Sashe 58
Ya Mace Kyautar Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
73__74 Da daddare Afeefah na kwance Rahmah ta shigo tace Mami na kiranta, mikewa tayi jiki ba kwari ta fita daga dakin ta nufi na Mami, duk an hade mata kai a gidan bbu me kallonta, Anty Safiya ce ta fito daga dakin ko kallonta bata yi ba ta kara gaba, Afeefah ta shiga dakin a sanyaye ta rasa me tayi ma 'yan uwan nata suke jin haushinta, lkci daya ta kawar da damuwar hkn tuna duk don sbda Yayanmu suke ita kuma bata sonsa, dakin Mami ta shiga da sallama, Mami dake xaune tana jiranta ta amsa sallamar, durkusawa tayi tana kallonta tace "Mami ga ni" Mami ta nuna mata gefen gado alamar ta xauna, ta mike ta xauna tana kallon uwar tata, cikin sanyin murya Mami ta soma magana tana kallonta, "Zainab kin san me nake so da ke?" Girgixa kai Afeefah tayi gabanta na faduwa, Mami tayi kasa da murya tace "Duk cikin 'ya yana kina daya daga masu jin maganata wa enda ba sa min musu, kukan ki na gaira bbu dalili ne kadae matsala ta da ke Zainab, wnn karan ma baxan so ki ki jin maganata ba," Afeefah ta sunkuyar da kanta har lkcn gabanta na faduwa, Mami tace "biyayya xa ki min ki amince da auren yayanku!" da sauri Afeefah ta dago tana kallonta, lkci daya ta ji komae ya tsaya mata, Mami ta kwantar da murya tace "Ah da nace baxa ki aure Aliyu ba sbda dalilan da duk na xayyane maku, sae dae baxan kuma iya jurewa gnin halin da yake ciki a ynxu a kanki ba, Ban taba tunanin irin son da Aliyu yace yana maki ya kai hka ba, snn dari bisa dari na yrda da Aliyu, raino na ne Aliyu, nasan abinda xae aikata da wanda baxae aikata ba, ina kuma da yakinin ko bayan ranmu xae rike ki a bisa gskya da amana, Kinga Aliyu yasan halayen ki daga farko xuwa karshe bbu abinda bae sani ba game da ke, don hka xae jure duk wani abinda xa ki yi masa, ba kmr wancan da kike so ba don kukan ki kadae ma abun takaici ne ga mutum, ba wae nace malamin ku bae son ki ba, A'a sae dae Aliyu xae fi iya xama da ke, nasan da wa ennan abubuwan na hana Aliyu ke don kawae in tura ma ubansa takaicin irin abin da ya min, ynxun ma va wae na saduda bne sbda shi sae don D'a na, baxan iya yunkurin kuma hana ke ba Zainab, ina son Aliyu iyakar abinda xae ma warce ta haifesa yake min bae taba min musu a duk shawarar da na yanke kan sa ba, bbu banbanci tsakanin Aliyu da Adnaan da 'ya yan da na haifa a Cikina bn taba ware ku ba, iyakacin son da nake masu shi nake masu, don hka kiyi hkuri kar ki watsa min kasa a ido Zainab, shi kuma malamin naku idan ya ga da warce tayi masa a yayyinki sae a basa, nasan nice na bata komae tun farko don da na amince da ba a kai ga karban kayan su ba" Bbu abinda Afeefah take sae hawaye kanta a kasa, ta ji wani mugun tsanan Aliyu ya dirar mata, inaa ita kam baxa ta taba auren Aliyu ba, bata son shi baxa kuma ta taba son shi ba, a xuciyarta ta fadi hkn tana kuka a hnkli, jin Mami ta kira ta yasa ta dago kai tana kallon uwar tata, Mami ta kwantar da murya tace "Kiyi hkuri nasan ynda kike ji ynxu dota, sae dae xaki ji ddi xa kuma ki gane gata na maki nn gaba don Aliyu mijin aure ne" kai kawae ta gyada ma Mami, Mami tace "Tashi ki tafi, kar kuma ki ce da kowa komae, Allah maki albarka dota" mikewa tayi da kyar ta fita daga dakin tana ganin dishi dishi ta shiga dakinsu ta fada kan gado ta dinga rusa kukan tausayin kanta. Washegari ta tashi da matsanancin ciwon kai sae dae bata nuna ma kowa ba, bbu kuma wanda ya bi ta kanta a gidan sae Mami da ta tilasta ta ta tafi kitchen ta dauki break dinta shima bata wani yi na kirki ba ta dawo tayi wanka snn tayi kwanciyarta, misalin sha biyu tana kwance har lkcn Anty Safiya ta shigo dakin tana kallonta tace "Wato ke 'yar rainin hnkli baxa ki sakko ayi aiki da ke ba, tunda kika dawo sae dae kiyi xaman ki a daki a gama girki ki sakko ki diba ki koma sama koh, to baki isa ba yau, tashi ki fita kitchen ki kama aiki tun kan ranki ya bace" tana kai wa nn ta fice daga dakin, a hnkli Afeefah ta mike xaune hawaye na bin kuncinta ta sakko daga kan gadon ta dauki dankwalinta ta daura snn ta fita daga dakin jiki ba kwari, Adnaan ta tarar falo yana Danna laptop, duk suna gida sbda yayanmu, har Abba ma ya dawo amma bae nemeta ba, ta gaida Adnaan a sanyaye ya amsa a dakile ba tare da ya kalleta ba ta nufi kitchen jiki ba kwari, lunch ta tarar yayyin nata na girkawa a kitchen, gun wanke wanken dake kitchen din ta nufa ta shiga wanke abubuwan da aka b'ata. Anty baby ta gama hada abincin Aliyu kan faranti ta daura da ruwan lipton da beverages ta juya tana kallon Afeefah dake rabe jikin kofa bbu yabo bbu fallasa ta mika mata tace "Ki kai ma yayanmu" karban farantin tayi gabanta na faduwa ta fita daga kitchen din ta tafi sama, Anty Safiya tace "Don me kike bata ta kai" Anty baby tace "Ita kadae xata kai masa ya ci shi yasa" Anty Safiya bata kuma cewa komae ba ta shi gaba da xuba white rice din da suka girka a kula. a hnkli Afeefah ta tura kofar dakinsa tare da yin sallama can ciki ynda ba lallai mutum ya ji ba, kwance ta samesa idonsa lumshe, ta karasa da sauri xata ajiye farantin ta fice sae dae ko gama dire wa bata yi ba ya bude ido, kasa motsi tayi a gun ta ajiye farantin daga karshe ta mike da kyar da niyar ta fita daga dakin amma ta kasa, ba tare da ta kallesa ba fuska daure tace "Ina kwana" ita kanta jin gaisuwar tayi wani iri, jin bae amsa ba yasa ta dago kai a hnkli tana kallonsa, kallonta ta ga yana yi, tayi saurin sunnar da kai sae dae ta kasa fita still daga dakin, samun kanta tayi da karasawa kusa da gadon snn ta dago tana kallonsa ta sulale nn kasa a hnkli tace "Ina kwana yayanmu," kai ya gyada mata cikin sanyin murya yace "Lfya lau" ta na wasa da fingers dinta tace "Ina hada maka tea'n yayanmu?" Bata jira cewarsa ba ta dauki cup ta fara hada masa tean ynda tasan ya fi so yana kallonta, har ta gama ta shiga fiffita masa tea'n dai dai ynda ya fi so snn ta mike ta hau kan gadon ta cire masa bargon jikinsa tace "Gashi yayanmu" dauke idonsa yyi daga kanta ya sa hannu a hnkli ya karba tea'n, ya kai bakinsa tare da lumshe ido, tace "In xubo maka shinkafa?" Bude ido yyi ya girgixa mata kai snn ya ci gaba da shan tea'n, ko rabi bae yi ba ya cire cup din bakinsa ya mika mata xae sauka daga kan gadon, ta karba da sauri tace "Me ya faru yayanmu" ko bae gaya mata ba tasan amai ne, tayi saurin rikosa bayan ta ajiye cup din kasa tace "A'a kar kayi amai plss kila na jini ne don Allah kar kayi yayanmu" a rikice ta kare maganar hawaye cike idonta, ta rungumesa ta shiga buga masa baya a hnkli, bae kuma yunkurin sauka ba, ya lumshe ido yana shakar kamshinta me ddi, sun fi minti shiddah a hka har ya ji bae jin aman kuma, ta daga kai tana kallonsa ya bude ido ya sakar mata murmushi, janye jikinta tayi daga nasa da sauri, sae kuma ta hade rae, lakace hancinta yyi yana murmushin sa me kyau yace "Daina hade rae little sis kin ga daga yau baxa ki kuma gani na ba xan tafi...." Da sauri ta katse sa tace "Ina xa ka?" Kkrin sauka ya shiga yi daga kan gadon ta bi sa da kallo ya nufi gun kayansa yace "Tafiya me nisa xan yi," da sauri tace "Ina xa ka, kuma me yasa xa ka tafi yayanmu" da jin muryarta kasan bata ji ddin tafiyar da yace xae yi ba, kayansa ya shiga fiddo wa yace "Waje me nisa xan tafi, I want to be far away from yhu princess, ba kuma xan dawo ba sae ran da kika yi aure" sakkowa tayi daga kan gadon hawaye cike idonta tana girgixa masa kai tace "A'a kar ka tafi yayanmu xan yi miss din ka" ba tare da ya kalleta ba yace "Ae xa mu din ga waya" shiru tayi tana kallonsa har ya gama hada kayan snn ya dawo kusa da ita ya kamo hannunta, duk tsayinta ko kafadunsa bata kai wa, sae ta daga Kai tana kallonsa hawaye cike idonta, goge mata hawayen yyi yace "Amma tsakanina dake ne wnn, its a secret kuma ki yi promise dina baxa ki gaya ma kowa ba, ynxu lgs xan ce masu xan tafi" kin cewa komae tayi yace "Shiga ki hada min ruwa ynxu" make kafada tayi tace "Ni sae ka gaya min in da xa ka" kmr xata fashe masa da kuka ta kare maganar, yace "Je hada min ki fito sae in gaya maki" a sanyaye ta nufi bayin, ya xauna gefen gadon yana rufe jakar kayansa, tana fitowa daga bayin ya mike ya cire jallabiyan jikinsa snn ya shiga bayin, kasa barin dakin tayi ta xauna gefen gado duk jikinta yyi sanyi, tana xaune ya fito ta nufesa da sauri tace "To gaya min inda xa ka" murmushi yyi yana goge gashin kansa da karamin towel ya nufi gaban mirror ya ja kujera ya xauna duk tana biye da shi, yana kallonta ta madubi yace "UK xan tafi" ta xaro ido tace "Kaje kayi me yayanmu" ya sauke