula
da Dr Sharif ba ta bude baki tace "meye hka
Zainab" kuka ta saka tace "Mami faduwa nayi a
cikin ruwa a makaranta ynxu gashi bn iya tafiya
sosae ba, shine ya dawo dani gida, ina jin kafar
ya karye ne" Rahmah ta juya ta fashe da dariya,
Mami ta hade rae tace "ke mahaukaciya ce da
xa ki fada cikin ruwa Zainab," ta girgixa ma
Mami kai tana hawaye, sae a snn Mami ta kalli
Dr Sharif, kansa a kasa ya gaisheta ta amsa tare
da cewa "mun gode bawan Allah" Afeefah ta
karbe da sauri tace "kuma makarantar mu daya
fa, shine ya kira aka sa min spirit da magani"
tana kai wa nn ta nufi cikin gida da kyar tana
dingishi, godiya Mami ta kara masa tace baxa ka
shiga daga ciki ba, dan murmushi yyi yace "A'a
mama, ngd" tace "To Allah saka da alkhairi"
sallama yyi mata ya shiga motarsa ita kuma suka
koma cikin gida da Rahmah don dama kasuwa
xata rakata ynxu kuma bbu maganar xuwa
kasuwan. Da daddare Afeefah na kwance daki
bayan Mami tasa Adnaan ya siyo mata
mugunguna a pharmacy ta sha kiran Dr Shariff
ya shigo wayarta, jawo wayar tayi ta daga a dan
kunyace tayi shiru, cikin sanyin murya yace "ya
kafar Zainab?" A hnkli tace "da sauki," yace "kun
je asibiti?" Tace "um um ni nace bna so," yace
"to ae sae an ja maki kafar xae daina," tace "ni
bana so ya dan daina" shiru ya dan yi snn yace
"in kawo maki fruits xa ki sha," shiru tayi bata ce
komae ba, yace "Zainab!" Tace "umm xan sha"
yace "mama xata bari ki fito?" Nn ma ta dan yi
shiru snn a hnkli tace "kila."
Eeshatullah Goni
[5/22, 07:56] Umar Dalha: 🌸👩🏻 'Ya mace kyautar Allah👩🏻🌸

A true life love story

By Ashmaad
Chapter 20 · 0% Book details